Tambayoyi da sakonnin masu karatu ta tes (2)

Salaamun alaikum Baban Sadik.  Ka taimaka mini da rubutun da ka yi kan tsibirin Bamuda, da wacce ka yi a kan wayoyin Blackberry.  Ga Imel di na nan: [email protected] Wa alaikumus salam Maman Abdulsamad, da fatan ana lafiya.  Kamar yadda na sanar da sauran jama’a a baya, a halin yanzu akwai TASKA ta musamman da […]

Tambayoyi da sakonnin masu karatu ta tes (2)

Salaamun alaikum Baban Sadik.  Ka taimaka mini da rubutun da ka yi kan tsibirin Bamuda, da wacce ka yi a kan wayoyin Blackberry.  Ga Imel di na nan: [email protected]

Wa alaikumus salam Maman Abdulsamad, da fatan ana lafiya.  Kamar yadda na sanar da sauran jama’a a baya, a halin yanzu akwai TASKA ta musamman da na bude a Intanet, inda na taskance dukkan kasidun da suka taba bayyana a wannan shafi mai albarka.  Sun kai kusan 500 a halin yanzu.  Tun da “Blackberry” kike nema, sai ki bi wannan rariyar: www.babansadik.com/category/wayar-salula.  Dangane da kasidar Tsibirin Bamuda kuma, kina iya samunta a wannan rariya, wanda shi ne bangaren da ke dauke da dukkan kasidun da suke dauke da Kiimiyyar teku: www.babansadik.com/category/teku.  

Allah sa albarka cikin abin da za a karanta, Ya kuma sa ya zama mai fa’ida ga ruyuwa, duniya da lahira, amin.

 

Assalamu alaikum, barkanka da kokari.  Tambayata ita ce: shin, sauran duniyoyi guda takwas da ake da su bayan wannan duniyar tamu, akwai halittun da ke rayuwa a cikinsu ne?  Sannan don Allah ina son ka yi mana cikakken bayani kan “Bamuda Triangle.”  – Aminu Isa Bakori: 07068147933

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Aminu.  Ya zuwa yanzu babu wani tabbataccen ruwaya na malaman kimiyya da ke nuna samuwar wasu halittu da ke wadannan sauran duniyoyi, baicin tamu da muke zaune ciki.  Bincike na kusa da wannan da aka yi shi ne, gano cewa akwai yiwuwar damar halittu su iya rayuwa a wasu daga cikin wadannan duniyoyi, sanadiyyar alamun samuwar ruwa da aka gano.  Amma wannan ba garanti ba ne.  Domin samuwar ruwa a wuri kadai, bai nuna dole halittu su iya rayuwa a wannan wuri ko mahalli.  

Bayan ruwa, halittu na bukatar kasar da ta dace da rayuwarsu, da tabbacin samuwar ruwan sama, da koguna, da iska madaidaiciya wacce dan Adam zai iya shakarta ta taimaka masa wajen tafiyar rayuwa, da kuma ka’idar kimiyya da ke nuna daidaituwar jiki a mahallin.  Wadannan, idan ka cire wannan duniayr da muke cikinta, babu wata duniya ko wani mahalli da ke da su.

Da wannan ma wasu malamai ke cewa, ba a banza ba dan Adam ya samu kansa a wannan duniyar tamu.  Domin an yi bincike an gano cewa, dukkan dabi’un da wannan duniya ta siffatu da su, da irin abubuwan da Allah Ya tanada ko ya zuba a cikinta, irin su yanayin iska, da samuwar koramu da gulabe da tekuna da kuma ruwan sana da mizanin zafin rana, da kuma iya tazarar ma da Allah Ya ajiye wannan duniya daga inda rana take, duk sun bambanta wannan mahalli da sauran mahallai da ake da su.

A tare da haka, Allah Ya ga dama kuma Ya samar da wannan dama a wasu wurare kuma Ya bayar da damar gano su.  Domin shi ne mahaliccin komai da kowa, kuma ma a cikin Al-Kur’ani Ya nuna cewa Zai ci gaba da halittar abin da ma bai sansu ba.  Amma a halin yanzu kam, babu.  

Dangane da bukatarka na kasidar Bamuda kuma, a gaskiya tuni na gama bayani gamsasshe a kan wannan mahalli.  Kana iya karanta kasidun a taskar da nake zuba kasidu a Intanet da ke wannan adireshi: www.babansadik.com/category/teku. 

Da fatan ka gamsu.

 

Assalamu alaikum Baban Sadik, barka da fatan kana lafiya.  Don Allah ina son karin bayani kan yadda ake kirkirar “Blog”.  Na gode.  – M. B. Sambo: [email protected]

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Sambo.  Ana kirkirar “Blog” ne (ko ka ce: ‘Taska’ ko ‘Mudawwana’) ta hanyar zaban manhajar da kake bukata, daga nan sai ka yi rajista a shafin manhajar, sai kuma ka fara zuba bayanai kana zawarcin jama’a don su zo su karanta.  

Manhajojin “blog” suna da yawa.  Shahararru daga cikinsu su ne: “Blogger” (www.blogger.com) na kamfanin Google. Sai “Wordpress” (www.wordpres.com) na kamfanin WordPress.  Akwai LibeJournal da dai sauransu.  Idan ka je shafin daya daga cikinsu, sai ka yi rajista, daga nan kuma sai ka hau don fara zuba bayanai.  Tsarinsu da kintsinsu ya sha bamban, haka ma yadda ake gudanar da al’amura a kai.  Kana iya ziyartar shafin kowanne daga cikinsu, ka ga wanda ya yi maka.  Allah sa a dace, amin.

 

Za mu ci gaba