Tambayoyi da amsoshi kan kimiyya da kere-kere (4)

Na farko dai dole ne ka mallaki tasha (Channel) a shafin Youtube. Hakan kuwa zai yiwu ne ta hanyar yin rajista a shafin. Shi kuma rajista na yiwuwa ne ta hanyar adireshin Imel na kamfanin Google, wato Gmail ke nan. Idan kana da adireshin Gmail, to, kana iya hawa shafin sai ka matsa: “Sign In,” […]

Tambayoyi da amsoshi kan kimiyya da kere-kere (4)

Na farko dai dole ne ka mallaki tasha (Channel) a shafin Youtube. Hakan kuwa zai yiwu ne ta hanyar yin rajista a shafin. Shi kuma rajista na yiwuwa ne ta hanyar adireshin Imel na kamfanin Google, wato Gmail ke nan. Idan kana da adireshin Gmail, to, kana iya hawa shafin sai ka matsa: “Sign In,” inda za ka shigar da suna da kalmar sirrin Imel dinka.  

Abu na biyu shi ne mallakar tasha, wato: “Channel” ke nan. Ka kiyasta “tasha” a matsayin “Profile Page” dinka ne a shafin Facebook. Nan ne ke dauke da yawan tashoshin da ka yi rajista (Subcribe) da su da sauran tsare-tsaren da suka shafi sunan tashar da sauran bayanai. A nan ne har wa yau kake da dakin shirye-shiryenka, wato: “Studio”, inda ta nan za ka iya loda bidiyon da ka yi, ka gyara shi da canja wa shafinsa siffa da dai sauran hanyoyin kayatarwa.

Abu na uku shi ne yin rajista don karbar tallace-tallace daga shafin Youtube.  Wannan tsari, kamar yadda na ayyana a sama, shi ake kira: “Youtube Monetization Programme.” Idan ka hau tasharka za ka ga alama mai dauke da wannan tsari. Sai ka matsa don yin rajista. Yin rajista na da sharudda. Na farko daga cikin ka’idojin rajista sai ka mallaki rajista da tsarin “Google Adsense,” wanda shi ne asalin tsarin da ke lura da biyan masu bai wa Google damar dora tallace-tallace a shafukansu na Intanet. Daga can tashar naka za su cillo ka shafin Google Adsense, don ka yi rajista. Idan ka gama, za a koma da kai tasharka ta Youtube, don ci gaba da yi maka tambayoyi.

Abu na hudu shi ne, bayan ka gama rajista, ba nan take za a fara dora talla a kan sakonnin bidiyonka ba. Dole sai ka mallaki adadin masu rajista a tasharka da suka kai dubu daya (1,000 subscribers). Sharadi na biyu kuma, dole ne ya zama an kalli sakonnin bidiyo a shafinka wanda tsawon lokacinsa ya kai sa’o’i dari hudu (400).

Abu na karshe, shi ne, shafin Youtube bai yarda ba ka dora bidiyo masu da dauke da tsantsar batsa, ko cin mutuncin wata al’umma ko addini kai-tsaye, ko kuma nuna tsana ga wani jinsi, ko kuma masu dauke da hanyoyin koyar da miyagun ayyuka ko satar yara ba, misali.

Da zarar ka cika wadannan ka’idoji da sharudda, nan take za a fara dora sakonnin tallace-tallace a kan bidiyon da kake lodawa, don bai wa masu kallonsu damar kaiwa gare su. Akwai iya adadin da ake la’akari da shi kafin a fara biyanka. Sauran bayanai kuma sai in ka shiga cikin tsarin tsundum. Allah Ya sa a dace, kuma da fatan ka gamsu da wannan gajeren bayani.  


Assalamu alikum. Ina yi wa Malam fatan alheri, Allah Ya kara nisan kwana mai amfani. Don Allah Malam yaya zan yi in samu adireshin Imel mai suna “info”?  Misali: [email protected]. Na gode. Sako daga Yahuza Idris Hotoron Arewa. Kano. 08039180699: [email protected] 

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Yahuza. Da fatan kana lafiya. Mallakar adireshin Imel mai wannan suna na samuwa ne idan kana da adireshin Gidan Yanar Sadarwa, wato: “Website Address.” Kafin ka bude Gidan Yanar Sadarwa jama’a su iya isa ga bayanan da ka zuba, dole ne sai ka sayi adireshi. Wannan adishireshi kuwa shi ne kwatankwacin: www.babansadik.com. Da zarar ka mallaki wannan, sai ka sayi muhallin da za ka dora Gidan Yanar Sadarwar.  Wannan muhalli shi ake kira: “Hosting”. A cikin tsare-tsaren “hosting” din galibi kamfanin da ka yi rajista da shi don adana maka shafinka, zai hada maka da manhajar Imel na kai-tsaye, wadda za ka iya zabar irin sunan (username) da kake so. Idan “info” din kake so, kana iya zaba.  

Amma idan ta manhajar Imel ta Intanet ne irin su Gmail da Yahoo!, zai yi wuya ka iya mallakar irin wannan suna. Da fatan ka gamsu.


Salamun alaikum Abban Sadik, barka da yamma. Ina fatan kana lafiya. A gaskiya ina jin dadin karanta jaridar AMINIYA, hakan ya sa na ji koyaushe ina tare da ita. Na kasance ina nuna so da kauna a gare ka duk da ban taba ganinka ba, amma wallahi kana barge ni kuma kana sa ni nishadi a koyaushe.  A karshe ina yi maka fatan alheri. Daga Nura Jigawa: 09063340724.


Wa alaikumus salam, Malam Nura barka dai. Ina godiya matuka da nuna kauna da kake min, tare da kebance ni da wannan kaunar. Allah Ya saka da alheri, musamman da ka sanar da ni. Ni na ina kaunarka don Allah. Kuma ina rokon Allah Ya hada fuskokinmu da alheri a ko’ina muke. Allah kuma Ya kara fahimta cikin abin da kake karantawa daga gare ni. Na gode. Na gode.  Na gode.


Assalamu alaikum; gaskiya ba abin da za mu ce sai dai Allah Ya kara basira.  Baban Sadik don Allah mene ne bambancin “Jaba” da “Python”? Kuma wanne ne ya fi saukin koyo? Na gode. A. A. Namada: 08168315523.

Wa alaikumus salam Malam Namadi, muna godiya da sakonka. Da farko dai zai fi dacewa mu yi takaitaccen bayani kan kowanne daga cikin wadannan nau’ukan dabarun gina manhajar kwamfuta da wayar salula guda biyu, kafin mu san mene ne bambancin da ke tsakaninsu. Mu fara da Jaba:

“Jaba” – Wannan yare mai suna “Jaba” an samar da shi ne a shekarar 1995, ta hanyar kokarin wani bawan Allah mai suna: James Gosling. Tsari da kintsin “Jaba” sun samo asali ne daga yaren “C++”, bambancin da ke tsakaninsu ba ya da fadi sosai. Ana amfani da yaren Jaba wajen gina abubuwa da yawa, daga manhajojin sarrafa injuna zuwa na wayar salula. Kashi 80 cikin 100 na manhajojin wayar Android duk da yaren “Jaba” aka gina su. Haka galibin manyan manhajojin kwamfuta na zamanin yau, duk da “Jaba” aka gina su.  “Jaba” ita ce “amarya” a tsakanin dabarun gina manhajojin kwamfuta.

“Python” – Wannan yare an samar da shi ne a 1990, ta sanadiyyar kokarin Guido ban Rossum, wani masanin fannin lissafi dan kasar Holland. Ana amfani da wannan yare wajen gina shafukan Intanet, da manhajojin kwamfuta masu amfani da Intanet. Shahararru daga cikin manhajoji da shafukan da aka gina da “Python” dai sun hada da: shafin “Youtube” da “BitTorrent” da wani bangaren manhajar “Facebook” da “Yahoo Maps” da “Google” da “Pinterest” da “Instagram” da “Drop Bod,” da “Firefod” na kamfanin Mozilla, da manhajar “Blender,” da “Cinema 4D” da sauransu.  Sannan a daya bangaren kuma, ana amfani da “Python” wajen gina manhajojin wayar salula na Android, ta amfani da wani yare mai sauki mai suna: “Kiby.”  Wannan yare na “Python” yana da matukar sauki wajen koyo, kuma da “Python” kana iya gina duk irin manhajar da ka ga dama, muddin kana da kwarewa da kuma zimmar yin hakan.

Bambancin da ke tsakanin wadannan yaruka guda biyu dai ba wani mai yawa ba ne can-can. Da farko dai dukansu yaren gina manhaja ne na zamani masu amfani da salon gina manhaja mai suna: “Object-Oriented Programming – (OOP). Sannan dukansu na cikin sahun yarukan gina manhaja na sama-sama wadanda ake wa lakabi da: “High Lebel Programming Languages,” domin sun sha bamban da yaren “C”, wanda ke da alaka ta kai-tsaye da kwakwalwar kwamfuta. Bayan haka, kowannensu ana amfani da shi wajen gina manhajar kyauta, wanda tsari ne da ake kira: “Open Source.” Wadannan manyan siffofi uku su ne abubuwan da suka hada alaka tsakaninsu.

A daya bangaren kuma, yaren “Jaba” ya fi shahara a duniya, kuma an fi amfani da shi sosai wajen gina manhajojin kwamfuta da na wayar salula fiye da Python.  Sai dai kuma, Python ya fi Jaba saukin koyo, da saukin al’amari, da kuma saukin fahimta wajen karantarwa. Abin da za ka rubuta shi cikin layi ko sadara daya da yaren Python, sai ka rubuta sadara uku ko hudu in a yaren Jaba ne.

Bayan haka, yaren Python ya fi shahara a fannin nazarin bayanai a duniya yanzu, wato: “Data Analysis.” Sannan an fi amfani da shi wajen gina manhajojin kwamfuta masu kwaikwayon dabi’un kwakwalen mutane, wato: “Machine Learning” ko “Deep Learning Applications.” Wannan ya faru ne saboda kwararru da aka samu masu lura da wannan yare, wadanda suka kirkiri dabarun nazarin bayanai da koya wa kwamfuta yin abubuwan da kwakwalwar dan adam ke iya yi na fahimta, cikin yaren. Shahararru cikin tsare-tsaren dake taimakawa wajen aiwatar da hakan kuwa sun hada da: “Matplotlib”, da “SciPy”, da “SymPy”, da “TensorFlow”, da “Pandas”, da “Numpy”, “SciKit Learn” da dai sauransu.