Tambayoyi da amsoshi kan kimiyya da kere-kere
Salamun alaikum, barka da dare da fatan kana lafiya. Don Allah Baban Sadik ina son a dan yi mini karin bayani a kan shafin “Paypal.” Daga Usman Aliyu Kano: 08133533448: [email protected] Wa alaikumus salam, barka dai Malam Usman. Ina godiya matuka da addu’arka […]
Salamun alaikum, barka da dare da fatan kana lafiya. Don Allah Baban Sadik ina son a dan yi mini karin bayani a kan shafin “Paypal.” Daga Usman Aliyu Kano: 08133533448: [email protected]
Wa alaikumus salam, barka dai Malam Usman. Ina godiya matuka da addu’arka gare ni. Ina rokon Allah Ya sa mu yi tarayya cikin alheri baki daya, amin. Dangane da tambayarka, shafin “PayPal” dai shafi ne da ke bai wa mutane damar aiwatar da cinikayya ta hanyar biyan kudaden hajojin da suka saya a shafukan Intanet cikin sauki, tare da ba su dama har wa yau wajen aike wa ’yan uwansu kudade kai-tsaye, wato “Instant Money Transfer” ke nan. Idan kana da rajista da wannan shafi har wa yau, za ka iya karbar kudaden cinikin da ka yi na hajojin da kake tallatawa idan kana da shafin sayar da kayayyaki a Intanet. A takaice dai, kamfanin “PayPal” dai dillalai ne kan hada-hadar kudi a duniya ta hanyar Intanet. Ba wai banki ba ne mai zaman kansa.
Asalin wannan shafi dai ya faro ne daga babban shafin sayar da hajoji a Intanet mai suna: “Ebay,” daga nan ya fara hada-hadar kudi ta hanyar bai wa jama’a masu sayen hajoji a shafin “Ebay” damar biyan kudin hajojin da kuma bai wa ’yan kasuwa damar karbar kudaden da ake biyansu na hajojin da suke sayarwa a shafukansu na Intanet. Daga nan wannan shafi ya habaka. A halin yanzu dai akwai masu rajista da shi sama da miliyan 188 a duniya.
Kuma shafin na samun kudaden shiga ne ta hanyar cajin hidima da yake yi wa masu rajista da shi. A karon farko dai kamfanin yakan tara kudaden da yake karba a madadin masu rasjita da shi ne a bankuna, yana karbar kudin ruwa kai-tsaye daga bankunan, tunda suna aiwatar da kasuwanci da kudaden, kamar yadda yake a tsarin hada-hadar kudade na zamani a kasashen Amurka da Turai. Daga baya da masu rajista da wannan shafi suka gano haka, sai suka yi ta rufe “account” dinsu suna ficewa. Domin wannan, a tunaninsu, ci da ceto ne.
Wannan bore da jama’a suka yi ne ya sa kamfanin ya canja tsarinsa, inda ya rika dora wa masu rajista haraji a kan duk hidimar da ya yi musu. Harajin masu sayar da hajoji daban da na masu karba ko aika kudade ga ’yan uwa ko abokansu. A halin yanzu da wannan tsari kamfanin ke rayuwa. Idan ka kebe kasashen Indiya da Ghana da Japan da Afghanistan da Crimea da sauran kasashen da kasar Amurka ta sanya wa takunkumi, duk sauran kasashen duniya na mu’amala da wannan shafi. A halin yanzu an kiyasta cewa, shafin PayPal na iya karba tare da aika takardun kudade sama da 25 daga cikin nau’ukan kudaden duniya.
Yin rajista a shafin PayPal ba wahala. Bayanan da za ka bayar sun hada da sunanka cikakke da adireshin Imel da adireshin inda kake zaune da kasar da kake zaune da lambar wayarka, sannan da lambobin katin ATM dinka. Kana iya tambayar ko dole ne sai mutum yana da taskar ajiyar banki sannan zai iya karba ko aika kudi? Amsar ita ce: eh! Domin za a bukaci lambobin katinka na ATM, wanda ta hanyar lambobin ne za a iya zuba maka kudade a taskarka ta banki da ke kasar da kake. Ni kaina ina amfani da wannan tsari wajen sayen manhajojin kwamfuta a Intanet. Hatta wasu manhajojin da nake amfani da su wajen tafiyar da shafin Taskar Baban Sadik da ke: http://www.babansadik.com, irin su “Elementor Pro” da sauransu, duk da wannan tsari na biya kudadensu.
Wannan shi ne takaitaccen bayani kan shafin PayPal. Idan kana bukatar gamsassun bayanai, kana iya ziyartar shafin kamfanin da ke: www.paypal.com. Da fatan ka gamsu.
Assalamu alaikum Baban Sadik, jinjina gare ka, Allah Ya kara basira da ilimi mai amfani. Allah Ya daga darajar jaridar Aminiya. Sako daga Bello Mijinyawa Galadima Mayosir
Wa alaikumus salam, Malam Bello ina godiya matuka da wannan jinjina. Allah saka da alheri, ya kuma kara zumunci mai dorewa a tsakaninmu, amin. Aci gaba da kasancewa tare da Aminiya. Mun gode matuka.
Assalamu alaikum Baban Sadik, yaya aiki? Tambayata ita ce! Ina da waya nau’in “Tablet Tecno G9,” to amma ba ta hawa Intanet, kuma kamfanin layina sun turo mini da “Settings” amma sai dai ta rika nuna mini cewa “Data Serbice has blocked.” Shi ne nake son don Allah ka taimaka mini.Na gode. Daga Aminu Muhammad Kundila, Jihar Kano.
Wa alaikumus salam, barka dai Malam Aminu Muhammad. Ga alama dai matsalar kusa take. Watakila ka jefa ne a “Flight Mode”, ba tare da saninka ba. Sai ka duba bangaren “Settings” daidai wajen “WiFi” ko “Wireless” ko “Network Settings.” Idan har ba a “Flight Mode” take ba, zai yiwu akwai matsala babba da ke hana ta hawa Intanet. Domin a zamanin yanzu ma dai, muddin ka dora katin “SIM” dinka a kan waya ko “Tablet,” ba ka bukatar wani sakon “Settings” daga kamfanin waya.
Idan har abin ya ci gaba, kana iya kai ta wajen masu gyara, kwararru. Zan maimaita: kwararru. Don su duba maka ita. In kuwa babu wasu bayanai masu tarin yawa a kanta, kana iya “Resetting” dinta kawai. Komai zai koma yadda yake, kamar yanzu ka sayo ta. Allah sa a dace, amin.
Assalamu alaikum Baban Sadik, gaskiya ina karuwa sosai da rubuce-rubucenka musamman a kan abin da ya shafi Kimiyyar Samaniya da sauransu. Allah Ya saka maka da alheri, Ya kuma kara maka ilimi da aiki na ari, amin.
Wa alaikumus salam, barka dai. Ina godiya matuka da kaunarka gare ni. Allah saka da alheri, Ya kuma bar zumunci a tsakaninmu. Allah kuma Ya sa ana amfana da abin da ake karantawa. Idan an ga kuskure a rika tunatar da mu. Na gode matuka. Allah saka da alheri, amin.
Assalamu alaikum Baban Sadik, sunana Hamza, daga Toro, Jihar Bauchi. Baban Sadik wayata ce ta samu matsala; Serbice ya dauke gaba daya. Na kai gyara an kwance ba a ga matsala ba. Shin, ko akwai wata shawara. Daga Barista Hamza Tilde
Wa alaikumus salam, barka dai. A gaskiya ba zan iya sanin hakikanin abin da ke damunta ba, musamman ganin cewa ka kai wa masu gyara amma ba abin da ya canja. Kana iya canja mai gyara. Idan kuma za ka iya, ka yi “Resetting” wayar ko ka ce a yi mata filashin. Wannan zai mayar da ita baya kamar yadda aka kera ta a farkon lamari. Da fatan ka gamsu.
Assalamu alaikum mai gidana Baban Sadik, Allah Ya kara basira kuma da fatan kana lafiya. Wallahi karatun shafinka a jaridar Aminiya ya kai ni har na bi ka a Duniyar Computer. Allah dai Ya biya ka. Na gode. Ni ne: Muhammadu Sani Galadima: 08024080026.
Wa alaikumus salam Malam Muhammad. Muna godiya da wannan kebantacciyar kauna gare mu. Allah bar zumunci Ya kuma saka da alheri, amin.