Tambayoyi da kalubale game da Boko Haram
Al’amarin ta’addancin Boko Haram dai ya gallabi kowa a kasar nan, dalili ke nan kowa ke addu’ar Allah Ya kawo karshensa. Dalili ke nan ma ya sa MALAMA A’ISHA USMAN LIMAN (09093467171) ta dauki alkalami ta antayo tambayoyi da kalubale zafafa game da ’yan Baoko Haram da masu daure masu gindi, sannan ta karkare da […]
Al’amarin ta’addancin Boko Haram dai ya gallabi kowa a kasar nan, dalili ke nan kowa ke addu’ar Allah Ya kawo karshensa. Dalili ke nan ma ya sa MALAMA A’ISHA USMAN LIMAN (09093467171) ta dauki alkalami ta antayo tambayoyi da kalubale zafafa game da ’yan Baoko Haram da masu daure masu gindi, sannan ta karkare da cewa lallai akidar tasu ba Musulunci ba ce ta kowane fanni. Ga abin da take cewa:
ISLAM – Ma’anar wannan kalma ita ce zaman lafiya, manufar ta kuwa bauta wa Allah (swa) kamar kana ganinSa. Kuma Annabi Muhammad (saw) bawanSa ne kuma manzonSa ne. Yana cikin imani ka yi imani da ranar lahira, ranar da za a tashi bayi, kowa a saka masa aikinsa. Yana cikin imani mutum ya so wa dan uwansa abin da yake so wa kansa na alheri. Wannan shi ne Musulumci da manufarsa.
Ta yaya wanda fatansa kar a zauna lafiya za a kira shi Musulmi, alhalin sunan Musulinci zaman lafiya? A cikin Islam ba ta’addaci, babu kisan kai ba tare da haddi na shari’a ba, ba wulakanta mutum. Ba a yarda ka ba shi tsoro ko ka aibanta shi ba. Ba ya halatta ga Musulmi ya zama abin fargaban abokin zamansa ko da ba addininsu daya ba. Zagin Musulmi ko aibanta shi, fasikanci ne.
Islam ya yarda da yaki kuma an yi yaki a Musulinci amma akwai sharuddan da ya gindaya kafin yakin ya hau kan Musulmi kuma a cikin yakin akwai wadanda ba a yarda a yake su ba. Misali, ba a yakar yara, ba za ka yaki mutum a cikin gidan bautarsa ba, koda ba addininku daya ba, balle wanda kake da’awar addininku daya da shi, ba ya halatta ka kai wa abonkin gabarka mamaya ta kowace irin hanya, wai don kana son ka yake shi, dole sai an shata fagen fama, ya sani ka sani.
Ta yaya Musulmi zai daura jigidar bom ya kashe kansa, ya kashe Musulmi ko akasinsa kuma a kira shi da sunan Musulmi? Alhalin Allah (s.w.a) Ya ce duk wanda ya kashe kansa ko wani rai ba da hakki ba sunansa Kafiri? Shi ne mu mun san da haka amma muke yin shiru ana danganta wadannan da ba su yarda da wata ka’ida ta Musulinci ba da mu? Babu ta’addan ci a Musulunci kuma bai yarda da shi ba har abada.
Ta yaya wani mutum zai sa ce matar wani ko diyar wani ko uwar wani, ya ce ta koma karkashin mallakarsa haka kawai don zalunci, sannan a kira shi da sunan Musulmi? Alhalin Allah bai yarda wani ya mallaki matar wani ba koda da zina ne, bai yarda wani ya kwace dan wani ba koda da kiransa tare da sunanka ne, Allah bai yarda da haka ba.
Ta yaya wani zai tarwatsa muhallin wani, ya kona, ya fidda shi gidansa haka kawai don zalunci kuma a kira shi Musulmi? Alhalin Allah bai yarda ka kai wa wani mutum hari har cikin gidansa ko cikin dakin bautarsa ba, koda ba Musulmi ba ne.
Wanne ne daga cikin wadancan ka’idojin ’yan Boko Haram suka sani kuma suke bi sau da kafa? Babu. To ta yaya za mu yarda da cewa su Musulmi ne, har wai a rika yi musu ikirari da sunan masu tsaurin addinin Musulunci? Mai tsaurin addini kam shi ne mai tsantseni da tsananin bautar Allah bisa dokokinSa.
Idan ma ta kasance kamar yadda ake rade-raden wai wasu ne ke amfani da su don a tagayyara Arewacin kasar nan, ko don wasu da ake son a azurta su ta hanyar zubar da jinin bayin Allah, to su ma su sani ba wata fuska ko akidar addini kowane iri da suka dogara da ita a kan wannan manufar tasu, domin dukkan addinan duniya ba wanda ya yarda da zalunci ko ta’addanci.
Wannan aikin aiki ne na jahilci da ta’addanci da zalunci da makircin wasu shashashan mutane, marasa ilimi da hankali da lura; wasu masu akidar sakarci da son kai na banza, marar amfani suke aikatawa, domin in ban da jahilci ta yaya za ka daura jigidar bama-bamai ka ratso mutane suna cikin bauta ko sha’anin rayuwarsu, ka tada musu bom ya kashe su da kai ga baki daya?
In ban da ta’addanci, ta yaya za ka raba mutum da ransa, ka raba iyaye da ’ya’yansu, ka raba mutum da muhallinsa haka kawai, don cikar wani burinka marar amfani?
In ban da zalumci, ta yaya wani ko wasu mutane kalilan za su hana jama’a ko al’umma sakat, su haddasa masu tsoro da fargaba da taraddadi a cikin zukatan al’ummarsu, gabas da yamma, kudu da arewa a cikin kasa?
In ban da makirci, ta yaya wasu za su so su yi kudi ko su samu rufin asiri a dalilin zubar da jinin wasu? Mene ne amfanin irin wannan arzikin? Ina za ka kai arzikin kuma me za ka yi da shi? Iyakar kowa da arzikin duniya a duniya, sai dai in ka yi aikin alheri da shi, ya bi ka lahira, ya amfane ka. To kai da ka kashe, sannan ka samu arzikin, to wane abin kirki ka yi ke nan? Wane amfani za ka gani gobe kiyama?
Wannan wane irin duhun kai ne haka? A hada kai da kai a zalunci al’ummarka da kai, a tarwatsa su, a kore su, a kashe su duk da sa hannuka? Domin ko mu so ko mu ki, “da dan gari aka nci gari” kuma “makashinka na tare da kai.” Wannan magana ta Bahaushe gaskiya ce kuma kowa ya san hakan take.
Amma mu ma sauran al’umma da ke wahala da ta’addancin ’yan Boko Haram mu sani kuma su ma shuwagabanninmu su sani cewa, wannan laifinmu ne kuma laifin kasar mu ce. Ta yaya ya zama laifinmu? Wadannan mutane ’yan Boko Haram, tun farko sun zo da sabuwar akidarsu wadda ba ta yi daidai da koyarwar alkur’ani da hadisi ba, a hankali suna ta yada ta cikin al’umma kuma mun sani, muna ji, muna ganinsu amma muka kawo ido muka sa musu. Sarakuna da malamai (in ban da marigayi Shaikh Jafar), ba wanda ya kwabe su ko ya yi kokarin dawo da su kan hanya, alhalin mun san ba za mu daidaita da akidarsu ba. Domin da tun farko mun daidaita da ubangidansu ‘Maitatsine.’
Ya zama laifin kasa ne, a dalilin sanin kowa kasa ita ke da alhakin kula da kai kawon dukkan al’ummara da kula da samar da duk wani sanadin da zai samar da zaman lafiya ga ’yan kasarta, tabbatar da tarbiya, bayar da ilimi, bin dokokin kasa da tsare su; duk hakkin kasa ne. Ba abin da kundi mulkinmu bai tanadar mana ba, sai dai kawai yanzu muna kan wata turba ce ta kowa tasa-ta-fisshe-shi. Da yau kasarmu ta zama mai ba da muhimmanici ga ilimi, da hakan ba ta same mu ba, domin da kowa ya waye, ya yi arziki, ba za a samu mai jahilcin da zai yi tunanin bada jinin al’ummarsa ko jama’arsa don ya yi arziki ba.
Daga karshe, muna kara jaddada sanarwa cewa Musulmi ba dan Boko Haram bane kuma Boko Haram ba Musulunci ba ne, ta’addanci ne!