Tambayoyi da amsoshi 100 domin mata (2)
Tambaya ta 5: ldan wani digon jini kadan ya fito wa mace a ranar azumin Ramadan ita kuma matar tana azumi shin azuminta ya inganta? Amsa: Eh azuminta ya inganta kuma wannan digon jini kankane ba komai ba ne domin daga jijiya yake. Aliyu bin Abu Dalib, (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Wannan […]
Tambaya ta 5: ldan wani digon jini kadan ya fito wa mace a ranar azumin Ramadan ita kuma matar tana azumi shin azuminta ya inganta?
Amsa: Eh azuminta ya inganta kuma wannan digon jini kankane ba komai ba ne domin daga jijiya yake. Aliyu bin Abu Dalib, (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Wannan digon jini kamar habo ne na hanci, ba haila ba ne, haka AIi bin Abi Dalib (RA) ya ambata.
Tambaya ta 6: ldan mace ta ji dumin jini amma jinin bai fito kafin magariba ba, ko kuma ta ji radadi na ciwon al’ada amma kuma jinin bai zo ba, shin azuminta na wannan ranar ya inganta ko ya wajaba ta rama?
Amsa: Idan mace ta ji dumi na haila kuma tana azumi amma kuma hailar ba ta fito ba sai bayan Sallar Magriba, ko kuma ta ji radadi na haila amma jinin bai zo ba sai bayan Sallar Magariba bayan faduwar rana, to azuminta na wannan rana ingantacce ne kuma ba za ta rama wannan azumi ba in na farilla ne kuma ladan azumin bai baci ba idan azumin ya kasance na nafila ne.
Tambaya ta 7: ldan mace ta ga jini amma ba ta tabbatar cewa jinin haila ba ne mene ne hukuncin azuminta a wannan rana?
Amsa: Azuminta ya inganta a wannan rana domin asalin jinin ba na haila ba ne, har sai lokacin da haila ce ta bayyana a gare ta, sannan azuminta zai baci.
Tambaya ta 8: Wani lokaci mace tana ganin wani gurbi na jini dan kadan ko kuma wani kankanen digon jini daban da wani lokaci ta gan shi a lokacin al’adarta, wani lokaci, kuma ta gan shi ba a lokacin al’adarta ba, to mene ne hukuncin azuminta a wadannan halaye guda biyu?
Amsa: Amsar tambaya mai kama da wannan ta gabata a baya, sai dai idan wannan digo ya zo ne a lokacin hailarta kuma ta Iura da cewa yana daga cikin jinin al’ada wanda ta sani to wannan ya kasance haila.
Tambaya ta 9: Idan mace a lokacin al’adarta, ta ga jini a ranar farko amma a rana ta biyu ba ta ga jinin ba har tsawon wuni guda, mene ne a kanta, me za ta aikata?
Amsa: Abin da yake zahiri shi ne lallai wannan tsarki ko kuma bushewar jini da bai zubo ba, wanda ya auku ga wannan mata a kwanakin hailarta to a lissafin haila yake ba a daukarsa tsarki, don haka sai ta wanzu a cikin hani na abin da mai haila take bari – kamar Sallah, Azumi da sauransu.
Amma sashin malamai sun ce: wadda ta kasance tana ganin jini rana daya sannan a washegari ta ga babu jinin idan haka take yi to idan jinin ya zo haila ne, idan kuma ya dauke tsarki ne, sai ta yi ta kirgawa har sai ya kai kwana goma sha biyar, wato in ya karu za ta kara kwana uku, idan ya zarce ta yi wanka ta nemi magani. Idan wani watan ya zo za ta yi karin kwana uku, to idan ya kasance kowane wata tana yin karin kwana uku amma jinin ba ya tsayawa har ya kasance ta zama mai al’adar kwana goma sha biyar, to daga nan ba za ta sake yin karin ba idan wani wata ya zo idan jinin ya wuce wadannan kwanakin sai ta yi wanka, ta yi Sallah, ta ci gaba da yin ibada sannan ta nemi magani don ya zama jinin ciwo.
Kuma shi wannan karin kwanaki da ake yi, ba a lokaci daya ake yi ba, idan tana yin kwana uku ne da wani watan ya zo sai ta ga ya wuce kwana uku bai dauke ba, to sai ta kara kwana uku ya zama kwana shida ke nan, idan ya yi kwana shida bai tsaya ba sai ta yi wanka, ta yi Sallah ta nemi magani. To idan wani watan ya zo ta zama mai al’adar kwana shida ke nan. Idan jinin ya yi kwana shida bai tsaya ba sai ta kara kwana uku ya zama kwana tara. Idan ta yi kwana tara jinin bai tsaya ba sai ta yi wanka, ta yi Sallah. To haka za ta yi ta yin kari har zuwa lokacin da zai kai kwana 15 daga nan kuma ba wani karin da za ta sake yi.
Wannan shi ne zance mafi shahara a Mazhabar, Ahmad bin Hambali, (Allah Ya jikansa).
Za a iya tuntubar Malam Ahmad Adam Kutubi (SP) ta: 08036095723
Mu kwana nan