Tambayoyi da alhini ga jami’an tsaron Najeriya
Kowa dai ya san halin alakakai da al’amuran tsaro ke ciki a kasarmu. Dalili ken an ya sa MALAMA A’ISHA USMAN LIMAN, [email protected] ta tsunduma alkalaminta cikin tawwada, ta amayar da wannan tsokacin ga al’umma, domin jawo hankalin jami’an tsaron Najeriya. Ga abin da take cewa: Hattara dai jami’an tsaron Najeriya! Hattara mana, tunda wankin […]
Kowa dai ya san halin alakakai da al’amuran tsaro ke ciki a kasarmu. Dalili ken an ya sa MALAMA A’ISHA USMAN LIMAN, [email protected] ta tsunduma alkalaminta cikin tawwada, ta amayar da wannan tsokacin ga al’umma, domin jawo hankalin jami’an tsaron Najeriya. Ga abin da take cewa:
Hattara dai jami’an tsaron Najeriya! Hattara mana, tunda wankin hula yana neman ya kai ku dare. Abu kamar wasa karamar magana ta zama babba. Sannu a hankali ruwa na neman ya kare wa dan kada. Kun kawo na mujiya kun sa wa masu hula, ana neman a zubar muku da martaba da kimar da kuke da su a cikin kasa da al’ummar duniya. To, wai me ya sa kuka yi zugum, kuka kasa yin wani tsayayyen katabus mai alfanu? Wannan ita ce tambayar da mu ’yan Najeriya muke yi, ita ce kuma tambayar da sauran kasashe masu ganin ku da kima suke yi.
Duk wannan rabe-raben da nake yi, ina nufin maganar tsaron kasata Najeriya ne da ya tabarbare kuma yake neman ya gagare ku. Wasa-wasa, fiye da shekara uku ke nan ana ta faman abu daya amma ba wani ci gaba, kullum al’amurra sai kara lalacewa suke yi. Tun muna da kwarin gwaiwa da dokin ganin za ku iya, har gwiwoyinmu sun fara sanyi, zuciyoyinmu sun karaya, ganin yadda kuke rikon sakainar kashi ga lamarin. Kun yi lakwas, kun bar mu a hannun ’yan Boko Haram, suna cin karensu ba babbaka da mu. Yau bom ya tashi a can, gobe a kona wancan kauye; jibi su karbe wancan garin. Aikin ke nan, duk garin da suka so ya kwana a hannunsu, to rannan sai ya kwana a hannun ragamar gudanarwar su.
Tun suna sari-ka-noke a kauyuka, har ta kai yanzu kananan hukumomi suke kwacewa. Don nuna isa, har bugun kirjin yin hakan suke yi a kafafen sadarwa kafin su aikata. sai ka ga sannu a hankali sai sun ida nufinsu, alhali kuwa kuna jin su, kuna ganin su.
Da mun fara yi wa gwamnati korafin cewa ba ku da isassun kayan aiki, sai kuka ce mu yi shiru ba haka ba ne; kuna nan kuna nazarin yaya za ku fuskanci abun. Kuna cewa wai ai shi yaki dan zamba ne, amma ga shi har yanzu kullum abun sai kara lalacewa yake yi; har ta kai ga yanzu ’yan Boko Haram sun yi jan wuyan da sukan fafare ku da gudu, har sai sun fitar da ku daga iyakar kasarku! Wannan wane irin abin kunya ne ke faruwa da ku? Alhalin kowa ya san jami’an tsaron Najeriya su ne garkuwar Afirika! Ku tuna baya ku ga irin jaruntakar da kuka yi a kasashen Laberiya da Saliyo da Sudan kuma kowa ya san da hakan.
Me yake faruwa ne? Yau a ce ga yaki cikin kasarku, har cikin gidajenku amma kun kasa tunkarar shi gadan-gadan, ku murkushe shi cikin gaggawa, sai hauhawa yake yana lakume rayuka da dukiyoyin jama’a. Kuma kuna ji kuna gani. A gaskiya irin rayukan da aka rasa a kasar nan, koda wata kasa ce ta far mana da yaki, iyakar hasarar rayukan da ya kamata mu yi ke nan. Idan kuwa asarar ta fi haka, ba makawa dole ne mu yarda da cewa lallai an ci mu da yaki.
Ku kalli irin hasarar tattalin arzikin kasa da ake ciki a halin yanzu, koda ba a bangaren da ake yakin ba, a dalilin yakin asarar ta shafe mu. Ku kalli yadda yawan marayu ke ta karuwa, wa zai kula da su? Ku kalli yadda yawan gwagware ke ta karuwa, wa zai zama majibancinsu? Ku kalli yadda jahilci ke ta bunkasa, gari nawa ne ba damar a bude makaranta? Kuma yaushe ne za a bude makarantun su zama kamar da? Ku kalli yadda lalacewar ta kai yau a ce ’yan Najeriya ne ke gudun hijira a kasashen Nijar da Kamaru da Cadi. Ga shi nan har sun fara korafin cewa an yi masu yawa a kasashensu. To dama me ke gare su da za su iya daukar nauyin ’yan Najeriya, in ban da lalura irin ta yaki?
To wai da kuke ta yin tafiyar hawainiya cikin al’amarin, har sai yaushe ne kuke ganin za ku tashi ku yi hobbasar ganin kun fuskanci yakin nan gada-gadan? Ku tuna fa, ga ’yan matan Chibok can kusan su 300 a hannun ’yan Boko Haram, sun share sama da watanni bakwai, har yanzu ba ku karbo su ba. Tun kuna ce mana kuna bin abin cikin hanyar hikima ne, kuka dawo kuka ce kuna sulhu da ’yan Boko Haram ne. Tun muna yarda har yanzu ta kai zukatanmu sun samu shakku a cikin maganganun da suke fitowa daga bakinku, kuna fa ji, kuna gani; yanzu har da ’yan mata cikin kai hare-haren bom. Anya kuwa ba ’yan matan Chibok ne ba? Idan ma su ne, duk wannan yana cikin sakacinku, domin a lokacin da aka sace yaran nan, jihohin suna cikin dokar-ta-baci ne, wato karkashin kulawar ku.
Yanzu ya kuke son mu yi? Mu fa tsoro da fargaba da taraddadi ya yi mana yawa a cikin zukatanmu, duk abin da muke yi cikin tashin hankali muke yin shi; tun da mun san ba mu cikin kowane mataki na tsarin tsaro. Masu tsare mu su ma sun kasa tsare kansu ballantana mu. Har ta kai da mun fara tunanin yaya za mu yi mu tsare kanmu. Ai ya zame mana dole mu fara irin wannan tunanin mana! To za mu zauna ne a rika kashe mu kamar kiyashi a dalilin jiran gawon shanu? Ba zai yuwu ba, sai dai ya kamata ku jami’an tsaro ku natsu tsaf, ku hankalta, ku yi nazarin makomar yin hakan. Za ku tarar da koma baya mai yawa a cikinta, domin in har farar hula zai matsu, tura ta kai shi bango, ya tunzura, ya dauki makamin kare kansa, to kuwa rashin katabus din jami’an tsaron ya yi yawa; ba na wasa ba! Kuma jami’an sun rasa kima da daraja mai yawa da da can suke da ita. Alhalin kuma a daya gefen ga gwamnati can tana yayata irin makudan kudin da take kashewa a kanku, don ku kare mu.
Shawarar da za n ba ku a nan ita ce, in dai har kun ankara kun gano wannan yakin ya fi karfinku, to ku sakar mana mara, mu yi zuciya, mu kare kanmu. Mutuncinku da kimarku ta zube a idonmu da idon duniya. A ganina, kamata ya yi ku koma ECOWAS ku nemi daukin sauran kasashen Afirika su tallafa muku da sojoji kamar yadda aka saba yi. Ko ku kai wa Majalisar dinkin Duniya kokenku, ta tallafa maku, tunda yaki ne da ’yan ta’adda. Hakan ya fi da ku ce za ku iya magance shi, alhalin ba za ku iya ba. Ga shi girma da kimarku na ta zubewa kuma ana cewa kuna samun nasara, alhali irin nasarar mai ginar rijiya ce kuke samu, yana kara yin kasa, shi kuwa yana cewa ya ci gaba.
A karshe, ya ku jami’an tsaron Najeriya, ku sani cewa har yanzu muna da fata tagari da alheri a kanku da burin ganin kun mike, kun jajirce, kun tunkari ’yan Boko Haram gadan-gadan da gaggawa. Ku sanya niyyar haka a zuciyarku, nasara na tare da ku. adduarmu na tallafawa da haskaka maku. Allah Ya ba ku sa’a, Ya yi maku jagora, amin!