Tambayoyi da amsoshi 100 domin mata (8)

Tambaya ta 53: Wanne ne ya fi, mace  ta  yi Sallah a dakinta ne, ko ta tafi masallaci, in ya zamo akwai wa’azuzzuka da tunatarwa? Amsa: Abin da ya fi, mace ta yi Sallah a dakinta, saboda Hadisin Annabi (SAW), da ke cewa: “Gidajen mata shi ya fi alheri su yi SaIlah a ciki don […]

Tambayoyi da amsoshi 100 domin mata (8)

Iyayen Giji

Tambaya ta 53: Wanne ne ya fi, mace  ta  yi Sallah a dakinta ne, ko ta tafi masallaci, in ya zamo akwai wa’azuzzuka da tunatarwa?

Amsa: Abin da ya fi, mace ta yi Sallah a dakinta, saboda Hadisin Annabi (SAW), da ke cewa: “Gidajen mata shi ya fi alheri su yi SaIlah a ciki don fitar mata akwai fitina a ciki. Don haka mace ta zauna a dakinta ya fi mata aIheri. Dangane da wa’azi kuma da ta ji a masallaci ta samu kaset ta sanya a dakinta ya fi.

Tambaya ta 54: Yaya hukuncin dandana abinci ga mace mai azumi da rana, don ta ji ko gishiri ya ji?

Amsa: Idan har an dandana ba a hadiye ba aka tofar, wani abu bai wuce makogwaro ba, to babu damuwa, azumi bai karye ba.

Tambaya ta 55: Ni mace ce, na yi barin cikina a wata uku tun shekara guda ban yi Sallah ba har sai da na yi tsarki, sai aka ce min dole ne sai na biya wadancan salloli ni kuma ban san yawansu ba?

Amsa: Abin da yake sananne ga malamai, in cikinta ya zuba da wata uku, idan (abin da ta haifa) halittarta uku na mutum cikakke ne, to wannan jini da ya biyo jini ne na nifasi (wato haihuwa) ba za ta yi Sallah ba, ba za ta yi Azumi ba, idan kuma halittar ba ta cika ba, wannan jini na ciwo ne, sai ta ci gaba da SalIah, amma ta nemi magani. To sai ta yi tunani in cikin ya zube ne ko ta yi bari, in ya kai kwana 80, sai ta biya Sallar kwana tamanin in kuma ba za ta iya sanin kwanakin ba, to sai ta yi ta yin SalIah har sai ta sakankance ta biya Sallar da ake bin ta.

Tambaya ta 56: Ni ce tunda Azumi ya wajaba  a kaina ina yi. Sai dai kwanakin da nake haila ba na biyansu. To mene ne hukunci?

Amsa: Amma abin akwai bakin cikin in wannan abin ya faru tsakanin matan muminai, to ita wannan alamun abubuwa biyu: ko don jahiIci, ko don wulakanta addini. Dukkansu biyu masifa ne. Amma dai shi jahilci, maganisa neman iIimi da kuma tambayar abin da ba ka sani ba. Amma sakaci maganinsa tsoron Allah (SWT) da kuma kiyaye dokokinSa da kuma jin tsoronSa. In mutum yana aikata wannan to, ya yi gaggawa zuwa ga nemam yardar Allah. Don haka shawara ga wannan mata dangane da wannan aiki, ta tuba ga Allah, sannan ta yi kirdado ta biya gwargwadon ikonta abin da ta sha. Da wannan ne za ta kubutar da kanta. Muna kuma roka mata Allah Ya karbi tubarta.

Macen da haila ta zo mata bayan shigar lokacin Sallah

Tambaya ta 57: Mene ne hukuncin macen da haila ta zo mata bayan shigar lokacin Sallah, shin ya wajaba ta biya in ta yi tsarki. Kuma mace ce ta yi tsarki kafin fitar Sallah (wato lokacin Sallah)?

Amsa: Idan mace haila ya zo mata lokacin Sallah, ya wajaba ta biya wannan Sallah wacce ba ta riga ta yi ba jini ya zo mata, don Iokacin ya yi ba ta riga ta yi ta ba. Don Annabi (SAW) ya ce duk wanda ya riski Sallah a cikin Sallah ya samu Sallah. Haka ma idan mace ta riski gwargwadon raka’a daya a cikin Sallah, to za ta biya wannan Sallah. Haka kuma in mace ta yi tsarki, sai ta samu ko da raka’a daya ce to dole ne ta biya wannan Sallah.

Tambaya ta 58: Ina Sallah sai jini ya zo min?

Amsa: Idan haila ta  zo wa mace, ba za ta biya wannan Sallah ba, in ta yi tsarki. Don Annabi (SAW) ya ce ai mata ba sa Sallah ba sa Azumi. Don haka malamai suka ce ba za ta biya wannan Sallah ba. Amma kafin ta yi tsarki ko da saura raka’a daya, to za ta biya wannan Sallah in ta yi tsarki a wannan Iokaci.

Tambaya ta 59: Shin ruwan nan da ke saukowa mata fatsi-fatsi ko fari- fari bayan haila ta dauke najasa ne, ko ba najasa ba. Kuma kafin kowance Sallah sai an sake alwala?

Amsa: Wannan ruwa ba najasa ba ne sai dai in ya fito bayan an yi alwala yakan warware alwala, don ba sharadi ba ne a ce abin da ke warware alwala ya zamo najasa. Don ga tusa ba ta najasa jiki amma tana fitowa ta warware alwala. Don haka in ya fito tana da alwala tilas ne ta sake alwala. Amma in koyaushe haka yake fitowa to babu damuwa, ya zama irin mai ciwon yoyon fitsari ke nan.

Alwalar mace mai yoyon fitsari da wasu hukunce-hukunce a kanta

Tambaya ta 60: Mace ce ta yi Sallar Asuba da alwala alhali tana mai yoyon ruwa (fitsari), ya halatta ta yi Sallar Walaha da wannan alwala?

Amsa: Mai irin wannan yoyon ruwa ba ya halatta ta yi Sallar Walaha da alwalar Sallar Asuba don kuwa ba bayan Sallar Asuba take za a yi ba, sai bayan fitowar rana don ita mai wannan yoyon ai kamar mai ciwon istihala ne. Tilas ne ta yi alwala a kowace Sallah. Annabi (SAW) ya ce mai istihala tilas ne ta yi alwala a kowane Sallah. Lokacin salloli kuma ga shi:

  1. Lokacin Sallar Azahar: Da zarar rana ta dan karkata da tsakiyar sama har zuwa La’asar.
  2. Lokacin Sallar La’asar: Daga shigar SalIar La’asar har zuwa rana ta yi fatsi-fatsi har zuwa
  3. Sallar Magriba: Daga faduwar rana har zuwa bayan jan da ke yamma (wato Shafaki).
  4. Sallar Isha’i: Daga bayan Shafaki har zuwa dare na karshe, har zuwa fitowar
  5. Sallar Asuba: Daga fitowar Alfijir har zuwa dab da fitowar

Tambaya ta 61: Ya halatta mace mai irin wannan ciwo ta yi Sallar nafiIa na rabin dare da alwalar Isha’i.

Amsa: Bai halatta ba har in ta kai rabin dare. Ta sake aIwaIa. Wadansu kuma suka ce in dai ta tabbatar alwaIar tana nan ba sai ta sake alwala ba.

Tambaya ta 62: Yaushe ne karshen lokacin Sallar Isha’i kuma yaya zan yi in gane?

Amsa: Karshen lokacin Sallar Isha’i shi ne in dare ya raba. Yadda za a gane haka kuma ya raba tun daga faduwar rana zuwa fitowar Alfijir na biyu. To kashi na farko Iokacin Sallar Isha’i ke nan, kashi na biyu kuma shi ne lokacin Sallar Isha’i da kuma Sallar Asuba.