Tambayoyi da tsokacin masu karatu (3)
A daya bangaren kuma, “E-business” tsari ne na aiwatar da cinikayya ta hanyar amfani da na’urori da hanyoyin sadarwa na zamani, ba wai ta hanyar Intanet kadai ba, kamar yadda ka fahimta. Nau’in “E-business” da ya kebanci Intanet shi ne amfani da gidan yanar sadarwa wajen aiwatar da kasuwanci. Ko dai ya zama kai ne […]
A daya bangaren kuma, “E-business” tsari ne na aiwatar da cinikayya ta hanyar amfani da na’urori da hanyoyin sadarwa na zamani, ba wai ta hanyar Intanet kadai ba, kamar yadda ka fahimta. Nau’in “E-business” da ya kebanci Intanet shi ne amfani da gidan yanar sadarwa wajen aiwatar da kasuwanci. Ko dai ya zama kai ne mai sayarwa, ko wanda zai je ya saya. Idan kana son gina “Shagon cinikayya” (E-business Portal) ta Intanet, dole ka tanadi gidan yanar sadarwa, wanda shi ne zai zama kamar shagon zuba hajarka. Wannan gidan yanar sadarwa dole ne ya kunshi dukkan hajojin da kake tallatawa, da bayaninsu, da yadda ake biyan kudi, da yadda bayan an biya kudi za ka aika wa wanda ya sayi hajar da hajarsa, cikin sauki da aminci. Bayan zuba bayanai kan haja da bayaninsu da bayani kan tsarin biya da karbar haja, dole ne kuma ka samar da taskar ajiya ta banki (Bank Account) wanda ta nan za ka rika karbar kudaden hajojinka. A zamanin baya galibin cinikayya a Intanet dole sai da dalar Amurka, shi ya sa a lokacin dole ne taskar ajiyarka ta banki ta zama mai daukar Dala ce, ba Nairan Najeriya ba, wato “Domiciliary Account.” Amma a yanzu tsarin ya canza, ko ta wayar salularka kana iya aiwatar da cinikayya na sayen haja ta amfani da katin bankinka, wato “ATM Card.” Wadannan su ne muhimmai cikin abubuwan da kake bukata don aiwatar da wannan cinikayya, bayan yin rajistar kamfaninka wajen hukuma. A karshe, adireshin da nake karbar sakonnin Imel daga gare shi shine: [email protected]. Sai na ji daga gare ka. Da fatan ka gamsu.
Assalamu alaikum Baban Sadik, me ake nufi da Computer Hacker, ko Hacking? – Abdulhamid Muhammad Alkali
Wa alaikumus salam, Malam Abdulhamid barka da warhaka. Abin da kalmar “Computer Hacker” ke nufi shi ne: mutum kwararre a fannin ilimin kwamfuta, wanda ya san ciki da wajenka, yake iya sarrafa ta ta hanyar da ya dace. Wannan kalma har wa yau ana amfani da ita wajen nufin wanda ke iya sarrafa kwamfuta wajen shiga da fita da aiwatar da kowane irin badakala da ita ko ta hanyarta, don cinma wata mummunar manufa. A ka’idar ilmin sadarwa, wanda ke amfani da kwarewarsa wajen cutar da mutane ta hanyar amfani da kwamfuta – wajen satar bayanai ta amfani da kwayar cutar kwamfuta da sauransu – shi ake kira “Cracker.” Amma “Hacker” mutumin kirki ne, mai amfani da iliminsa wajen amfanar da al’umma ta hanyar gyatta kwamfuta da samar da abubuwan amfani daga gare ta. Amma saboda wasu dalilai, kalmar “Hacker” ta fi shahara ga mutanin da ke amfani da kwarewarsu wajen cutar da al’umma ta hanyar kwamfuta. A daya bangaren kuma, “Hacking” shi ne sana’ar “Hacker.” Da fatan ka gamsu.
Salamun alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya Allah yasa haka ameen. Da farko suna na Muhammad Hashr, Bafulatanin Yola ne ni, daga jihar Adamawa, amma yanzu haka ina karatu a birnin New Delhi a kasar Indiya. Gaskiya ina matukar fa’idantuwa da wannan gudumawa taka a fannin Kimiyyar Sadarwa na Zamani, wato Information Technology. Allah Ya bada lada Ya kuma kara basira, amin. Ga ga lambar waya ta: +9871093803, don Allah ka tura mini taka ta inbod di na. Na gode. – Muhammad Elhash, New Delhi, India.
Wa alaikumus salam Malam Muhammad. Ina godiya matuka da wannan sako naka. Ina kuma rokon Allah Ya taimaka maka, ya kara maka fahimta wajen cin nasarar abin da ya kai ka wannan kasa. Na kuma tura maka nawa lambar. Sai ka ji ni. Allah saka da alheri, amin.
Salamun alaikum Malam Baban Sadik Allah Ya saka maka da mafificin alkhairi, amin! Allah Ya yi wa Sadik albarka. – Alhaji Isa Kanwa.
Wa alaikumus salam, godiya nake Malam Isa. Allah saka da alheri ya kuma albarkaceka kaima. Na gode. Na gode. Na gode.
Assalamu alaikum Baban Sadik. Yaya aiki? Allah Ya kara basira. A yau Alhamis da misalin karfe (7:59am) na samu sako daga wannan lambar;+2348178223365. Sakon na cewa “Ana taya ni murna da samun kyautar N950,000.00 (Naira dubu dari tara da hamsin). Wai a “Ongoing Dangote Promo…” inda suka ce in kira ita lambar don karbar wannan kyauta, wato 08178223365. Bayan na kira ya tambayi Ref number, na gaya masa kamar yadda na gani a sakon (Ref No:KF22C). A karshe ya ba ni zabi wajen karbar kudin kamar haka: a aiko mini ta hanyar “Money Transfer” a taskar ajiyar bankina, ko a tura ta tsarin “Courier Serbice Delibery?” Na zabi hanyar banki. A karshe ya ce sai na biya N4,000 (Naira dubu hudu) kafin a tura min. Ina neman shawara; in aika musu kudin ko a a? Amma fa a sakon babu wani adireshin Imel; lambar waya ce kadai. Idan kuma da yadda zan duba a kwamfuta ta don tabbatarwa sai a taimaka mini don Allah. – Prince Jameelu.
Wa alaikumus salam, Malam Jameelu wannan sako ne na bogi. ’Yan zamba-cikin-aminci ne (419) ke aiko wa mutane ire-iren wadannan sakonni. Ko kadan kada ma ka kuskura ka aika musu jawabi ta hanyar kira ko tes, balle har ka yi kokari ko tunanin aika musu kudi. Wannan Naira dubu hudu da ka ji sun bukata, idan ka ba su, karshen gaisawarka da su kenan idan masu imani ne. Amma idan kasurguman ne, marasa tausayi kuma suka fahimci ba ka gane kan gadon lamarin ba, suna iya sake bullo maka ta wate hanyar da za su ci kudinka cikin sauki. Don haka, duk wanda ya turo maka sako (galibi sun fi yi ta hanyar layin Etisalat da MTN, da lambar kasar Ingila) cewa ka ci wata reful ko wani abu makamancin haka, ka share, ka goge, kada ka amsa musu. Wannan ita ce shawara. Allah dada bamu kariya, amin.