Tambayoyi da sakonnin masu karatu ta tes da Imel (4)
Assalamu Alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya. Tambayata a nan ita ce: me wadannan kalmomi suke nufi a fannin kwamfuta? “Archibe”, da “Encrypt”, “Synchronize”, da “Configure”, da “Compress”, da kuma “Debug”. Ka huta lafiya. Daga: Idirs Hamza Wa alaikumus salam Malam Idris Hamza, barka ka dai. Wadannan kalmomi dai da kake son sanin […]
Assalamu Alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya. Tambayata a nan ita ce: me wadannan kalmomi suke nufi a fannin kwamfuta? “Archibe”, da “Encrypt”, “Synchronize”, da “Configure”, da “Compress”, da kuma “Debug”. Ka huta lafiya. Daga: Idirs Hamza
Wa alaikumus salam Malam Idris Hamza, barka ka dai. Wadannan kalmomi dai da kake son sanin ma’anoninsu a takaice, kalmomi ne da suka shafi fanni da harkar sadarwar wayar salula da kwamfuta da kuma tsarin sadarwa na zamani. Ga ma’anoninsu nan a takaice.
“Archibe”
Kalmar “Archibe” kalma ce dake nufin “matattara” ko “taska” ko wata ma’adanar bayanai, amma ta manhajar sadarwa, ba ma’adana irin wacce ake jona wa kwamfuta don zuba bayanai a ciki ba. Sannan kalmar na iya daukar ma’anar aiki, ko “fi’ili.”
“Encrypt”
Kalmar “Encrypt” an samo ta ne daga kalma mai suna: “Encryption”, wanda ke nufin tsarin “boyewa ko layance bayanai, don tabbatar da ingancinsu da kamalarsu.” Wannan tana da kishiyarta mai suna: “Decrypt” wacce aka samo asalinta daga kalmar “Decryption.” Ita kuma tana ishara ne ga tsarin “warware bayanan da aka layance su, don mayar da su zuwa asalinsu.” Wannan tsari ilimi ne mai zaman kansa a fannin sadarwar zamani. Shi ne bangaren dake lura da tsarin tsaro da kariyar bayanai, wato: “Information Security.” Idan ka je shafin kamfanin Imel dinka (Yahoo!, ko Gmail, ko Hotmail), bayan ka shigar da sunanka (username), kana fara rubuta kalmar sirrinka (password), nan take za ka ga dunkulallun bakake ne ke bayyana, ba hakinanin kalmomi ko haruffa ko lambobin da kake rubutawa ba. Wannan fanni na “Encryption” shi ne ke tabbatar da yiwuwar haka a aikace. Ilimi ne mai fadin gaske, kuma wanda ya samar da asalinsa shi ne: Sheikh Muhammad bin Musa Alkhawaarizmi, daya daga cikin shaharrun malaman musulunci.
“Synchronize”
Kalmar “Synchrinize” kuma na nufin tsarin musayar bayanai ne tsakanin ma’adanan bayanai biyu, kai tsaye. Ka lura, na ce kai tsaye domin tabbatar da hakan na faruwa ne a lokaci guda. Misali, idan ka taskance lambobin wayarka nau’in Android gaba a kan manhajar taskance lambobin waya na Google mai suna: “Google Contact,” a duk sadda ka sake shigar da wata sabuwar lamba kan wayarka, muddin wayar a jone take da Intanet, nan take wannan manhaja ta “Google Contact” za ta aiwatar da musayar bayanai tsakaninta da wayarka, ta hanyar duba canjin da aka samu tsakanin yawan lambobin da ke kanta da wadanda ke kan wayarka. Da zarar ta lura akwai sauyi, sai ta duba, shin sauyin ta bangaren wayarka ne ko ta bangarenta? Ma’ana, karuwa lambobin suka yi ko raguwa? Idan karuwa suka yi, sai ta loda wadanda ba ta da su daga wayarka. Idan kuma raguwa suka yi, sai ta sauko da wadanda aka cire daga kanta zuwa kan wayarka. Wannan na faruwa ne ba tare da saninka ba. Haka ma idan sakonnin Imel ne aka aiko maka, da zarar sakon ya diro cikin jakar Imel dinka dake kwamfanin Imel din, nan take manhajar Imel dake wayarka za ta lalubo sakonnin Imel dake kan wayarka ta gwama su da wadanda ke kan kwamfutar Imel na kamfanin. Idan ta ga akwai bambancin adadi, sai ta aiwatar da musayar bayanai tsakaninta da wadanda ke kan kwamfutar kamfanin Imel dinka. Wannan, a takaice, shi ne abin da ake kira: “Synchronize”.
“Configure”
Kalmar “Configure” asalinta daga kalmar “Configuration” ne, wadda ke nufin “tsara hanyoyin mu’amala da waya ko kwamfuta ko wata manhajar ko tsarin sadarwa.” Duk wata kwamfuta ko wayar salula ko manhajar sadarwa tana zuwa ne da wani tsari da kamfani ko maginin ya dora ta a kai. Wannan tsari shi ake kira: “Default Settings.” Tsarin canza wadannan tsare-tsare da waya ko kwamfutar ta zo da su, shi ake kira: “Configure”.
“Compress”
Wannan kalma an samo ta ne daga asalin kalmar: “Compression”, wanda ke nufin tsarin nadewa da takura bayanai, don adana mizanin bayanai mai girma a mahalli ko ma’adana takaitacciya. Wannan kalma ta sha bamban da kalmar “Decryption,” wacce ke nufin tsarin layance bayanai. Ita wannan kalma tana nufin takura bayanai ne masu yawa, don adana su a ma’adana takaitacciya ko mara girma. Mu kaddara kana da bayanai ma su girman mizani 10GB. Ana iya takura wannan bayani ya zaman mizani 5GB ko kasa da haka. Akwai manhajojin kwamfuta da wayar salula da yawa wadanda za a iya amfani da su don takura bayanai. Shahararru daga cikinsu su ne: “Windows Zip”, da “7-zip File Manager” da dai sauransu. Ana amfani da kalmar “zip” don nufin “compressing” bayanai zuwa mahalli takaitacce.
“Debug”
Kalmar “Debug” daga asalin kalmar “Bug” ne, wanda ke nufin wani kwaro, ko wata matsala dake cikin wani abu. A fannin fasahar sadarwar zamani, kalmar “Debugging” na ishara ne ga tsarin gano kurakuran dake cikin bayanan gina manhajar kwamfuta. Idan maginin manhajar kwamfuta ya gama rubuta umarnin da zai baiwa kwamfuta don aiwatar da su, a wasu lokuta akan samu matsala wajen kuskuren kalma ko harafi ko wani digo ko aya, wanda kwamfuta ke kasa fahimtarsa. Wannan zai sa da zarar an shigar mata, sai ta kasa aiwatar da umarnin da aka bata. Wadannan kurakurai dake cikin umarni, su ake kira: “Bugs.” Tsarin nemo su, da tantance su don cire su ko gyara su kuma, shi ake kira: “Debugging.” Kalmar ce shahararriya a wajen magina manhajar kwamfuta, wato: “Prgrammers.”Wadannan, a takaice, su ne ma’anonin kalmomin da ka bukata. Da fatan ka gamsu.
Assalamu Alaikum warh matullahi wabarakatuh, ranka ya dade. Gaskiya muna jin dadin yadda kake kara mana karfin gwiwa ta hanyar ilmantar damu. Don Allah ina bukatar a fahimtar da ni yadda zan saita manhajar Android Studio da kuma hanya mafi sauki da zan fara kirkirar Android App. Nagode. Ga gmail account dina nan:- [email protected]
Wa alaikumus salam, barka dai. Bayani kan wannan maudu’i abu ne mai fadi, takaita bayani ba zai gamsar da kai ba. Don haka, ga dan abin da ya sawwaka nan na kalato maka.
Dabaru da Kayan Aikin Gina Manhajar Android
Bayan littattafai da kwarewa da kuma manhajoji, mai karatu na bukatar abubuwa guda uku mahimmai kafin ya gwanance wajen tsarawa da gina ingantattun manhajojin Android. Idan ba mu mance darasin makon jiya ba, mun yi bayani ne kan matakan ilimi ko kwarewa da a halin yanzu ake bi wajen gina wadannan manhajoji. Tare da nuna cewa matakin karatu da kwatanta abin da aka karanta a aikace, su ne manyan tubali wajen gwanancewa a wannan sana’a. A wannan mako za mu karkare wannan doguwar kasida ce da bibiyar hanyoyi uku na karshe, don cinma burin mai buri a wannan fage.
Zamu ci gaba…