Tambayoyi da sakonnin masu karatu ta tes da Imel (5)

Da yawa cikin masu karatu sun sha turo mini tambayoyi cewa wadanne hanyoyi za su bi wajen koyon ilimin gina manhajar kwamfuta?  Wato “Computer Programming” ke nan. Ga wadanda na samu damar ba su amsa, nakan shawarce su da su tanadi lokaci ne, a karon farko. Domin sai ka baiwa karatu lokacinka, sannan zai baka […]

Tambayoyi da sakonnin masu karatu ta tes da Imel (5)

Da yawa cikin masu karatu sun sha turo mini tambayoyi cewa wadanne hanyoyi za su bi wajen koyon ilimin gina manhajar kwamfuta?  Wato “Computer Programming” ke nan. Ga wadanda na samu damar ba su amsa, nakan shawarce su da su tanadi lokaci ne, a karon farko. Domin sai ka baiwa karatu lokacinka, sannan zai baka kansa, ka kwashi abin da kake so. Amma idan dabi’arka ita ce kailula, ka je ka nemi wani fannin daban ba wannan ba. Wannan ita ce gaskiya mai daci da ta kamata mai karatu ya santa, ya fahimce ta, sannan ya hakikance samuwarta don cin nasara.

Kayan Aiki

Kayayyakin aikin da kake bukata sun kai biyar zuwa shida. Abu na farko dai shi ne, dole ka mallaki kwamfuta, nau’in tafi-da-gidanka (Laptop) ko ta kan tebur (Desktop), wacce za ka iya jona ta da Intanet lokaci zuwa lokaci. Sannan dole ne ya zama tana dauke da manhajar da za ta iya riskar da kai zuwa Intanet, wato Manhajar Lilo kenan (Internet Browser). Amfanin mallakar kwamfuta kuwa shi ne, duk abin da za ka gabatar a kanta zai gudana; daga farko har karshe.  Sannan dukkan manhajojin da za ka yi amfani da su wajen wannan aiki, daga Intanet za ka saukar da su. Wani abin sha’awa ma shi ne, dukkan wadannan manhajoji da tsare-tsare kyauta ne, ba za ka kashe ko kwandala ba.

Bayan mallakar kwamfuta da karikitanta, sai manhajoji guda hudu da za ka saukar, daga gidajen yanar sadarwa daban-daban. Kamar yadda na fada a baya ne, dukkan wadannan manhajoji kyauta ake bayar da su.

Manhajar farko ita ce manhajar JAVA. Za ka samu wannan manhaja mai dauke da tubalin gina manhajar kwamfuta da yaren Jaba ne a http://jaba.oracle.com/downloads. Duk da cewa zubin Jaba a halin yanzu yana kan na takwas ne (Version 8 – Jaba 1.8), har yanzu ba a fara gina manhajar Android da zubin Jaba na bakwai ma ba sosai, balle na takwas. Idan ka je za ka saukar da zubin Jaba na shida ne (Jaba 6, ko Jaba 1.6). Bayan haka, akwai nau’uka wajen uku ne – Jaba Runtime Enbironment, da Jaba EE, da Jaba SE. Sai ka saukar da Jaba SE, wato “Standard Edition” kenan. Bayan ka gama saukarwa sai ka loda (Install) wa kwamfutarka.

Manhaja ta biyu ita ce manhajar “Android SDK,” wato tubalin dake dauke da tsare-tsaren gina manhajar Android. Cibiyar aikin kenan, gaba daya. Wannan za ka same ta a gidan yanar sadarwar Android, kai tsaye. Sai ka saukar, amma bayan ka gama saukarwa (Downloading), ba loda (Install) wa kwamfutarka za ka yi ba, domin ba dunkulalliyar manhaja ba ce irin ta al’ada. Za ka nemi mahalli ne a ma’adanar kwamfutarka (Dribe C:), sai ka bude sabon burgamin adana bayanai (Folder), ka adana a ciki. Idan ba canza mata suna aka yi ba, za ka ga sunan kamar haka: android-sdk-windows. Da zarar ka adana wannan tubali a mahallinsa, sai ka zarce Intanet don neman makami na uku, wato allon rubutu kenan.

Manhaja ta uku ita ce allon rubutu, wato “Tedt Editor.” Akwai nau’ukansu da yawa. Amma wanda ya fi shahara, ya fi sauki, sannan ya fi dacewa da tubalin Jaba SE da ka saukar a fari, shi ne: Eclipse Tedt Editor, wanda ke dauke da abubuwa da dama masu sawwake aikin. Babban aikin wannan allon rubutu, kamar yadda mai karatu zai ga shafinsa a tsakiya, a kansa ne maginin manhajar zai yi ta tsara yadda yake son manhajar ta kasance, a rubuce. Bayan ya rubuta, ya yi gwaji, sannan ya yi ‘yan gyare-gyaren da suka kamata, akwai kwarangwal na wayar salula nau’uka daban-daban a jikin wannan allo, wadanda mai karatu zai rika amfani da su wajen gwaji.  Wadannan kwarangwal su ake kira “Mobile Emulator.” Duk abin da ka gina, sai ka kira wannan kwarangwal na wayar salula, ka loda manhajar a ciki, za ta nuna maka yadda manhajarka za ta bayyana a hakikanin wayar salula. Amma kafin ka kai ga wannan mataki na fara gina manhaja, sai ka saukar da makami na karshe.

Wannan makami kuwa ba wata manhaja ba ce mai zaman kanta, a a.  Qarin tagomashi ne, wato “Plugins.” Da zarar ka loda wa kwamfutarka wancan manhaja ta allon rubutu mai suna: “Eclipse Tedt Editor,” sai ka budo wannan allo, ka je sashen “Windows” dake sama ka matsa, sai ka gangara can kasa, ka latsa: “Android SDK Manager,” nan take zai fara saukar maka da wadannan bayanan tagomashi.  Wadannan bayanai ana kiransu “Eclipse Android Plugins” ne.  Aikinsu kuwa shi ne su tabbatar kana gina manhajar da ta dace da babbar manhajar Android dake dauke kan wayoyi ne.

Idan mai karatu bai mance ba, a baya mun yi bayani kan nau’in zubin Android, wato “Android Versions.” Wadannan nau’uka sun sha bamban, tunda ba lokaci daya aka gina su ba. Don haka, wannan dan aike mai suna “Android SDK Manager” shi zai saukar maka da dukkan bayanan da suka dace da kowane irin nau’in Android ne.  Domin da zarar ka yi yunkurin kirkirar sunan manhajar, tun kafin ka kai ga samar da sassanta, za a bukaci ka tantance nau’in Android din da kake son Manhajar da kake ginawa ta dace da ita. Sai dai kuma, idan kana saukar da wadannan bayanai, dole ne ka tanadi “Data” mai dimbin yawa, domin yana daukan lokaci, duk da cewa ya danganci nau’in bayanan da kake bukatar saukarwa. Da zarar ka gama saukarwa kuma, sai ka kama aiki.

Wannan kadan ne cikin abin da ya samu na bayani kan yadda za ka fara aiwatar da wannana aiki. Da fatan ka gamsu. Ina maka fatan alheri.

Sadaukar da Lokaci

Dayan biyu ne; ko dai ya zama ka kauki wannan fage ne don sha’awa kawai (hobby), don ka rika gina manhajoji kana amfani da su ko raba wa mutane su na amfani da su, ko kuma ya zama kana son daukan wannan fage ne a masayin sana’a. Zai iya yiwuwa kuma kana son farawa da matakin farko ne, daga baya, iya gwargwadon yadda ka ga ka kware, ka nausa zuwa mataki na biyu. Ko ma dai mene ne, dole sai ka sadaukar da kanka wajen wannan aiki. Domin fannin gina manhajar kwamfuta (Programming) ba fannin ‘yan kailula ba ne; ayi yau, ba za a sake dawowa ba sai bayan wata ko watanni. Idan ka fara karatu (a aji ne ko ta hanyar littattafai), dole ne ka ciyar da lokacinka a kowane lokaci; dare da rana safe da yamma. Karatu ne da ya shafi karantawa da kwatantawa. Duk abin da ka karanta, to dole ne ka kwatanta shi, don ilimin da fasahar da hikimar su tabbata a kwakwalwarka. Hakan kuwa ba zai yiwu ta dadi ba sai ka sadaukar da kanka.