Tambayoyi da amsoshi 100 domin mata (7)
Matar da ake bin bashin azumin Ramadan na shekaru Tambaya ta 50: Mace ce ta sha azumin kwana bakwai lokacin da take jinin biki, har wani Ramadan ya zo ba ta biya ba, kuma a cikin Ramadan na biyu shi ma ta sha na kwana bakwai, kuma ya zamo tana ciyarwa saboda rashin lafiya da […]
Matar da ake bin bashin azumin Ramadan na shekaru
Tambaya ta 50: Mace ce ta sha azumin kwana bakwai lokacin da take jinin biki, har wani Ramadan ya zo ba ta biya ba, kuma a cikin Ramadan na biyu shi ma ta sha na kwana bakwai, kuma ya zamo tana ciyarwa saboda rashin lafiya da take tare da ita.
Sannan ga Ramadan na uku ya kusa zuwa, to mene ne hukuncinta?
Amsa: Kada mace ta zama kamar yadda tambayar take, wato in ba ta da lafiya ne babu damuwa, lokacin da ta samu lafiya sai ta biya na shekarar can baya da ta bara amma idan sakaci ne, to bai halatta a gare ta ba shan azumi ta yi sakaci ba ta biya ba, har wani Ramadan ya zo ba ta biya ba. In kuma ta yi haka to ta yi laifi.
An samu Hadisi daga A’isha (RA), ta ce “Ya kasance Annabi (SAW) yana azumi amma ba na iya biya sai an shiga watan Sha’aban, to idan muka lura da wannan Hadisi na A’isha (RA) yana nuna duk yadda za a yi mutum ya biya kafin Ramadan. To ita wannan mata ta duba ta gani in da gangan ne ta yi gaggawar tuba ga
Kada mace ta zama kamar yadda tambayar take, wato in ba ta da lafiya ne babu damuwa, lokacin da ta samu lafiya sai ta biya na shekarar can baya da na bara amma idan sakaci ne, to, bai halatta gare ta shan azumi, ta yi sakaci ba ta biya ba, har wani Ramadan ya zo ba ta biya ba.
Allah (SWT) ta kuma biya abin da ake bin ta. In kuma rashin lafiya ne, to Allah Ya sani, Shi Ya sa ta jinkirta shekara daya ko biyu, to babu laifi, duk lokacin da ta samu lafiya, sai ta rama abin da ake bin ta.
Tambaya ta 51: Mace ce ta sha azumi amma ba ta rama ba kuma ga sabon azumi ya zo?
Amsa: Wanda ta jinkirta ba ta rama ba har wani Ramadan ya zo, to ta tuba ga Allah (SWT) da wannan mummunan aiki da ta yi don bai halatta ba mutum ya yi jinkirin biyan azumi har wani Ramadan amma ba na biya sai a watan Sha’aban.
” Wannan Hadisi na A’isha (RA) bai halatta ga mutum ya yi jinkirin abin da ake bin sa na azumi har wani Ramadan ya zo ba. Don haka ta tuba zuwa ga Allah (SWT), in sabon azumin ya wuce sai ta biya amma za ta ciyar gwargwadon azumin da ta sha, amma in ya wuce ta rama.
Hukunci kan shan maganin hana haila don yin azumi
Tambaya ta 52: Mene ne ra’ayinku kan mace ta sha maganin hana ganin jini don ta yi azumi duka tare da jama’a?
Amsa: Ina tsoratar da wacce za ta yi haka don wadannan kwayoyi suna cutarwa sosai domin likitoci sun yi bincike suna cutar da mahaifa; a hana jini fita kuma yana cutar da jijiyoyi, kuma yana cutar da jinin jiki don wannan jini Allah (SWT) Shi Ya kaddara wa mata ya fita, to, hana shi illa ce babba don haka ne muke gani ki yi azumi kawai lokacin da kika samu damar yi, amma in jini ya zo ki bar shi ya fito. in kin yi haka kin yarda da kaddarar Allah ke nan. Bayan ya wuce sai ki rama.