Tambayoyi da sakonnin masu karatu ta tes da Imel (3)

Assalamu alaikun Baban Sadik, na ji dadin tambayoyin da aka yi kan Tsibirin Bamuda da kuma tekuna. Kamar don ni aka yi su. Ina godiya da amsoshin da aka bayar da kuma saukaka mana da aka yi. Fatan Allah Ya kara yassare min waya mai hawa yanar gizo. Allah Ya saka da alheri ya kuma […]

Tambayoyi da sakonnin masu karatu ta tes da Imel (3)

Assalamu alaikun Baban Sadik, na ji dadin tambayoyin da aka yi kan Tsibirin Bamuda da kuma tekuna. Kamar don ni aka yi su. Ina godiya da amsoshin da aka bayar da kuma saukaka mana da aka yi. Fatan Allah Ya kara yassare min waya mai hawa yanar gizo. Allah Ya saka da alheri ya kuma kara basira, amen. Daga Sammani Shu’aibu. 

Wa alaikumus salam, Malam Sammani. Ina godiya matuka, tare da farin cikin jin ka samu gamsuwa cikin dan abin da na gabatar na bayanai. Da fatan za a ci gaba da kasancewa tare da jaridar AMINIYA, wacce a koyaushe take dauke da amintattun bayanai don fadakar da masu karatu. A duk sadda aka ga kuskure kuma cikin abin da nake gabatarwa, sai a nusar dani. Ina kara godiya matuka. Allah bar zumunci. Na gode.

Salam Baban Sadik ni dai mai bibiyan filinka ne na AMINIYA, kuma ina gaisheka bisa himma da kokarinka a wannan fage da ya shafi kimiyya. Wallahi kana matukar burgeni da bani sha’awa. Don Allah ka isar da gaisuwata ga Sadik danka. Na gode. Daga Basiru dan Bazazzagi. 

Wa alaikumus salam, Malam Basiru ina godiya matuka da fatan alheri da kake mana baki daya. Sannan na yi farin cikin jin cewa kana samun gamsuwa da irin bayanan da kake karantawa masu dauke da binciken da nake gabatarwa iya gwargwadon hali da sani. Sadik zai ji gaisuwarka in sha Allah. Ina kuma rokon Allah da Ya albarkaci rayuwarka, tare da ci gaba da kasancewa tare da mu a jaridar AMINIYA. Na gode. Na gode. Na gode.

Assalamu Alaikum Baban Sadik, muna son don Allah ka yi mana bayani akan tsawa dake faruwa a lokacin da ake ruwa. Mene ne ke fadowa, kuma me ke haddasa ta a kimiyyance? Daga Aminu M. Mai Aduma. 

Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Aminu. Da fatan an wuni lafiya. Dangane da iya binciken malaman kimiyya, sun nuna kafin samuwar tsawa, akwai haske da ke bayyana, wato walkiya kenan kamar yadda muke cewa, daga nan sai samuwar rugugi mai karfi mai girgiza da muke kira cida a harshen Hausa. Bayan cida ne kuma sai sautin tsawa ya biyo baya a karshe. Haka abin ke biye, kamar yadda mu ke ji ko gani. Amma a hakika, lokaci guda duk suke samuwa.  Meye dalilin samuwar tsawa? Yaya walkiya da rugugin cida ke rigayar sautin tsawa?

Wannan tambaya da ka mini, irinta aka yi wa Farfesa Richard Brill da ke Kwalejin Honolulu (Honolulu Community College) a kasar Amurka, cikin shekarar 2000, wanda kuma Mujallar “The Scientific American” ta buga a shafinta a watan Disamba na shekarar 2002. Ga nassin amsar da ya bayar nan kai tsaye na fassaro maka: 

“Abin da ke haddasa samuwar tsawa shi ne walkiya, wanda asali yake dauke da  cunkoson sinadaran “Electron” da ke makare a cikinsa ko a tsakanin giragizai, ko kuma tsakanin giragizai da mahallin da muke rayuwa a ciki a wannan duniya tamu. Nau’in iskar da ke gewaye da wadannan sinadaran “Electron” kan yi zafi (sanadiyyar zafin rana), zafi mai tsananin da ya kai kimanin digiri 50,000 a ma’aunin zafi na farahait (50,000F), daidai da zafin rana ninki uku kenan. Da zarar wannan iska mai dan karen zafi ya fara hucewa, sai ya samar da wata jakar iska a gewaye da titin da iskar ke bi. Nan take sai iskar da ke makwabtaka da wannan jakar iska ta rika fadada tana tsukewa, tana fadada tana tsukewa (edpansion and contraption), lokaci-lokaci.  Wannan ke sa jakar iskar da ke gefe ta rika girgiza cikin batsewa, hakan kuma yana haifar da sautin tsagewa. Da zarar wannan girgiza ta fara lafawa, sai ta haifar da wani sauti mai tsakanin kara da muke kira Tsawa.

Muna iya jin masifaffen sautin tsawa da bugawarsa daga tazarar mil goma (kilomita 13) ko sama da haka daga hasken da ke haddasa tsawar. Sannan idan walkiya ta auku a iya tazarar da ake iya ganinta, ita muke fara gani (ba sautin rugugin cida ko tsawar ba), domin gudun sauti a cikin haske bai kai gudun sinadaran “Electron” da gudanuwarsa ba. Shi yasa ma sautin tsawar ke aukuwa kamar sautin hatsarin wutar lantarki (Shockwabe), ba kamar sauti irin wanda aka sani na al’ada ba. Shi wannan sauti mai kama da sautin hatsarin wutar lantarki yana bibiyar titin wannan sinadarin “Electron” ne (a yayin da yake aukuwa) kamar yadda dunkulen yatsu ke tasiri a jiki yayin da aka naushi mutum.

Bayan haka, gudun sauti ba komai ba ne idan aka kwatanta shi da gudun haske. Hasken da ke samuwa a yayin walkiya na riskarmu ne (a wannan duniya) cikin kasa da dakika (second) guda, a yayin da sautin ke biye da shi cikin saibi da nawa, kai ka ce dodon kodi ne ke biye da jirgi nau’in roket dake shawagi a tsakanin duniyoyi. Don haka, yanayin sauti da haske da ke samuwa a lokacin walkiya da tsawa hadaka ne na abin da ke samuwa sanadiyyar girgizan da sinadaran iska ke yi wajen hargitsa karfin sinadaran lantarki. Wannan wani al’amari ne mai matukar ban mamaki hakika, kuma wannan ke dada tunatar damu duka cewa mu ba komai ba ne idan aka gwama halittarmu da na sararin samaniya.”

Wanda ya yi wannan fatawa dai Malamin Jami’a ne, ba musulmi ba ne kuma. Amma ka ga yadda ya kare fatawarsa da jawo hankali zuwa ga girma da karfin kudurar Ubangiji a kaikaice. Da fatan ka gamsu da dan abin da ya samu na bayani.

Assalamu alaikum Baban Sadik barka da warhaka, kuma barka da dawainiya da jama’a. Ina maka fatan alheri da Allah Ya kara fahimta, ameen. Baban Sadik, a shafina na Facebook idan na yi log in sai na dinga ganin “comment” wanda ni ba ni na rubuta da kaina ba. Ko kuma na dinga ganin “Your rekuest is accepted”, ba tare da ni na yi rekuest ba. Don Allah ina neman mafita. Allah Ya kara fahimta.  Daga Sunusi Muhammad: [email protected]

Wa alaikumus salam Malam Sanusi. Da fatan kana lafiya. Daga bayaninka kamar kana nufin ba kai ba ne ka yi wadannan “ta’aliki” (Comments); kawai ka ga abin ne. A iya sani na dai, ba zan iya tuna wani al’amari da zai iya haddasa hakan ba sai dalilai uku, ko dayan uku. Na farko shi ne, watakila kai ne ka yi, amma ka mance. Na biyu, ko dai ta’alikin da kake ganin wasu ne suka yi a kasan sakon (Post) da ka rubuta a baya. In har babu dayan biyun nan, to, ta yiwu, Allah sawake, watakila wani ne ya kutsa cikin shafin naka yake wakiltarka ba tare da izininka ba. Amma in ba haka ba, ba abin da zai iya sa hakan ya faru. Don haka, kana iya bincika shafin naka ka gani, don tabbatar da hakikanin abin da ya faru ko yake faruwa da shafin naka.

Ka kuma nuna cewa wasu lokuta kana ganin sakonni dake cewa: “Your Rekuest is accepted.”  Wannan sako na bayyana ne bayan wani ya karbi bukatarka ta yin abota da shi, wanda ka aika masa a baya.  Muddin ka ga wannan sako, to lallai a baya ka taba aikawa da sakon neman abota (Friend Rekuest) ga wani, kuma amincewarsa ce ta haddasa samuwar wannan sako da ka ci karo da ita. Don haka, sai ka duba ka gani, shin wanda ya karbi bukatarka ta abotan nan, ka san shi? Ko za ka iya tuna sadda ka aika masa bukatar neman abota? In har baka san shi ba, kuma ba za ka taba iya tuna sadda ka aika masa da wannan sako na neman abota ba, to lallai akwai abin da ke faruwa.  Sai ka duba tsare-tsaren shafin naka sosai ka gani, Tabbas, ba za a rasa dayan biyu ba: ko dai kai ne ka aika, amma ka mance, watakila saboda tsawon lokacin da aka dauka bai amince maka ba, ko kuma wani yana hawa shafin naka yana wakiltarka ba tare da izininka ba.  Wannan dalili na biyu shi ake kira: “Identify Theft.”

Wannan shi ne dan abin da zan baka na shawara. Ina maka fatan alheri da rokon Allah Yasa ka samu hanyar warware wannan matsala cikin sauki. 

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos