Tambayoyi da sakonnin masu karatu ta tes da Imel (2)

Assalamu Alaikum Abban Sadik. A matsayina na dalibinka na yau da kullum tambayata a nan ita ce: ta yaya tauraron dan Adam (satellite) yake zama a cikin tsararin samaniya?  Sannan kuma a wace duniya ce aka fi jefa shi?  Daga dalibinka: Saminu Artillery Yelwa Shendam, Jihar Filato: 08032436477 [email protected]  Wa alaikumus salam Malam Saminu, da […]

Tambayoyi da sakonnin masu karatu ta tes da Imel (2)

Assalamu Alaikum Abban Sadik. A matsayina na dalibinka na yau da kullum tambayata a nan ita ce: ta yaya tauraron dan Adam (satellite) yake zama a cikin tsararin samaniya?  Sannan kuma a wace duniya ce aka fi jefa shi?  Daga dalibinka: Saminu Artillery Yelwa Shendam, Jihar Filato: 08032436477 [email protected] 

Wa alaikumus salam Malam Saminu, da fatan kana cikin koshin lafiya.  Wannan tambaya ce mai matukar muhimmanci, kuma tana cikin tambayoyin da suke yawan maimaituwa a wannan shafi mai albarka.  Don haka na kebance wannan lokaci don fadada bayani iya gwargwado.

Da farko dai, Tauraron dan Adam shi ne duk wata na’ura mai cin gashin kanta da ake harbawa zuwa sararin samaniya don mikawa da karbo bayanan yanayi ko dauko hotunan wasu wurare da dan Adam ba ya iya kai wa garesu ta dadi, ko kuma sinsino irin yanayin da mahalli zai kasance a wasu lokuta na daban, ko kuma don yada bayanan sadarwa daga wani bigire na duniya zuwa wani bigire.  Ire-iren wadannan taurari suna shawagi ne a cikin falakin wannan duniya tamu, ko duniyar Wata da taurarin da Allah Ya halitta, ko kuma cikin falakin wasu duniyoyi makamantan na mu.  A halin wannan shawagi ne suke gudanar da aiyukansu na nemo bayanai, ko karbowa daga wani bangaren wannan duniya don yada bayanan zuwa wasu bangarorin daban, ko kuma nemo bayanan da ke da nasaba da falakin da suke shawagi a ciki, don aiko sakon da suka taskance zuwa garemu a wannan duniya, ko kuma, a wasu lokutan, su dauko mana hotunan abin da ke faruwa ga manya-manyan tekunan da ke zagaye da mu a duniya baki daya.

An fara harba ire-iren wadannan taurarin wucin-gadi ne zuwa cikin falaki shekaru kusan hamsin da tara da suka gabata (1957), kuma ya zuwa yanzu, an harba wajen dubunnai masu zuwa don karbowa da aikawa da bayanai ko sinsino yanayi ko kuma dauko hotunan sararin samaniya, don amfanin dan Adam.  A karon farko ana amfani ne da roket ne mai dauke da kumbo (space shuttle), don cilla wani tauraro zuwa sararin samaniya.  Daga baya aka zo ana amfani da jiragen sama masu masifar gudu, duk da yake shi ma wannan tsari na bukatar roket wanda ke harba jirgin zuwa wani mizanin nisa cikin samaniya, kafin wannan jirgi ya ingiza tauraron cikin falaki.

Ana cikin haka sai kuma masana kimiyyar sararin samaniyar Amurka suka bullo da wata hanya wacce ta sha bamban da sauran wajen sauki da inganci.  Wannan hanya kuwa ita ta cilla tauraron dan Adam daga babbar kumbon tashar binciken sararin samaniya da ke can sararin samaniya, wato US Space Shuttle.  Hakan na faruwa ne domin masana na iya kera tauraron dan Adam a halin zamansu cikin wannan kumbo da ke tashar, har su harba shi.  Haka idan ya lalace ko ya gama aikinsa, suna iya sanya shi cikin wani kumbo karami don aikowa da shi wannan duniya tamu don a gyara shi yadda ya kamata. Nan gaba, masana harkar falaki a Amurka na tunanin bullo da wani tsari mai suna Single Stage to Orbit, wato “tsalle daya zuwa falaki”, a misali.  Wannan tsari zai rage yawan tashoshin da tauraron dan Adam zai bi kafin kai wa ga falakin da aka tunkuda shi don gudanar da aikinsa.  Idan har suka dace, wannan tsari zai zo ne da kumbon sararin samaniya guda daya, tafkeke, mai iya daukan taurarin dan Adam da dama, don aikawa da su zuwa cikin falakin da ya dace da su, cikin harbawa guda!

Tauraron dan Adam na farko da ya fara shiga cikin falakin wannan duniya tamu shi ne Sputnik 1, wanda kasar Rasha ta harba a ranar 4 ga watan Oktoba, shekarar 1957. Wannan tauraro ya yi shawagi cikin falaki yana aiko sakonni har tsawon kwana 21. Bayan ya kamo hanyarsa ta dawowa duniya, sai ya kone a hanya.  Hakan ya faru ne ranar 4 ga watan Janairun shekarar 1958. Daga nan kasar ta sake cilla wani tauraron mai suna Sputnik 2, a ranar 3 ga watan Nuwamba na shekarar 1957 dai har wa yau.  A ciki suka sanya wata kariya don gwaji, wacce a karshe ta mace, sa’o’i biyu da harba ta, sanadiyyar tsananin zafin da ke cikin tauraron da aka sanya ta ciki.  Tauraron Sputnik 2 ya dawo wannan duniya tamu ranar 14 ga watan Afrailun shekarar 1958, inda ya kone bayan ya shigo shi ma.

Da ganin haka sai kasar Amurka ta fara narkewa da kishi.  Nan take sai kawai aka ji ita ma ta harba tauraronta na farko zuwa cikin falakin wannan duniya tamu, mai suna Edplorer 1, ranar 31 ga watan Janairun shekarar 1958.  Bayan nan ta sake cilla wani tauraro mai suna Discoberer 13, tauraron dan Adam na farko da ya fara zuwa falaki, ya taskance bayanan da yake bukata ta hanyar wata na’ura, sannan ya cillo wannan na’ura zuwa wannan duniya tamu, masu binciken kasar Amurka suka dauka don tantance sakonnin da ya kalato musu.  Wannan aiki ta gudanar da shi ne cikin shekarar 1960, ranar 10 ga watan Agusta.  Daga nan sauran kasashe suka biyo baya.

Akwai nau’ukan tauraron dan Adam da dama a cikin falaki, masu shawagi don gudanar da ayyukan da aka aike su gudanarwa.  Shahararru daga cikinsu sun hada da taurarin dan adam kan sadarwa, da taurarin dan adam kan binciken kimiyya na jami’o’in kasashen yamma, da taurarin dan Adam kan harkan tsaro wanda hukumomin sojin kasashen Amurka da sauran kawayenta suka harba da dai sauran makamantansu.

Bayan tauraron dan Adam ya samu kansa a cikin falaki, ba abin da zai ta yi sai shawagi don gudanar da aikinsa, sai in matsala ya samu.  Tsarin tafiyar da tauraron dan Adam a cikin falaki abu ne mai matukar ban mamaki. Ana tanada musu makamashin lantarki ne ta amfani da tsarin taskance makamashin hasken rana (Solar Energy), don bashi damar gudanar da abin da aka tura shi gudanarwa a mahallin da yake.

A yayin da tauraron dan Adam ya samu kansa cikin falaki, dole yana da jiha ta musamman, ko yanayi na musamman da yake kasancewa cikinsa.  Wannan yanayi shi ake kira Satellite Orientation. Da zarar ya fara shawagi, yakan bude fuka-fukansa ne suna fuskantar rana (don taskance masa makamashin da yake bukata), sannan ya juya na’urorin daukan bayanansa (Antennas and sensors) zuwa jihar wannan duniya tamu, ko kuma dukan abin da aka harba shi don yin nazarinsa.  Idan tauraron sadarwa ne (communication satellite), sai ya fuskantar da na’urar daukan bayanansa zuwa wannan duniya; idan na lura da yanayi ne, zai fuskantar da kemararsa ne shi ma zuwa wannan duniya tamu; amma idan tauraron binciken sararin samaniya ne, zai fuskantar da na’urar hangen nesansa ne zuwa halitta ko duniyar da aka aike shi yin nazarinta.  Har wa yau, kowane tauraron dan Adam na dauke ne da inji na musamman, wanda ke taimaka masa tabbatuwa a jiha ko yanayin da zai taimaka masa yin aikinsa.

A cikin falaki, tauraron dan Adam ba shi da inuwar da zai iya fakewa don shan inuwa. Bayan nan, shi kanshi yana dauke ne da wasu injina na roket, masu haddasa masa tsananin zafi sanadiyyar aikin da suke yi ba kakkautawa.  Abin da ke taimaka masa kawai shi ne, an yi masa wani inji da ke sanya shi mazayawa lokaci-lokaci, don baza zafi da tururin da ke damfare da shi, ta hanyar jujjuyawa.  Wanda inda a wuri guda yake tabbace a kullum, zafin na iya haddasa masa illa mai tsanani.  Sannan idan yamma ta yi, wata ya hasko, akwai tsananin sanyi da zai sake darkake shi, tare da rage masa inganci.  Bayan haka, a can sararin samaniya, ba irin nan duniya ba, akwai iska mai tsananin karfi da ke bugawa babu kakkautawa.  Idan da rana ne, wannan iska kan rikide tare da zafin rana; haka idan da dare ne, sai ta rikide tare da sanyin dare. A daya bangaren kuma, akwai taurarin da kwanakinsu ya kare, suka farfashe, balgacen su kan warwatsu cikin falaki; wasu su fado cikin duniyarmu, kamar yadda bayanai suka gabata a baya, wasu kuma su ta shawagi a cikin falaki.  A yayin shawaginsa, tauraron dan Adam kan ci karo da su, har su kwakkwafe shi, ko su babballe masa fuka-fukansa, ko kuma su haddasa masa wata illa babba da ka iya hana shi ci gaba da aiyukansa.

Dangane da yanayin rayuwa da yin zamani a cikin falaki, tauraron dan Adam ya kasu kashi uku; akwai wadanda ke yin shawaginsu har su gama ba tare da samun wata matsala ba.  Idan suka gama rayuwa da shekaru ko muddar da aka yanke musu, sai su nemi hanyar shigowa duniya da kansu.  Da zarar sun kutso sararin samaniya (earth’s atmosphere), sai su kone gaba daya.  Idan kuma rayuwarsu ba ta kare ba, amma akwai na’urorin da ake son cirewa daga garesu don sarrafa bayanan da suka taskance, sai ayi amfani da kwarewa ta kimiyya, a harbe injin da ke sarrafa tauraron, nan take sai ya rage gudunsa, ya fara saukowa cikin duniya da kansa, har a riske shi.  Sai kashi na uku, wadanda injinsu ko wasu sassansu masu muhimmanci ke lalacewa, su daina aiki, kawai sai su “haukace”, su yi ta shawagi ba-kai-ba-gindi, cikin falaki.  Wadannan su ake kira “Space Junk”, wato sun zama sharan cikin falaki ke nan.  Haka za su yi ta kai-komo har su kone.

Sannan, iya girma da rashin nauyin tauraro, iya saukin da zai samu wajen shigowa duniya; iya gajarta da nauyinsa, iya wahalar da zai sha wajen shigowa, saboda tasiri da karfin iska da ke janyo jiki zuwa kasa. Iya nisan tauraro da duniya, iya yawan shekaru ko lokacin da zai iya dauka yana shawagi.  Taurarin da ke shawagi a falakin da bai wuce nisan kilomita dari biyu ba, basu wuce mako guda zuwa watan uku suna shawagi a ciki.  Wadanda ke iya nisan kilomita dari uku kuma, suna iya yin shekara biyu ko fiye da haka.  Idan tauraro ya kai nisan kilomita dubu daya kuma, yana iya shawagi a cikin falaki na tsawon shekara dubu ko fiye da haka.  To ko ma dai a ina yake, da zarar kwanakinsa sun kare, dole ya nufo gida. Idan ya iso lafiya alhamdulillahi.  Idan kuma kwanaki sun kare, sai ya kone a yayin shigowarsa, ko wasu sassansa su daina aiki sanadiyyar dimbin kalubalen da ke samunsa a can, har ya zama shara, wacce iskar falaki ke dibansa na iya wani zamani, kafin ya kwanta dama.

Wannan shi ne dan abin da ya samu, kan abin da ya shafi bincike kan tauraron dan Adam da tsarin tafiyar da aiyukansa.  Abubuwa ne masu ban mamaki, kamar yadda mai karatu ya ji kuma ya karanta.  Amma abin da ya fi komai mamaki shi ne, wanda ya halicci mai wannan tunani, wato Allah.  Idan wannan bayani ya bamu mamaki, to mu san cewa ikon Allah shi ya fi komai zama abin al’ajabi.  Don shi ne wanda ya halicci dan Adam din da ya yi tunanin kirkiran dukan wadannan abubuwa da bayanansu ya gabata, da kuma halittun da ake gudanar da binciken kansu.  Idan muka dubi hatta wadannan taurarin dan Adam din, sai mu ga ai kwaikwayon halittar Ubangiji aka yi, don samun ci gaba.

Allah Yai mana afuwa, Ya kuma sa mu dace, amin.