Tambayoyi da sakonnin masu karatu ta imel da tes (4)
A wannan mako za mu ci gaba da amsa tambayoyin masu karatu ne kamar yadda muka faro makonni uku da suka shude. Kada a mance, a rika rubuto cikakken suna da adireshi a karkashi ko farkon sako. A sha karatu lafiya: —————————- Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatar kana lafiya kai da iyalanka. Wannan karon […]
A wannan mako za mu ci gaba da amsa tambayoyin masu karatu ne kamar yadda muka faro makonni uku da suka shude. Kada a mance, a rika rubuto cikakken suna da adireshi a karkashi ko farkon sako. A sha karatu lafiya:
—————————-
Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatar kana lafiya kai da iyalanka. Wannan karon shi ne na biyu da na rubuto maka wasika. Na rubuto maka wasikar ce domin na jinjina maka kan yadda ka yi gyare-gyare a shafinka na Taskar Baban Sadik. Gaskiya ya kayatar da ni sosai. Sai dai kuma a yanzu na samu bambanci; a baya idan ina karanta shafin zan iya karance shafin duka, amma yanzu gaskiya rubutun ya yi yawa ta hannun dama. Ma’ana rubutun ya yi wa wayata tsawo ba na ganinsa duka. Amma watakila ina tunanin matsalar wayata ce.
Daga Sunusi, Unashi Danko/Wasagu, Jihar Kebbi. 07054106655
Wa alaikumus salam Malam Sunusi, ina godiya da gaisuwa. Lallai kamar yadda ka fada ne, matsalar daga wayarka ce. Idan ka hau shafin da wayar salula, za ka ga jerin sakonnin da na sabunta a farko, daya-bayan-daya. Wannan na biye da wancan. Daga kasa kuma za ka ga sauran fannonin da na jera. Idan ka matsa taken Makala, za ta budo dauke da takaitattun bayanai. A kasan bayanin kuma za ka ga wani maballi (Button) launin ja, an rubuta: “Continue Reading.” Idan ka latsa, nan take sauran bayanan za su bayyana, su cike shafin gaba daya, ba wai a hannun dama ba kamar yadda kake gani a wayarka. Hakan zai ba ka damar karanta dukkan makalar daga farko har karshe. A kasan makalar ma za ka ci karo da hotunan wasu makaloli masu alaka da wacce ka gama karantawa. Sannan akwai mashigi da zai riskar da kai zuwa ga makalar da ke gaba ko bayan wacce ka gama karantawa. Duk wannan na samar da su ne don sawwake wa mai karatu tsarin mu’amala da shafin ne.
Don haka, idan kana ganin sabanin yadda na yi bayani a sama, to, yana da kyau ka bibiyi wayarka. In kana da wata wayar da kake iya hawa Intanet da ita, ka gwada hawa shafin da ita, don gane bambancin da ke tsakaninsu. Hakan zai taimaka maka wajen gano daga ina ne matsalar take. Da fata ka gamsu. Allah Ya sa a dace, amin.
Assalamu Alaikum Baban Sadik, ina da tambaya: Don Allah a yi mini bayanin abin da Allah Ya sanar da kai game da gaskiyar wai Amurkawa ko kuma sauran jama’ar yankin irin su Kanada in za su tafi kasar Japan wai ta yamma za su yi tafiyar – maimakon gabas. Wai saboda duniyar kamar kwallo take, inji masu ikirarin haka. Na gode. Malam Dalhatu Aminiya.
Wa alaikumus salam, Malam Dalhatu barka ka dai. Da farko dai, bayani kan siffar duniya mun gama da shi tun a jerin makalolin da muka gabatar shekara 8 da suka gabata masu take: “Kimiyyar Kur’ani da na Zamani: A Ina Aka Hadu?” Kuma mun bayyana hakikanin gaskiyar wannan lamari na cewa, ita duniya a shimfide take kamar tabarma ko a cure take kamar kwallo.
Tambaya ta biyu kan cewa Amurkawa da mutanen kasar Kanada kan bi yammacin duniya ne don hadewa da kasar Japan, don kusancinsu da ita idan aka gewayo ta yammaci, hakan gaskiya ne ta wani bangare, kuma ba gaskiya ba ne idan aka bi ta wani bangare. Da farko dai ban da masaniya kan cewa lallai Amurka kan koma ta yamma don karasawa kasar Japan; haka ma ’yan kasar Kanada. Na biyu, don saukin fahimtar wannan bayanai, yana da kyau mu fahimci cewa kasar Amurka, ta la’akari da mu da ke Najeriya, tana yammacin duniya ne. Ita ce kasa ta karshe da ke yammacin duniyarmu ta yau. Domin jiharta mai suna Alaska, ita ce jiha ta karshe da ke yammacin duniya; daga ita sai ruwa kawai. Haka ma kasar Kanada take, bigire daya suke da kasar Amurka, bayanta babu komai sai ruwa. Ita kuma kasar Japan tana gabashin duniya ne, can kuryar gabas. Ita ma daga ita sai ruwa kawai. Kuma tunda duniyar a mulmule take kamar kwallo, wannan ya sa idan ka dubi alakar da ke tsakanin kuryar gabas da kuryar yamma sai ka ga ashe za su iya hadewa daga baya. Kamar dai karin maganar Bahaushe ne da ke cewa: “Inna ta zaga Baba ya zaga…”
Ta la’akari da bayanin da ya gabata kan bigiren kasar Amurka da Kanada a bangare daya, da bigiren kasar Japan da wani bangaren kasar Rasha ma, a daya bangaren, sai ka ga cewa abu ne mai sauki kuma mai yiwuwa ka iya isa kasar Japan idan ka zagayo daga kasar Amurka ko Kanada. Haka ma idan kana son isa kasar Amurka da Kanada daga kasar Japan; zai fi sauki da saurin zuwa idan ka zagaya ta baya. Ya zama yanke ke nan, wato “Short Cut.”
To amma kuma, kamar yadda na fada a farko, ba ni da tabbacin faruwar haka a aikace. Saboda na farko dai galibin tafiye-tafiye tsakanin wadannan kasashe kan faru ne ta hanyar jirgin sama. Ko ta hanyar jirgin ruwa, wanda kuma ke daukowa daga kasar Amurka ne ta tekun Atlantika, a kutso ta bangaren Afirka da Asiya, sannan a dire a kasar Japan. Haka wadansu kan bi jiragen ruwa zuwa kasashen Turai daga nan su bi jiragen kasa don watayawa tsakanin kasashe da bude ido ko don kasuwanci. Amma zagayawa daga bayan kasar Amurka da Kanada zuwa kasar Jafan, ta baya, abu ne da ban da masaniya a kai. Ko dai saboda ba a yi a aikace, ko kuma hakan bai shahara ba. Domin bigiren da ke tsakanin wadannan kasashe teku ne mai zurfi, kuma nan ne bangaren da ya fi kowane bangare sanyi daga cikin tekunan duniya. Domin galibinsa kankara ne. Wannan na iya zama dalilin da zai sa a kasa kutsawa ciki don yin tafiya makamancin wannan.
Wannan shi ne takaitaccen bayanin da zan iya yi kan wannan al’amari. Da fatan ka gamsu. Na gode.