Tambayoyi da tsokacin masu karatu ta imel (I)
A yau dai mun koma cikin taskarmu ne inda muka dauko sakonninku ta Imel. Wadanda suka rubuto sakonni ta hanyar wayar salula za su gafarce ni, domin wayar ta samu matsala, shafinta ya cire, sai na gyara sannan zan iya kaiwa ga sakonninku. Ina fatan za a yi mini afuwa kan haka. Wadanda suka bukaci […]
A yau dai mun koma cikin taskarmu ne inda muka dauko sakonninku ta Imel. Wadanda suka rubuto sakonni ta hanyar wayar salula za su gafarce ni, domin wayar ta samu matsala, shafinta ya cire, sai na gyara sannan zan iya kaiwa ga sakonninku. Ina fatan za a yi mini afuwa kan haka.
Wadanda suka bukaci kasidu na musamman ta wayar salula suna iya turo mini sakon Imel, zai fi sauki. Allah ya karbi ayyukanmu kyawawa, ya kuma yafe mana kura-kuranmu, amin.
—————————–
Assalamu alaikum, Baban Sadik wadanne hanyoyi mutum zai bi domin ganin ya kare shafinsa na Facebookdaga masu bude masa ba bisa ka’ida ba?Asha ruwa lafiya. Daga Nasiru Kainuwa Hadejia; 08100229688 – [email protected]
Wa alaikumus salam, barka da warhaka. Dangane da abin da ya shafi kare shafinka na Facebook daga masu yunkurin shiga, wannan abu ne mai mahimmanci. Akwai hanyoyi da dama da za ka iya bi wajen kare shafinka. Da farko dai ya zama ka sa “Password” mai tsauri, kada ka sanya lambobi ko haruffa sanannu wadanda kowa zai iya hararo su cikin sauki. Abu na biyu, kada ka taba baiwa kowa “Password” dinka, duk kusancinka da shi. In kuwa ka bashi saboda wani dalili mai karfi, da zarar dalilin ya kau, kayi maza ka canza “Password” dinka. Abu na uku, ka rika canza “Password” dinka lokaci-lokaci; ma’ana, kamar duk bayan wata daya ko biyu ko duk yadda ka tsara. Abin nufi dai shi ne, kada ka taba barin “Password” dinka iri daya tsawon lokaci. Hikimar a nan ita ce, ko da wani ya yi kirdadon “Password” dinka ya dace, kuma yana amfani da ita ba tare da saninka ba, da zarar ka canza shi ke nan, ya rasa.
Abu hudu, ya zama akwai matakan kariya a shafinka ta fuskar lambar waya ko adireshin Imel ko duk biyun. Ma’ana, ka shiga “Profile” dinka ka kara adireshin Imel dinka, sannan ka tabbata sun turo maka lambobin tantancewa, kuma ka samu har ka shigar, wato: “berification Code.” Haka ma idan lambar waya ka sa a “Profile” din, ya zama sun turo maka da lambobin tantancewa (berification Code) don tantancewa. Wannan zai sa ko wani ya yi yunkurin hawa, ba zai iya ba. Domin za a turo lambar canza “Password” ne zuwa adireshin da ke shafin ko lambar wayarka. Amma muddin kawai ka sanya lambar ce ko adireshin Imel ba tare da an turo maka lambobin tantancewa don tabbatar da cewa adireshin naka ba ne, hakan bai da bambanci da rashin sakawa. Duk wanda ya yi yunkurin hawa shafinka zai same shi cikin sauki; araha. Domin maimakon a bijiro masa da adireshin Imel da ka sa ko lambar wayarka don karbar lambobin canza “Password” (Password Reset Code), sai dai kawai a ce masa: “Wannan shafin ba a sa masa wata hanya ta kariya ba. Shigar da adireshin Imel ko lambar waya don canza ‘Password.’” Yana ganin haka zai sa lambar wayarsa ko adireshin Imel dinsa; daga nan ya mallake shafin ke nan kai tsaye.
Abu na biyar, dole ne ya zama lambar wayarka da adireshin Imel da kake amfani da su wajen hawa shafinka na Facebook su zama a killace; kada ka rika amfani da su a wasu shafuka daban. Domin idan cikin kuskure wani ya mallake shafinka guda, to, yana iya mallake sauran ma kai tsaye, tunda duk hanya daya kake amfani da ita wajen hawa da sauka. Abu na shida, ka tsare “Password” din akwatin Imel dinka da kake amfani da shi wajen hawa Facebook ko wanda kasa a “Profile” dinka. Amfanin hakan shi ne, ko da wani ya yi ta yunkurin hawa shafinka amma ya kasa, kuma hakan ya sa hukumar Facebook suka rufe shafin saboda ayyukan tuhuma da suka lura da su, a karshe idan ka zo hawa za a sanar da kai cewa wannan shafin na fuskantar tuhuma sanadiyyar ayyukan dandatsanci da aka lura da su a baya. Don haka, ana son ka tabbatar da cewa kai ne mai shafin, ta hanyar bayar da wasu bayanai, ciki har da adireshin Imel da ke kan “Profile” dinka. Ta wannan hanya za su aiko maka da bayanan bude shafin. Ka ga idan ka bar “Password” dinka galala, ko ya zama ba ka shafin Imel din har suka kulle, a yanayi irin wannan sai dai ka hakura da shafin, domin ba ka iya isa ga akwatin Imel din balle ka ga sakon da suka aiko maka wanda zai taimaka wajen bude shafin.
Abu na bakwai, ka yi amfani da hakikanin sunanka. Idan ma kana son amfani da lakabi ko alkunya (kamar “Baban Sadik” ko “Abu Aisha” misali), to, ya zama a kasan lakabin ko alkunyar akwai hakikanin sunanka. Wannan na da fa’ida guda biyu; na farko duk wanda ke nemanka, kuma bai sanka da lakabin ba, zai iya gane ka cikin sauki. Na biyu, idan shafinka ya samu matsala har hukumar Facebook suka rufe shi, idan ka bukaci a bude maka, za a bukaci ka aiko da hoton fasgo dinka (Passport), mai dauke da hakikanin sunanka, da jinsinka, da kuma ranar haihuwarka. Ka ga idan alkunya kawai ka yi amfani da shi, za a samu matsala. Don haka, ya zama rajistan farko da za ka yi, sunanka ne na hakika.
Abu na takwas, kasan irin abokan da za ka rika yi. Sannan ka san irin zantukan da za ka rika fada a yayin da kake hira da abokan da musamman ta hanyar Facebook ne kadai ka sansu ko ka hadu da su. Duk wani zance ko bukata da za ta danganci wasu bayananka na kusa-kusa – kamar a tambayeka me ka fi so a rayuwarka? Yaushe ne ranar haihuwarka? Da wace lambar waya kake hawa Facebook? – dole ka yi taka-tsantsan wajen bayar da wadannan bayanai. Domin a sane yake cewa da yawa cikin mutane sun fi amfani da ire-iren wadannan bayanai a matsayin “Password” dinsu.
Wadannan, a takaice, su ne zan iya hararowa, masu saukin fahimta daga cikin hanyoyin da za su taimaka wa mai mu’amala da shafukan sada zumunta, ba wai Facebook kadai ba, wajen kare shafinsa daga fataken dare. Allah Ya sa a dace, amin.