Tambayayo da sakonnin masu karatu ta tes (5)
Assalamu alaikum Baban Sadik. Don Allah ni wayata ce a kullum ba ta hawa Intanet kuma an yi mata “Restore” amma abin ya gagara. Don Allah ya ya zan yi? Wa alaikumus salam, barka dai. Eh to, wanann ya danganta. Shin iya dalilan ke nan? Ka ga ba zan iya sani ba. Sai dai […]
Assalamu alaikum Baban Sadik. Don Allah ni wayata ce a kullum ba ta hawa Intanet kuma an yi mata “Restore” amma abin ya gagara. Don Allah ya ya zan yi?
Wa alaikumus salam, barka dai. Eh to, wanann ya danganta. Shin iya dalilan ke nan? Ka ga ba zan iya sani ba. Sai dai ga alama akwai wasu matsalolin daban da ba zan iya sani ba. Domin a ka’ida muddin har aka goge manhajar waya aka mayar da ita yadda ta zo sabuwa, wato: “Restore”, to, ya kamata a ce komai na wayar ya koma kamar ranar da aka kera ta. Wannan ke nuna za ta iya hawa Intanet ke nan, muddin akwai “data” a wayar kuma an kunna.
Don haka, sa ka duba ka gani; shin akwai “data” a wayar? In eh. Shin, a kunne yake? In eh. To, ka ga akwai wata matsalar ke nan. Don haka, shawarata ita ce: a kai wa masu gyaran waya su sake duba ta. dayan biyu; ko dai “System Restore” da akai mata a farko bai yi ba, sama-sama ne. Ko kuma akwai wata matsala daban, wadda ba zan iya sani ba tunda ba ganin wayar nake ba balle. Allah sa a dace, kuma da fatan ka gamsu.
Assalaamu alaikum Baban Sadik, Allah ya saka da alheri game da irin gudunmawar da kake bayarwa, amin. Ni ma daya ne daga cikin masu sauraro da karanta rubuce-rubucenka. Na aiko sako ta Imel, amma ban ga amsa ba. Don Allah ni ma ina son ka aiko mini kasidar “Bamuda Triangle” ta adireshin Imel dina da ke: [email protected]. A karshe, shin akwai wani dandalin Whatsapp da ake tattauna mas’alar da ta shafi kwamfuta ne da dangoginta? Na gode.
– Bashir Sani: 08167957333
Wa alaikumus salam Malam Bashir, da fatan kana lafiya. Lallai haka ne. Sai dai kuma na sha fada cewa sakonnin sukan zo da yawa. Kuma ni ma’aikaci ne. Ba abu ba ne mai yiwuwa a gare ni in amsa sakon kowa da kowa a duk lokacin da aka aiko ba. Wannan ne dalilin da ya sa na tanadi wannan bangare da lokaci don tattaro sakonnin lokaci zuwa lokaci, don amsa su. Ka da ka mance cewa bayan Imel, akwai sakonnin Tes kuma da ake aikowa ta wayar salula. Kuma suna nan jibge yanzu haka ba. Don haka a rika hakuri idan aka ji shiru. Sai hali ya samu nake tara su in amsa iya gwargwadon hali.
Dangane da bukatarka, a halin yanzu akwai shafin Intanet na bude mai suna: “TASKAR BABAN SADIk”, inda na taskance dukkan kasidun da na taba rubutawa a wannan shafi, ciki har da wanda kake bukata. Akwai kasidu sama da 460 yanzu haka a shafin. Kana iya zuwa wannan rariyar don karanta kasidar da ka bukata, kai tsaye: http://www.babansadik.com/category/teku, sai ka gangara kasa kadan za ka ci karo da kasidar, daga na farko har zuwa kashi na uku. Idan kuma kana son saukar da kasidar ne zuwa kan kwamfutarka, ka je wannan shafin: http://www.babansadik.com/dunkulallun-kasidu, sai ka gangara lamba ta 3, daga bangaren dama da taken kasidar za ka ci karo da wata alama shudiya mai suna: “Sauke”, kana matsawa za a saukar maka da kasidar a kan wayarka, kai tsaye.
Bayani kan zauren Whatsapp kuma dai shi ne, har yanzu ban bude wani zaure makamancin hakan ba. Ina la’akari da yanayin lokacina ne. Duk sa’adda na samu dama zan bude, kuma in sanar da jama’a. Da fatan ka gamsu. Na gode.
Salaamun alaikum Baban Sadik. Na samu matsala da akwatin Imel dina saboda ba na iya hawa. Ina tambaya ne a kan yadda ake filashin waya da yadda ake cire “Password” idan an mance. Ka huta lafiya.
– Aliyu Y. Ibrahim: 08179539573
Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Aliyu. Bayani kan yadda ake filashin wayar salula ya gabata tun shekarar 2016, inda na tsawaita bayani sama da kowane lokaci. A takaice dai wani tsari ne da ake amfani da shi wajen “farke” babbar manhajar wayar salula, tare da cire dukkan wani kaidi da kamfanin wayar ya sanya bayan ya kerata. Misali, galibin wayoyin salula sukan zo ne da wasu tsare-tsare a boye da ake kira: “Default Settings” ko “Factory Settings,” wanda hakan ke sa ka kasa cirewa ko goge wasu manhajoji, irin manhajar rubutawa da aika sakonnin tes (Message), da manhajar lambobin wayar salula (Contacts), da dai sauransu. Amma idan aka “farke” babbar manhajar wayar (Operating System), ana iya aiwatar da hakan, tare da loda mata wasu manhajoji wadanda kafin yin hakan, ba abu ba ne mai yiwuwa.
Kamar yadda na fada dai, bayani ne mai tsawo kam. Kuma na amsa tambayar a shekarar da ta gabata, a wani bayani mai tsayi da nayi. Kana iya riskar wannan amsa a wannan adireshi da ke “TASKAR BABAN SADIk”, don fa’idantuwa da su: http://babansadik.com/sakonnin-masu-karatu-2016-13.
Dangane da batun cire kalmar sirri daga wayar da aka mance, duk yana da alaka ne da harkar filashin. Idan ka karanta wancan bayani da ke wannan adireshi a sama, za ka samu cikakken bayani sosai in Allah Ya so.
Ina godiya matuka, kuma da fatan ka gamsu.
Assalamu alaikum Baban Sadik. Ni ma a turo mini kasidar nan mai take: “Binciken Malaman Kimiyya Kan Tsibirin Bamuda.” Na gode.
– Baban Hamza: [email protected]
Wa alaikumus salam, Malam Baban Hamza barka dai. Kana iya zuwa wannan rariyar don karanta kasidar da ka bukata, kai tsaye: http://www.babansadik.com/category/teku, sai ka gangara kasa kadan za ka ci karo da kasidar, daga na farko har zuwa kashi na uku. Idan kuma kana son saukar da kasidar ne zuwa kan kwamfutarka, ka je wannan shafin: http://www.babansadik.com/dunkulallun-kasidu, sai ka gangara lamba ta 3, daga bangaren dama da taken kasidar za ka ci karo da wata alama shudiya mai suna: “Sauke”, kana matsawa za a saukar maka da kasidar a kan wayarka, kai tsaye. Da fatan ka gamsu. Na gode.