Tambayoyi da sakonnin masu karatu ta imel da tes
Salamun alaikum Baban Sadik da fatar kana lafiya. Ni ma’abocin karanta shafinka ne, amma ban taba rubuto tambayata ba sai yau. Ina son in san ta yaya nau’in tauraron dan Adam na sadarwa yake aiki wajen nuna tashoshin talabijin? Saboda abin yana ba ni mamaki. Daga Abubakar Sa’idu Dankanjiba: 08136346418 Wa alaikumus salam, barka dai […]
Salamun alaikum Baban Sadik da fatar kana lafiya. Ni ma’abocin karanta shafinka ne, amma ban taba rubuto tambayata ba sai yau. Ina son in san ta yaya nau’in tauraron dan Adam na sadarwa yake aiki wajen nuna tashoshin talabijin? Saboda abin yana ba ni mamaki. Daga Abubakar Sa’idu Dankanjiba: 08136346418
Wa alaikumus salam, barka dai Malam Abubakar. Mun dade muna kwararo bayanai kan ma’ana da tarihi da tsarin gudanuwar tauraron dan Adam, sama da shekara bakwai da suka gabata, a wannan shafi mai albarka. Cikin bayanan da muka yi mun nuna akwai nau’o’in tauraron dan Adam, wanda daga ciki aka samu na harkar sadarwa. Tauraron dan Adam ne da aka harba shi sama, watsa bayanan sadarwa na sauti ko hoto mai motsi, wato bidiyo ke nan. Wadannan nau’o’in taurarin dan Adam su ake kira: “Communication Satellites”. Kuma su ne suke cilla shirye-shiryen gidajen talabijin na tauraron dan Adam, wato “Satellite TB Channels” daga kasashen da ake harbawa ko watsa su.
Wadannan shirye-shirye dai ana loda su ne daga cibiyar watsa shirye-shiryen, sannan a haska su ta amfani da wadannan taurarin dan Adam da aka riga aka harba su tunda jimawa, suna shawagi a cikin falaki ko sararin samaniya. Duk shirin da aka loda, ana saita masa lokacin da tauraron zai nuna shi, da ranar da ake son shirin ya bayyana ga masu kallo. Misali, shiryen-shiryen talabijin din Hausa na Sunnah TB, ana cilla su ne daga tashar watsa shirye-shirye da ke kasar Nijar.
A halin yanzu dai akwai taurarin dan Adam masu dimbin yawa a cikin sararin samaniya, wadanda aka cilla su don aiwatar da ayyuka daban-daban. Akwai na gano bigire, wadanda galibin manhajar taswirar duniya ke amfani da su, irin su: “GPS” na kasar Amurka da “GLONASS” na kasashen Turai da dai sauransu. Bayani kan hakikanin yadda abin ke faruwa ko aukuwa kuma, wannan wani darasi ne mai zaman kansa. Da fata ka gamsu.
Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya. Don Allah idan mutum ya saci Pin dinka na katin banki, shin, zai iya sace kudinka ba tare da ya sami katin ATM ko wayarka ba? Ka huta lafiya. Daga Misbahu Ibrahim Musa Fagwalawa: 08079903302
Wa alaikumus salam, Malam Misbahu barka ka dai. Masu irin wannan mummunar dabi’a suna da hanyoyi da dama da suke bi wajen aiwatar da badakalarsu. Kamar yadda Malam Bahaushe ne kan ce: “Mai son kayanka ya fi ka dabara.” Abu ne mai yiwuwa tabbas wanda ya san PIN din katinka na ATM ya iya sace maka kudi ba tare da ya samu katinka na ATM ba, kuma ba tare da ya san lambar wayarka ba. Wato a wannan zamani na sadarwa, su bayanan da suka shafi mutum suna da alaka ne da junansu. Misali, idan mutum ya san adireshinka na Imel, ko sunan da kake amfani da shi wajen hawa shafinka na Facebook, to, zai iya kirdadon kalmar sirrinka, wato: “Password” ke nan, iya gwargwadon abin da ya sani dangane da rayuwarka.
A bangaren barayin banki ta kafafen sadarwa na zamani, ko ba a samu katinka na ATM ba, ana iya kera makamancinsa cikin sauki. Wannan shi ake kira: “ATM Card Cloning;” kamar a yi wani abu makamancin naka, amma kuma asalinsu daban-daban ne. Abin da zai hada alaka tsakaninsu kawai shi ne bayananka na banki. Misali, lambar taskar bankinka, wato: “Account Number,” ko lambar katin ATM dinka, wato: “ATM Serial Number.” Idan na ce lambar katin ATM ba ina nufin “PIN” dinka ba ne. A’a wadannan dogayen lambobin nan guda 16 ko 14 da ke kan katinka na ATM. Suna da amfani matuka wajen dan dandatsa. Domin ko hajoji za ka saya a kafafen sadarwa na zamani da wadannan lambobin ne ake iya gane cewa kana da taskar ajiya a wani banki, kuma akwai kudi a ciki. Da wadannan lambobin ake iya tuntubar bankinka don su ba da umarnin a cire kudi daga taskar ajiyarka. Shi ya sa, idan ka taba aiwatar da cinikayya ta hanyar amfani da katinka na ATM, za ka ga bankinka ya aiko maka wasu lambobi da ake son ka shigar a inda kake son biyan kudi.
A takaice dai, abu ne mai yiwuwa a iya sace kudin mutum daga taskar bankinsa ba tare da an sace katinsa na ATM ba. Kawai ya danganci irin bayanan da barawon ya samu ne dangane da taskarka ko katinka na ATM. Shi ya sa bankuna suke wayar mana da kai a kullum, cewa, ba za su taba aiko maka sako don ka ba su lambar taskarka na banki ba (don suna da shi kuma sun sani), ko katin sirrin ATM dinka ba (don ba su bukatar wannan bayanin wajen magance maka wata matsala), ko lambar katin ATM dinka ba (don sun sani, kuma suna da shi). Duk sa’ar da ka samu sako ta waya ko Imel da ke cewa ka aika bayanan katinka na ATM ko lambar taskar bankinka ga wata lamba ko wani adireshi na Imel, ko ka matsa wata rariyar likau (Internet link) don shigar da wadannan bayanai a wani shafi na musamman, to, ka san cewa wannan sako ne na bogi. Kuma idan ka bayar, duk abin da ya same ka na asarar kudi da mutunci, ba ruwansu.
Da fatar za a kiyaye. Wannan shi ne dan takaitaccen jawabin da zan iya ba ka a yanzu. Da fatar ka gamsu.