Tambaya da Amsa: Sakonnin tes daga masu karatu (8)

Tambaya: Assalamu alaikum warahmatullah, Baban Sadik ga tambayata kamar haka: Idan na shirya da masu “Cyber Cafe” kan cewa za su hada ni in rika amfani da siginar intanet dinsu daga inda nake kuma suka hada ni din; shin ba za su rika ganin duk wani motsina ko aikina ba, tunda da siginar intanet dinsu […]

Tambaya da Amsa: Sakonnin tes daga masu karatu (8)

Shagon na’uror8in kwamfuta ana duba intanet

Tambaya: Assalamu alaikum warahmatullah, Baban Sadik ga tambayata kamar haka: Idan na shirya da masu “Cyber Cafe” kan cewa za su hada ni in rika amfani da siginar intanet dinsu daga inda nake kuma suka hada ni din; shin ba za su rika ganin duk wani motsina ko aikina ba, tunda da siginar intanet dinsu nake amfani? Na gode, Allah taimaka.

Amsa: Wa alaikumus salam, barka dai. Idan har masu shagon mashakatar lilo (Cyber Cafe) suka hada wayarka ko kwamfutarka da siginar intanet din shagonsu, babu abin da za su iya gani na shafukan da kake hawa ko mu’amala da su. Ba ma su kadai ba, hatta kamfanin da suke ba su siginar intanet (MTN ko 9Mobile) ba su iya ganin shafukan da ake mu’amala da su.  Abin da zai sa su iya gani shi ne, sai in sun yi amfani da wata manhaja ta musamman don kutsawa cikin wayarka ko satar layin siginar intanet din da ke tsakanin wayarka da shafin intanet din da kake mu’amala da su. Yin hakan kuma da kamar wuya, domin a ka’ida da dokokin mu’amala da intanet, haramun ne; zan maimaita: HARAMUN NE ga kamfanin sadarwa ya yi amfani da wata na’ura ko manhaja don tatso abin da masu amfani da siginar intanet din da yake bayarwa. Idan har kuwa aka gano hakan, ana iya kai su kotu kuma a yi nasara a kansu.

Da fatan ka gamsu da wannan dan gajeren jawabi nawa.  Allah sa mu dace baki daya, amin.

Tambaya: Assalamu alaikum Baban Sadik, don Allah ni wayata ce idan na hau intanet sai ta yi ta nuna mini alamar kamar tana nemo bayanai ne (Searching) amma ba ta budewa sai ta tsaya. Ko mene ne dalili? Daga Anas Umar Gwadabawa, Jihar Sakkwato.

Amsa: Wa alaikumus salam, barka dai. Abin da wannan ke nunawa shi ne, ko dai ba ka da data ne a wayar, ko kuma siginar intanet da ke tsakanin wayarka da kamfanin sadarwarka ba ya da karfi. Dayan wadannan dalilai biyu ne zai iya haddasa faruwar wannan lamari. Don haka sai ka bincika ka gani, idan rashin “data” ce a wayar, sai ka loda mata. Idan kuma akwai amma duk da haka wayar ta kasa hawa, to lallai akwai matsala. Hanya ta karshe da zan ba da shawarar a gwada ita ce, a tabbatar wayar na dauke da tsare-tsaren da ke ba ta damar hawa intanet, wato: “Configuration Settings.” Duk da cewa a yanzu akwai wadannan tsare-tsare a gine a cikin katin SIM din kamfanonin waya, amma tabbatar da samuwarsa zai taimaka matuka. Allah sa a dace, amin.

Tambaya: Assalamu alaikum Baban Sadik, gaskiya sai dai mu ce Allah Ya biya da mafificin alheri game da ilimin da muke samu daga gare ka. Kuma lallai za mu so a fara ba mu ilimin programming kamar yadda ka kwadaitar da mu. Daga Yakubu Abdulkadir, Jihar Bauchi.

Amsa: Wa alaikumus salam, barka dai Malam Yakubu, daga Bauchin Yakubu. Ina matukar farin cikin jin cewa abin da ake karantawa yana ba da fa’ida iya gwargwado. Dangane da bukatarka kuwa na samun muhalli na musamman don koyar da ilimin “Programming” tabbas wannan alkawari ne da na dauka cikin shekarar da ta gabata. Kuma a halin yanzu ina kan kokarin ganin na cika wannan alkawari nawa. Kada a mance, na yi alkawarin samar da gidan yanar sadarwa ne na musamman don yin hakan. Duk da cewa daga baya wadansu cikin masu karatu sun shawarce ni da in fara samar da darussa na musamman don karantar da hakikanin kwamfuta da yadda take aiki tukun, wanda wannan ne asali ko tubalin da ake son duk wanda zai koyi wancan ilimi na “Programming” ya fara da shi, in ya so daga baya sai in dora kan wancan din.

Zan gina gidajen yanar sadarwa ne guda biyu; daya da harshen Ingilshi, dayan kuma da harshen Hausa. Kuma a halin yanzu na mallaki adireshin gidajen yanar tuni, ina kan ginawa ne. Da fatan za a ci gaba da taimakawa da addu’a tare da kasancewa da mu a wannan shafi mai albarka. Domin kasantuwarku na kara mini kwarin gwiwa a kowane lokaci. Na gode matuka, Allah saka da alheri, amin.

Tambaya: Salaamun alaikum, Baban Sadik. Na yi farin cikin dawowar shafin Taskar Baban Sadik, sai dai ban ga abin da na yi matukar zakuwa in gani ba. Wato bangaren karbar horarwa da ka yi bayani a kai. Sai na ji daga gare ka, na gode. Muhammad Baba Idriss, mai sha’awar aikin jarida kuma dalibinka daga Damaturu, Jihar Yobe.

Amsa: Wa alaikumus salam, barka dai. Idan mai tambaya bai mance ba, cewa na yi ina kan aiki ne kan gidajen yanar da za su dauki wadannan darussa. Don haka sai a ci gaba da kasancewa tare da mu a wannan shafi mai albarka. Idan na gama zan sanar, ta dukan hanyoyin da na bayar da sanarwar farko. Wancan kawai ina yi mana albishir ne. A halin yanzu na mallaki adireshin gidajen yanar sadarwar tuni, kuma na fara kintsa bayanan da zan zuba a ciki na darussan da za a yi mu’amala da su. Sai a ci gaba da kasancewa tare da mu.  Na gode matuka.

Tambaya: Assalamu alaikum ranka ya dade. Tambayata ita ce, shin ko akwai wasu makarantun koyon ilimi kan na’urar kwamfuta da ake koyarwa ba tare da wahala irin ta kashe kudi ba, a fili ko ta yanar gizo, kamar yadda ka fada a baya cewa akwai karatu ta yanar gizo da ake yi kyauta tare da samun shaidar kammalawa ta yanar gizo? Ina fatar samun kammalallen bayani da amsa mai gamsarwa, tare da kasidun da ka rubuta daga shekarar 2015 zuwa yanzu. Daga Usama Namadina Umar.

Amsa: Wa alaikumus salam, barka dai Malam Namadina. Dangane da samun kasidun da na rubuta a shekarar 2015, wannan sai dai ka ziyarci Taskar Baban Sadik da ke: <http://www.babansadik.com>, a can na taskance dukkan kasidun da suka bayyana a wannan shafi, wanda na fara rubuta su tun shekarar 2006; shekara 12 ke nan a halin yanzu. Akwai kasidu sama da 500 yanzu haka.

Dangane da batun amsar da na bai wa wancan mai tambaya kan hanyoyin koyon ilimin kwamfuta ta intanet na kyauta, lallai na buga bayanan a shafin jarida, watakila ka riski amsar da na bai wa wanda ya maimaita makamanciyar tambayar ne. Duk da haka, ga kadan daga cikin amsar da na bayar nan kasa:

“Lallai akwai shafuka ko in ce “Makarantun” koyon ilimin kwamfuta kyauta a intanet. Wadannan makarantu ko wurare dai sun kasu kashi-kashi; akwai na kudi, akwai na kyauta, akwai wadanda bayanan a rubuce suke sai ka karanta, sannan akwai wadanda suke dauke da bayanan bidiyo ne tsantsa. Sai dai wani abu kuma, galibinsu, kashi 90 cikin 100, duk da harshen Ingilishi suke. A wasu shafukan kuma dole ne ka yi rajista kafin ka fara daukar darasi. Wasu shafukan na bayar da takardar shaidar gama karatu, wasu kuma ba su bayarwa.  Wasu na dauke da wuraren gwaji, wasu kuma ba su da wuraren gwaji, sai dai ka yi amfani da kwamfutarka.

Duk da ba dai ban san wane bangare kake son koyo ba, shafin da ya fi kowanne shahara kuma yake bai wa masu bukatar koyon nau’ukan ilimi daban-daban (ba wai na kwamfuta kadai ba), shi ne shafi mai take: “Tutorials Point.” Wannan shafi ko makaranta tana dauke ne da rubutattun darussa da suka shafi fannoni daban-daban na ilimi. Duk wani fanni na kimiyya da kere-kere za ka iya koyonsu a wannan shafi kyauta. Kusan dukan fannonin ilimin kwamfuta za ka iya koyonsu a wanan shafi. Sannan shafi ne da ke koyar da kai a tsarin mataki-mataki; daga farko har zuwa karshe.  Adireshin wannan shafi dai shi ne: www.tutorialspoint.com <http://www.tutorialspoint.com>. Kana hawa shafin daga sama sai ka matsa: “Tutorials Library,” don zabar fannin da kake son koyo. Ko kuma ka gangara can kasa, za ka ga wani dogon jadawali mai dauke da dukan fannonin da za ka iya koyo a wannan makaranta. Duk na nuna cewa makaratar na dauke ne da rubutattun darussa, sai dai akwai bangaren darussan cikin bidiyo, sannan akwai bangaren kwatanta abin da ka koya, idan ilimi ne mai dauke da koyo a aikace. Misali, idan bangaren gidan shafin yanar intanet kake son koyo (Web Design), akwai bangaren da za ka je ka kwatanta abin da ka koya a aikace, ba sai kana da kwamfuta ta kashin kanka ba.  Kana iya samun wannan wuri a shafin farko daga sama, can bangaren dama, mai take: “Coding Background.”

Idan kana son kuma inda za ka koyo nau’ukan kwamfuta, musamman yadda ake gina manhajar kwamfuta ne (Programming) ne kai-tsaye, daga farko har zuwa karshe tare da takardar shaidar karatu (Certificate), duk a kyauta, sai ka je shafi mai take: “Solo Learn.” Wannan makaranta na daga cikin makarantu da ke karantar da ilimi cikin sauki, tare da hanyar kwatanta karatun, cikin sauki. Ba ma wannan kadai ba, ana karantar da kai ne mataki-mataki, cikin tsari mai dauke da nishadantarwa da saukin fahimta, ba a cika ka da tarin bayanai. Rubutattun bayanai kadan ne, sai misalai birjik. Cikin kankanin lokaci za ka koyi ilimi mai yawa, wanda ake dauka da dabbakawa. Idan ka gama karatun nan take za a aiko maka da takardar shaida ta adireshin Imel dinka.

Amma dole sai ka yi rajista kafin ka fara daukar darasi.  Idan na ce rajista ba na nufin biyan kudi.  A a, ina nufin za ka bude “account” ne. Idan kuma ba ka son bude wani “account” kana iya hawa da adireshinka na “Facebook” ko “Gmail,” kai-tsaye, a duk sa’ar da ka tashi shiga. Bayan dukan wannan, kana iya saukar da manhajar wannan makaranta a wayarka daga cibiyar “PlayStore” na wayoyin Android, sai dai kuma dole ne sai kana da intanet za ka iya hawa a kowane lokaci.  Adireshin wannan shafi yana: www.sololearn.com <http://www.sololearn.com>

A daya bangaren kuma, akwai shafukan koyon ilimi ta hanyar bayanan bidiyo, su ma kyauta. Wannan na samuwa ta hanyar shafin “Youtube” na kamfanin Google. Wannan shafi na Youtube dai wata duniyar ilimi ce, mai dauke da kusan “kowane” nau’in ilimi kake bukata ko abin da ya dangance shi. Jakar magori ce! Idan kana da wayar salula irin ta zamani mai iya mu’amala da fasahar intanet, to lallai ba za ka rasa samun manhajar Youtube a kan wayar ba. Ko dai ya zama wanda wayar ta zo da shi ne (musamman idan Android ce), ko kuma ka same ta a cibiyar Play Store ko Store, idan nau’in “Windows Phone” kake amfani da ita.

Idan kuma da kwamfuta kake son hawa shafin, kana iya shigar da: www.youtube.com <http://www.youtube.com>. Da zarar ka hau, a sama daga tsakiya akwai inda aka tanada don yin “tambaya” (Search) kan nau’in ilimi ko bayanan da kake bukata. Kada ka mance, galibin ire-iren wadannan ilimi dai cikin harshen Ingilshi suke. Don haka, duk tambayar da za ka yi ta zama cikin harshen Ingilishi ne, kan wani fanni na ilimin kwamfuta kake son koyo. Kana tambayowa kuma za a ba ka amsa bila-adadin.

Wadannan su ne wadanda zan iya ba ka shawarar ka lizimta a halin yanzu. Ba wai iyakarsu ba ke nan, a a, suna da yawa. Aika maka dandazonsu zai rikitar da kai, har ka kasa tabbatuwa a kan guda daya.  Idan ka lizimci wadannan, ka fa’idantu, da kanka za ka nemo kari, ba sai ka sake tambayar wani ba. Allah sa a dace, amin.