Tambayoyi da tsokacin masu karatu (2)

Assalamu alaikum. Ina maka fatan alhairi da fatan Allah Ya kara basira. Tambayata ita ce; ina amfani da wayar Nokia nau’in E5 ne. To idan na saukar da manhajar 2go ba na iya shigar wa wayar. Duk sadda na yi kokarin loda mata sai a gaya min cewa: “Jaba failed…” ko “Authorisation failed…” da makamantan […]

Tambayoyi da tsokacin masu karatu (2)

Assalamu alaikum. Ina maka fatan alhairi da fatan Allah Ya kara basira. Tambayata ita ce; ina amfani da wayar Nokia nau’in E5 ne. To idan na saukar da manhajar 2go ba na iya shigar wa wayar. Duk sadda na yi kokarin loda mata sai a gaya min cewa: “Jaba failed…” ko “Authorisation failed…” da makamantan haka. Kuma duk manhajojin wayar lafiya suke, amma wannan ne ya ci tura. Na gode. – Ahmad Lawal

Wa alaikumus salaam, barka ka dai Malam Ahmad. Ina godiya da addu’o’inku. Wannan sako da kake gani yana nuna cewa wayarka ba za ta iya daukar nau’in bayanin da ka saukar ba kenan. Ko dai saboda haka aka tsara ta, ko kuma saboda gurbacewar bayanan a sadda k agama saukar da su. Abin da “gurbatan bayanai” ke nufi, wanda a harshen kimiyyar sadarwa ake kira “Data Corruption” shi ne lalacewar sa sadda ake kokarin saukar da su ko ta’ammali da su, sanadiyyar ko dai yankewar yanayin sadarwar Intanet a sadda ake saukar da su, ko kuma tasirin kwayar cutar kwamfuta (birus) da ke cikin ma’adanar da aka taskance su a ciki ko aka saukar dasu a ciki. Don haka, idan sadda kake kokarin saukar da manhajar 2go din yanayin sadarwar Intanet dinka ya yi ta yankewa, to, kana iya sake saukar da ita a karo na biyu, ta yiwu manhajar da ka saukar ta gurbace; wayar ba za ta iya sarrafa su ba balle ka amfana da hakikanin abin da bayanan ke wakilta na manhaja ko masarrafa don aiwatar da sadarwa. Idan kuma ka sake saukarwa ba tare da matsala ba amma duk da haka wayar ta ki dauka, to, alamar cewa manhajar ba ta dace da yanayin tsarin wayar ba kenan. Wannan shi ake kira “Incompatibility” a ilimin kimiyyar sadarwa na zamani. Da fatan ka gamsu.

Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan kana cikin koshin lafiya. Ga tambayata; idan na tura sakon Imail daga baya sai a aiko min cewa sak on bai je ba ga wanda na tura masa. Yaya zan yi da matsalar? Daga Umar Adamu Biriboy
Wa alaikumus salam Malam Umar, barka ka dai. A ka’ida, ya kamata a duk sadda aka aika sakon Imel, to, lalle ne ya tafi. Amma idan ka samu sanarwar cewa “Sakon da ka aika bai isa ga wanda aka aika masa ba,” – wanda dole ne a sanar da kai dalilin – to, dalilan ba su wuce dayan abubuwa biyu; ko dai ya zama adireshin da kayi amfani da shi wajen aikawa ba daidai ba ne, ko kuma a a, daidai ne, sai dai an rufe shi. Muddin aka aika skko zuwa adireshin Imel din da ba daidai ba ne, to masarrafar da ke karban sakonnin Imel din (Mail Serber) za ta dawo dashi nan take, babu jinkiri. Haka idan adireshin daidai ne, amma aka yi rashin sa’a an rufe jakar Imel din mai adireshin, wato “Deactibated” nan ma sakon zai dawo; tunda babu jakar Imel din a hakika. Don haka, nan gaba sai a kiyaye. A duk sadda za a rubuta sakon Imel, a tabbatar adireshin daidai aka rubuta shi, sannan a tambayi mai adireshin in za a iya, shin, yana amfani da Imel din ko a a? Idan har ya dauki tsawon watanni tara bai yi amfani da Imel din ba, to lalle babu makawa an rufe. Mafi karancin lokacin da ake rufe jakar Imel shi ne watanni shida. Mafi tsawon lokaci kuma watanni tara. Sai a kiyaye. Da fatan ka gamsu da wannan takaitaccen bayani.

Assalamu alaikum, barka da dare da fatan kana lafiya. Muna godiya akan kokarinka game da wayar mana kai akan harkar kwamfuta da waya. Gaskiya biyanka sai Allah. Tambayata a nan itace; don Allah Wi-Fi na aiki a Nijeria, kuma yana aiki a kan Android da Jaba? Kuma don Allah yaya ake aiki dashi ko saita shi? Da fatan za ka taimaka. Allah ya baka ikon taimakawa. Daga Lawal Ahmad
Wa alaikumus salam Malam Lawal, barka da warhaka. Ina godiya da addu’a, Allah saka da alheri, amin. Dangane da tambayarka, lallai tsarin Wi-Fi na aiki kuwa a Najeriya, sannan kuma yana nan a kan wayoyi masu dauke da babbar manhajar Android, da Windows Phone, iOS na kamfanin Apple. Ba ma wadannan kadai ba, hatta wayoyin salula na zamanin baya masu dauke da babbar manhajar Jaba da Symbian, akwai masu dauke da tsarin Wi-Fi. Abin da Kalmar “Wi-Fi” ke nufi shi ne, “Wireless Frekuency Radio,” wanda tsari ne dake killace yanayin sadarwa na zamani. Idan kana son ganin wannan tsari a wayarka mai dauke da babbar manhajar Android, ka je: “Settings”, a bangaren “Network Connections” za ka ga wannan tsari, sai ka kunna shi. Idan akwai na’urar Wi-Fi a inda kake, nan take wayarka za ta sanar da kai cewa: “Akwai tsarin sadarwar Intanet a nan, ta hanyar Wi-Fi. Shin, kana a son a jona ka da shi?” Idan ka ce eh, sai a jona ka. To amma sai ba dukkan tsarin Wi-Fi yake kyauta ba. Galibin wuraren da za ka je ka ci karo da wannan tsari za ka samu na wasu kamfanoni ne ko hukumar gwamnati, wanda dole sai an saita maka ta hanyar shigar da wasu kalmomi na sirri da suka kebanci kamfani ko hukumar da ke dashi. Da faran ka gamsu.

Assalamu alaikum, tambayata a nan ita ce; na kasance idan na sa na’urar ‘Wireless Bluetooth headphone’’ har ya jima a kunne na, sai kaina ya fara ciwo? Me ye dalili? – Abubakar Musa Abdullahi
Wa alaikumus salam, Malam Abubakar barka ka dai. Shawarar da zan baka ita ce: kayi kokari kaje ka ga likita. Domin alama ce dake nuna cewa akwai wata lalura ta musaman a kunnenka. Duk da cewa su kansu kamfanonin da ke kera kayayyakin sadarwa na zamani sukan nusar da mai amfani dasu cewa yawan sauraran sauti mai karfi wanda ya kai makura yana illa ga kunne da tsarin ji na dan adam. Kana iya ganin likita don ya duba ka, don tabbatar da hakikanin abin da ke damunka. Allah dada kiyayewa, amin.

Assalamu Alaikum Baban Sadik. Ina matukar gaisuwa a gareka. Ina son a yi min karin bayani akan manhajar Skype. Sannan ina son ka wayar mini da kai dangane da yadda ake gudanar da cinikayya ta hanyar Intanet, wato e-bussiness. Na gode a karshe ina son ka ba ni adirishin Imail din da masu karatu suke aiko maka da tambayoyinsu. Daga Bello Isiyaku Biri-Fulani, Jihar Gombe.
Wa alaikumus salam, Malam Bello barka da warhaka. “Skype” manhajar kwamfuta ce da ake amfani da ita wajen aiwatar da sadarwa ta hanyar rubutu (Tedt Chat), da murya (boice Chat) da kuma bidiyo (bideo Call/Chat). Akwai nau’in Skype da ke wayar salula, sannan akwai wanda ake dorawa a kan kwamfuta, kuma shi ne. Kafin ka iya aiwatar da sadarwa da manhajar Skype kana bukatar ka yi rajista (ta hanyar samun suna – username – da kalmar sirri – password) wadanda da su manhajar za ta rika sheda ka. Idan kana da jakar Imel na manhajar Hotmail kana iya amfani da wannan manhaja, domin kamfanin Microsoft ya saye kamfanin a halin yanzu. Haka kana bukatar lambar wayar salular wanda kake son magana ko hira ta hanyar bidiyo da shi, idan ba shi da adireshin Skype.

Za mu cigaba