Tambayoyi da amsoshi kan kimiyya da kere-kere (3)

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Bello. Wadannan kafafe dai na samun kudaden shiga ne ta hanyoyi da yawa. Shahararru daga cikinsu su ne: tallace-tallace da suke karba daga wajen kamfanonin kasuwanci da ke kasashen duniya daban-daban da kuma sayar da kididdiga ko alkaluman adadin masu rajista da su, da kuma bayar da shawarwari ga […]

Tambayoyi da amsoshi kan kimiyya da kere-kere (3)

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Bello. Wadannan kafafe dai na samun kudaden shiga ne ta hanyoyi da yawa. Shahararru daga cikinsu su ne: tallace-tallace da suke karba daga wajen kamfanonin kasuwanci da ke kasashen duniya daban-daban da kuma sayar da kididdiga ko alkaluman adadin masu rajista da su, da kuma bayar da shawarwari ga kamfanonin kasuwanci ko hukumomin gwamnatocin wasu kasashe a duniya, sai kuma manhajoji da suke kirkira wadanda ake iya amfani da su wajen ci gaban kasuwanci da sadarwa. Galibi suna sayar da wadannan manhajoji ga manyan kamfanonin duniya na kasuwanci wadanda suka kasaita.  

Wadannan hajoji da na lissafa kadan ne cikin abubuwan da suke yi wajen samun kudaden shiga. Kuma hakan ya danganci kamfanin sadarwa. Ma’ana ba tsari iri daya suke amfani da shi ba. Misali, bayan kamfanin Twitter da Facebook, hatta Google, da Yahoo! da Microsoft da Baidu (na kasar Sin), duk suna da nasu tsare-tsare.

A bangaren Facebook suna dora tallace-tallace na hajojin kamfanoni. Idan ka hau shafinka a bangaren sakonnin jama’a (News Feed), za ka ga wasu sakonni cikin hotuna ko bidiyo ko rubutattun sakonni na wasu kamfanoni ko hukumomin gwamnati, ba mutane ba, wadanda kuma ba abokanka ba ne.  Baka ma sansu ba. Idan ka lura a gefen hotunan ko sakonnin, ko a sama da su kadan, za ka an rubuta: “Ad” ko “Adbertisement”; alamar cewa tallace-tallace ne. Bayan wannan, Facebook na iya tallata maka sakonnin da kake rubutawa a shafinka (Facebook Page), wanda ka bude don yada wata manufarka ta siyasa ko kasuwanci. Haka idan karantarwa kake yi, duk kana iya bai wa Facebook talla su tallata maka abin da kake yadawa na manufa. Kusan dukan bankunan Najeriya suna bai wa Facebook talla ta hanyoyi daban-daban.  

Sannan hatta adadin masu rajista a Facebook da yawan shafukan da suke budewa da yawan sakonnin da suke zubawa a shafukansu da kuma yawan abokansu da kasa ko garin da suke zama da abubuwan da suka rubutawa na tarihinsu da kuma yawan “Like” da suke matsawa a kan kowane sako suka gani ko karanta, duk wadannan abubuwa da na zayyana, hajoji ne ga kamfanin Facebook kuma yana iya “sayar” da su ga kamfanoni a yanayi da farashin da ba ka taba tunani ba. Abin sirri ne.

A bangaren Twitter ma suna da wannan tsari, sai dai tsarinsu ya sha bamban da na Facebook.  Sannan Facebook ya fi Twitter yawan jama’a da shahara da kuma tsabar dukiya. Domin alkaluman sun nuna cewa adadin masu dora tallace-tallace ma a Twitter ya ragu matuka, musamman tsakanin shekarar 2014 zuwa 2016. Wannan ya sa har masu kamfanin suka fara yunkurin sayar da kamfanin gaba daya, amma a karshe hakan bai yiwu ba.

Daga cikin manyan kamfanonin sadarwa da suka fi kowa yawan dora tallace-tallace a duniya akwai Google da Microsoft da kuma Yahoo!. Wadannan su ne iyaye a fannin karba da bayar da tallace-tallace a shafuka, saboda damar da suke da ita ta sanya tallace-tallacen a shafukan neman bayanai da mutane ke amfani da su a kowace dakika na lokacin duniyar nan. 

Dangane da tambayarka ta biyu kan tsarin da Youtube ke bayarwa na sanya tallace-tallace da abin hasafi da yake bayarwa ga wadanda suka yi rajista da wannan tsari, lallai akwai ka’idoji da suka tanada da kuma sharudda da suka gindaya ga mai son yin hakan. Da farko dai tukun, ya kamata ka san cewa shafin Youtube dai shafi ne da kamfanin “Alphabet Inc.” (Kamfanin Google) ya mallaka. Kuma shafi ne da ke dauke da sakonnin bidiyo, wadanda jama’a ke zubawa ko lodawa. Su abin da suka tanada shi ne mahalli da ma’adana. Amma hakikanin bidiyoyin da ke kan wannan shafi duk jama’a ne ke zuba su. An kiyasta cewa a duk minti daya, ana kallon sakonnin bidiyo da tsawonsu ya kai sa’o’i biliyan uku! Ma’ana, yawan bidiyon da ake kallo a duk minti guda, idan aka tara tsawon lokacin da sakonnin bidiyon suka dauka ana kallonsu, ya kai awanni ko sa’o’i biliyan uku.

Shafin Youtube na karbar tallace-tallace daga kamfanoni kamar sauran shafukan da bayanansu suka gabata. Sannan yana dora wadannan sakonni ne ga masu kallon bidiyon da ke shafin, ta hanyoyi daban-daban. Hanya ta farko ita ce ta amfani da tsofa tallace-tallacen bidiyon a farkon bidiyon da jama’a ke kallo. Wannan tsari shi ake kira “Embedded bideo Ads.” Da zarar ka budo bidiyo za ka kalla, za ka fara cin karo da talla ne na tsawon dakika biyar (5 seconds). Daga nan sai a isar da kai ga bidiyon da ka budo. Haka idan bidiyon na da tsayi, bayan wasu lokuta ma za ka sake cin karo da talla.  Haka dai har ka gama kallonka. Manufa dai ita ce, idan ka matsa kowanne daga cikin bidiyon da ke dauke da tallar nan, to, shafin Youtube ya ci kudin kamfanin da ya ba shi tallar. Sannan akwai tsarin loda tallace-tallace a tsakanin gungun sakonnin bidiyo da ke shafin, a gefensu, ko a saman jadawalinsu, ko kuma a tsakaninsu. Idan ka lura sosai, a gefen wasu bidiyon za ka ga wata alama mai launin rawaya (Yellow), dauke da kalmar “Ad”. Wannan ke nuna wannan bidiyon na talla ne. Idan ka kalla, shafin Youtube ya ci kudin mai tallar.

Bayan haka, shafin Youtube ya kasu kashi uku ne. Akwai babban shafi, na kowa da kowa Ke nan, in da za ka iya kallon bidiyo kyauta, amma masu dauke da tallace-tallace, kamar bayanin da na yi a sama ke nan. Sai kuma bangare na biyu, mai suna: “Youtube Red”, wanda ke dauke da nau’ukan bidiyo marasa tallace-tallace a ciki ko harabarsu. Shi wannan bangare ba kowa ke iya shiga ba sai wanda ya yi rajista kuma ya biya kudi. Idan kana bukata, a duk wata za ka rika biyan Dala goma ne ($10), kwatankwacin Naira dari uku da hamsin ke nan (N350), akalla. Sai bangare na karshe, wanda ke dauke da nau’ukan bidiyo ne daga tashoshin talabijin na duniya, shahararru. A wannan tsari ko sashe, dukan shirye-shiryensu ne suke watsawa, amma ta hanyar tashar Youtube. Wannan shi suke kira: “Youtube Tb”, kuma shi ma na kudi ne; ya ma fi “Youtube Red” tsada. Iya kudinka iya shagalinka.

Nau’ukan bidiyon da ke shafin Youtube sun kunshi wadanda jama’a ke lodawa don kashin kansu da wadanda tashoshin talabijin suke lodawa da wadanda kamfanonin fina-finai ke lodawa da sauransu. Har wa yau, akwai nau’ukan bidiyo masu dauke da wakoki na shahararrun (tantiran) mawakan duniya duk a ciki. Wadansu masana na ganin cewa duk wani ilimi da kake son koyonsa, idan ka hau shafin Youtube, akwai tabbacin wani ya taba yin bidiyo ya yi bayani a kansa. 

Bayan tallace-tallace da suke dorawa na kamfanonin kasuwanci, shafin Youtube na bai wa masu mu’amala da shi damar dora tallace-tallace a kan bidiyon da suke lodawa, don su ma su samu wani abin hasafi. Wannan tsari shi ake kira: “Youtube Monetization Programme.” Tsari ne da ke ba ka damar samun kudaden shiga ta hanyar sakonnin bidiyo da kake lodawa a tasharka ta Youtube.  Sharuddaan dai su ne kamar haka:

Za mu ci gaba.