Tambayoyi da sakonnin masu karatu ta Tes da Imel (5 – 6)

Assalamu alaikum Baban Sadik. Gaskiya sai dai muce Allah Ya biya da mafificin alheri game da ilimin da muke samu daga gareka. Kuma lallai za mu so a fara bamu ilmin programming kamar yadda ka kwadaitar da mu. Daga Yakubu Abdulkadir, Jihar Bauchi. Wa alaikumus salam, barka dai Malam Yakubu, daga Bauchin Yakubu. Ina matukar […]

Tambayoyi da sakonnin masu karatu ta Tes da Imel (5 – 6)

Assalamu alaikum Baban Sadik. Gaskiya sai dai muce Allah Ya biya da mafificin alheri game da ilimin da muke samu daga gareka. Kuma lallai za mu so a fara bamu ilmin programming kamar yadda ka kwadaitar da mu. Daga Yakubu Abdulkadir, Jihar Bauchi.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Yakubu, daga Bauchin Yakubu. Ina matukar farin cikin jin cewa abin da ake karantawa yana ba da fa’ida iya gwargwado. Dangane da bukatarka kuwa na samun mahalli na musamman don koyar da ilimin “Programming”, tabbas wannan alkawari ne da na dauka a watannin baya, cikin shekarar da ta gabata. Kuma a halin yanzu ina kan kokarin ganin na cika wannan alkawari nawa. Kada a mance, na yi alkawarin samar da gidan yanar sadarwa ne na musamman don yin hakan. Duk da cewa daga baya wasu cikin masu karatu sun shawarce ni da in fara samar da darussa na musamman don karantar da hakikanin kwamfuta da yadda take aiki tukun, wanda wannan ita ce asali ko tubalin da ake son duk wanda zai koyi wancan ilimi na “Programming” ya fara da shi, in yaso daga baya sai in dora kan wancan din.

Zan gina gidajen yanar sadarwa ne guda biyu; daya da harshen turanci, dayan kuma da harshen Hausa. Kuma a halin yanzu na mallaki adireshin gidajen yanar tuni, ina kan ginawa ne. Da fatan za a ci gaba da taimakawa da addu’a tare da kasancewa damu a wannan shafi mai albarka. Domin kasantuwarku na kara mini kwarin gwiwa a kowane lokaci. Na gode matuka, Allah saka da alheri, amin.

Assalamu alaikum ranka ya dade. Tamyata ita ce: shin, ko akwai wasu makarantun koyon ilmi kan na’ura mai kwakwalwa da ake koyarwa ba tare da wahala irin da kashe kudi masu yawa ba, a fili ko ta yanar gizo, kamar yanda ka fada a baya cewa: akwai karatu ta yanar gizo da ake yi kyauta tare da samun shaidar kammalawa ta yanar gizo. Ina fatan samun kammalallen bayani da amsa mai gamsarwa, tare da kasidun da aka rubuta daga shekarar 2015 zuwa yanzu. Ana iya turo amsar ta wannam Imel: [email protected].  Usama Namadina Umar.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Namadina. Dangane da samun kasidun da na rubuta a shekarar 2015, wannan sai dai ka ziyarci Taskar Baban Sadik dake: http://www.babansadik.com, a can na taskance dukkan kasidun da suka bayyana a wannan shafi, wanda na fara rubuta su tun shekarar 2006; shekaru 11 kenan a halin yanzu.  Akwai kasidu sama da 480 yanzu haka.  

Dangane da batun amsar da na bai wa wancan mai tambaya kan hanyoyin koyon ilmin kwamfuta ta Intanet na kyauta, lallai na buga bayanan a shafin jarida, watakila ka riski amsar da na baiwa wanda ya maimaita makamanciyar tambayar ne. Duk da haka, ga kadan daga cikin amsar da na bayar nan kasa:

“Lallai akwai shafuka ko ince “Makarantun” koyon ilimin kwamfuta kyauta a Intanet. Wadannan makarantu ko wurare dai sun kasu kashi-kashi; akwai na kudi, akwai na kyauta, akwai wadanda bayanan a rubuce suke – sai ka karanta – sannan akwai wadanda suke dauke da bayanan bidiyo ne tsantsa. Sai dai wani abu kuma, galibinsu, kashi 90 cikin 100, duk da harshen Turance suke. A wasu shafukan kuma, dole ne ka yi rajista kafin ka fara daukan darasi. Wasu shafukan na bayar da takardar shedar gama karatu, wasu kuma ba su bayarwa. Wasu na dauke da wuraren gwaji, wasu kuma ba su da wuraren gwaji, sai dai ka yi amfani da kwamfutarka.

Duk da ba dai ban san wani bangare kake son koyo ba, shafin da yafi kowanne shahara kuma yake baiwa masu bukatar koyon nau’ukan ilimi daban-daban (ba wai na kwamfuta kadai ba), shi ne shafi mai take: “Tutorials Point.” Wannan shafi ko makaranta tana dauke ne da rubutattun darussa da suka shafi fannoni daban-daban na ilimi. Duk wani fanni na kimiyya da kere-kere za ka iya koyonsu a wannan shafi kyauta. Kusan dukkan fannonin ilimin kwamfuta za ka iya koyonsu a wanan shafi. Sannan shafi ne dake koyar da kai a tsarin mataki-mataki; daga farko har zuwa karshe. Adireshin wannan shafi dai shi ne: www.tutorialspoint.com. Kana hawa shafin daga sama sai ka matsa: “Tutorials Library,” don zaban fannin da kake son koyo. Ko kuma ka gangara can kasa, za ka wani dogon jadawali mai dauke da dukkan fannonin da za ka iya koyo a wannan makaranta.  Duk na nuna cewa makaratar na dauke ne da rubutattun darussa, sai dai akwai bangaren darussan cikin bidiyo, sannan akwai bangaren kwatanta abin da ka koyo, idan ilimi ne mai dauke da koyo a aikace.  Misali, idan bangaren gidan shafin yanar Intanet kake son koyo (Web Design), akwai bangaren da za ka je ka kwatanta abin da ka koya a aikace, ba sai kana da kwamfuta ta kashin kanka ba.  Kana iya samun wannan wuri a shafin farko daga sama, can bangaren dama, mai take: “Coding Background.”

Idan kana son kuma inda zaka koyo nau’ukan kwamfuta musamman yadda ake gina manhajar kwamfuta ne (Programming) ne kai tsaye, daga farko har zuwa karshe, tare da takardar shedar karatu (Certificate), duk a kyauta, sai kaje shafi mai take: “Solo Learn.”  Wannan makaranta na daga cikin makarantu dake karantar da ilimi cikin sauki, tare da hanyar kwatanta karatun, cikin sauki.  Ba ma wannan kadai ba, ana karantar da kai ne mataki-mataki, cikin tsari mai dauke da nishadantarwa da saukin fahimta.  Ba a cika ka da tarin bayanai.  Rubutattun bayanai kadan ne, sai misalai birjik.  Cikin kankanin lokaci za ka koyi ilimi mai yawa, wanda ke dauka da dabbakawa.  Idan ka gama karatun nan take za a aiko maka da takardar sheda ta adireshin Imel dinka.

Amma dole sai ka yi rajista kafin ka fara daukan darasi.  Idan nace rajista ban nufin biyan kudi.  A a.  ina nufin za ka bude “account” ne.  Idan kuma ba ka son bude wani “account”, kana iya hawa da adireshinka na “Facebook” ko “Gmail,” kai tsaye, a duk sadda ka tashi shiga.  Bayan dukkan wannan, kana iya saukar da manhajar wannan makaranta a wayarka daga cibiyar “PlayStore” na wayoyin Adroid, sai dai kuma dole ne sai kana da Intanet za ka iya hawa a kowane lokaci.  Adireshin wannan shafi yana:  www.sololearn.com.

A daya bangaren kuma, akwai shafukan koyon ilimi ta hanyar bayanan bidiyo, su ma kyauta.  Wannan na samuwa ta hanyar shafin “Youtube” na kamfanin Google.  Wannan shafi na Youtube dai wata duniyar ilimi ce, mai dauke da kusan “kowane” nau’in ilimi kake bukata ko abin da ya dangance shi.  Jakar magori ce!  Idan kana da wayar salula irin ta zamani mai iya mu’amala da fasahar Intanet, to lallai baza ka rasa samun manhajar Youtube a kan wayar ba.  Ko dai ya zama wanda wayar tazo da shi ne (musamman idan Android ce), ko kuma ka same ta a cibiyar Play Store ko Store, idan nau’in “Windows Phone” kake amfani da ita.

Idan kuma da kwamfuta kake son hawa shafin, kana iya shigar da: www.youtube.com.  Da zarar ka hau, a sama daga tsakiya akwai inda aka tanada don yin “tambaya” (Search) kan nau’in ilimi ko bayanan da kake bukata.  Kada ka mance, galibin ire-iren wadannan ilimi dai cikin harshen turanci suke.  Don haka, duk tambayar da za ka yi ta zama cikin harshen turanci ce, kan wani fanni na ilimin kwamfuta kake son koyo.  Kana tambayowa kuma za a baka amsa bila-adadin.

Wadannan su ne wadanda zan iya baka shawarar ka lazimta a halin yanzu.  Ba wai iyakansu ba kenan, a a, suna da yawa.  Aika maka dandazonsu zai rikitar da kai, har ka kasa tabbatuwa a kan guda daya.  Idan ka lazimci wadannan, ka fa’idantu, da kanka za ka nemo kari, ba sai ka sake tambayar wani ba.  Allah sa a dace, amin.