Tambaya ga Gwamna Wammako

Mutanen Sakkwato ta Arewa , mun fara tambaya kan ko Gwamna Wammako na kaunar jama’ar wannan karamar hukuma? Wasu za su yi mamakin sanya ayar tambayar, wannan ya biyo ne akan rashin bai wa Hon Abdullahi M Hassan damar zama Kantoma, domin dorawa kan ayyukkan ci gaban al’umma da yake yi wa jama’a, a inda […]

Tambaya ga Gwamna Wammako
Tambaya ga Gwamna Wammako

Mutanen Sakkwato ta Arewa , mun fara tambaya kan ko Gwamna Wammako na kaunar jama’ar wannan karamar hukuma? Wasu za su yi mamakin sanya ayar tambayar, wannan ya biyo ne akan rashin bai wa Hon Abdullahi M Hassan damar zama Kantoma, domin dorawa kan ayyukkan ci gaban al’umma da yake yi wa jama’a, a inda ya tsaya. Koda yake wata majiya mai tushe ta tabbatar da cewa ba Wamakko da kansa, ya dauki alkalami ya soke sunan A. M. Hassan a kan zama Kantoma ba; wani ko daya daga cikin yaransa ne, wanda gwamnan ba ya son saba masa, domin yana da sha’awar tsayawa takarar dan majalisar wakillai ta tarayya, ta yadda zai wakilci kananan hukumomin Sakkkwato ta Kudu da ta Arewa, wanda ake jin ya fito ne daga mazabar Tudun wada (B).
Wannan matashin wanda ya yi tsayin daka, domin ganin tsohon shugaban karamar hukumar mulkin ta Kudu ya dawo a matsayin Kantoma, haka ma ya tsallaka karamar hukumar su, zuwa Sakkwato ta Arewa, wadda aka bai wa yaronsa Kantoma, don a yi masa shimfidar siyasa a kan burinsa na tsayawa takara, zuwa zauren majalisar wakillai ta kasa. Wanan matashin dan siyasa, wanda yake ganin yana da daurin gindi, shi ya sa zai samu hadin kai da goyon bayan shugabanin mazabun kananan hukumomin biyu, tunda  za a iya sayen shugabannin da kudi, don ya kai ga biyan bukatarsa.
Jama’a in ban da sha’anin mulkin dimokuradiyya, ina za a ce dan karamar hukumar mulkin Wurno, wanda kowa bai san gidansu ba, balle sanin kakansa, a ce shi zai jagoranci jama’a a shugabancin jam’iyya a karamar Hukumar Sakkwato ta Arewa? A halin yanzu ya kara daura damarar cewa, Hon Abdullahi M Hassan bai sake dawowa ba. Don haka yake kokarin ganin samar wa Kantoma shugabannin muzabu, duk da cewa ba ya da kyakkyawar hulda ko da shugabannin mazabar da yake zaune, sai aka soma sari kanoke, nan gaba kadan za su yi da nasani domin gaskiya za ta yi halinta.
Ya zama wajibi mu shaida wa Mai girma gwamna cewa idan ba za a ba jama’a da wanda suke goyon baya ba, to zai sha mamaki, domin siyasar ma, muna iya sauya sheka zuwa wata jam’iyya, har mu, har kwamitocin rumfunanmu gaba daya. Da ma bai saka musu da komai ba, bay a bai wa jama’ar karamar hukumar mu ko mai ba.
Muna kokarin jawo hankali da tunanin mai girma gwamna akan al’amura daban-daban, domin a dauki matakan gyarawa, amma duk a banza. Mai girma gwamna ya kauda kai akan wannan lamari, don ba ya son saba wa wasu ’yan kalilan mutane da ke kusa da shi.
Mu jama’ar wannan karamar hukuma ta Sakkwato ta Arewa, munyi amanna da cewa duk mai kishin ci gaban wannan yankin, yasan zuwan M Hassan ya kawo ci gaba, domin ya bi lungu da sakon kowace unguwa, wanda muna iya tunawa a bara wacccan, a cikin jawabin Mai martaba Sarkin Musulmi, wanda ya gabatar a gidan gwamnatin jiha, da yake yi wa mai girma gwamna barka da Sallah, ya bayyana masa cewa shi gwamna ya isar da sakon godiyar majalisar Sarki zuwa ga Abdullahi M Hassan akan na mijin kokarin da ya yi na gyaran Masallacin idi.
“Kuma ina sanar da kai cewa hanyar motar da ka ga ni, da duk wani abu, ba majalisar Sarki ta yi  ba, kokarin Hon Abdullahi M Hassan ne, don haka a mika sakon godiyar mu zuwa gare shi, domin yana neman shawarwarinmu ga ayyukkan alherin da yake wa jama’a,” a cewar Maimartaba.
Wallahi-wallahi wallahi M Hassan bai san mu ba, bai san za mu yi ba, wani bai sa mu ba, mu muka hada matasa daga mazabu 11, kowane sashe an dauko wakilci. Wallahi M Hassan bai taba ba mu aiki ko na dubu 100 ba, balle tunani ya bayar don neman ya dawo, ko don mu samu aiki.  Muna yi ne domin a tarihin tashinmu ba mu taba ganin shugaban karamar hukumar da ya yi wa jama’a aiki kamarsa, a cikin gaskiya da rikon amana, mun amince da imaninsa da akidarsa da kishinsa da tsoron Allah da yasa gaba. Shi yasa muke kishin tallafa wa dawowarsa akan mulki.
Ya rage wa shugabannin muzabu 11, wadanda suka amfana da mulkinsa, baya ga yin ayyukka suka samu kudi wanda a tarihi ba a taba nuna musu tasirinsu da matsayinsu a siyasa ba, sai zuwansa a takara. Muna tsammanin za su ji tsoron Allah, su yi masa sakayyar sake zabarsa a zaben share fage, domin tarihi ya sake maimaita kansa da kansa, wajen cin gajiyar mulkin dimokuradiyya.
Muna kira ga masarautar Mai martaba da dattawa da malaman addini da masu unguwanni da duk wani mai fada aji akan su sanya baki, ka da wani ko wasu su hana mu ‘yancinmu, na dawowar Hon Abdullahi M Hassan, wanda ya yi wa al’umma aiki. Don haka duk lokacin da za mu fito fili jama’a su gan mu su wane ne, za mu kai ziyara makarantunmu na Allo, mu sanar da su abin da ake so, koma aka yi mana, domin ba a son a yi musu malale, da duk wani aikin jinkai, kuma za mu bi gidajen jama’a mazaba-mazaba  don sanar da su bukatarmu.
A karshe muna sanar da Maigirma Gwmna Wammako, ba nufinmu cin fuska ga wani ko wasu ba, amma dai a matsayinsa na uban al’umma, wjaibi ne ya kiyayi dauko wa al’umma “gumamar siyasa.” Mu dai fatar mu a tallafa wa wanda zai yi wa al’umma aiki, don su samu garabasar romon dimokuradiyya. A kuma kiyayi son rai, tunda Malam Bahaushe ya ce, “son zuciya, bacin zuciya.”
Za a iya tuntubar Sardauna Sameer Aliyu ta kafarr sadarwa na [email protected].

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya