Tambayoyi da tsokacin masu karatu ta imel (II)

A wasu manyan wayoyi muna ganin wani manhaja mai suna Wi-Fi. Shin, mene ne aikinta a aikace?  Daga Mainasara Nasarawa Funtuwa; 08034208356 – [email protected] Wa alaikumus salam, barka dai Malam Mainasara.  “Wi-Fi” manhaja ce da ke taimakawa wajen hada wayar salula ko kwamfuta da yanayin sadarwa na Intanet a inda mai wayar ko kwamfutar yake.  […]

Tambayoyi da tsokacin masu karatu ta imel (II)

A wasu manyan wayoyi muna ganin wani manhaja mai suna Wi-Fi. Shin, mene ne aikinta a aikace?  Daga Mainasara Nasarawa Funtuwa; 08034208356 – [email protected]

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Mainasara.  “Wi-Fi” manhaja ce da ke taimakawa wajen hada wayar salula ko kwamfuta da yanayin sadarwa na Intanet a inda mai wayar ko kwamfutar yake.  Idan wannan masarrafa a kunne take, da zarar ka zo inda yanayin sadarwa na Intanet yake (wato “Wireless Connections”) nan take wayar za ta hango su.  Idan na kyauta ne kana iya amfani da su ta hanyar latsa kowanne daga cikinsu, sai kaje “Connect” ka matsa, wayar za ta jonu da wannan yanayin sadarwa, har ka iya mu’amala da Intanet a wajen.  Amma da zarar ka bar wurin wannan yanayi na sadarwa zai dauke.  Kamar tsarin sadarwar wayar salula ne.  Kana iya kira ko amsa kira ne a wurin da akwai yanayin sadarwa (Network Connection), amma idan ka bar wurin shi ke nan, sai a yanayin ya dauke.  
Idan kuma yanayin sadarwar da ke wurin kaje tsararre ne (Secured Connection), dole sai an shigar maka da kalmar shiga, wanda babu mai saninsu kuwa sai wadanda suka mallaki yanayin sadarwar.   
Bayan wannan nau’i na Wi-Fi wanda shi ne shahararre, akwai wata manhaja kuma da wayoyin zamani ke zuwa da ita mai suna: “Wi-Fi Direct,” wacce ta sha bamban da wanda bayaninta ya gabata.  Ita wannan aikinta shi ne taimakawa wajen aikawa da sakonni tsakanin wayoyin salula.  Tana da inganci sosai, domin ko sako ya kai 1G, kana iya aika shi cikin kasa da minti guda.  Wannan ita sabuwar fasaha mai inganci, wacce ke zuwa a wayoyin salula masu dauke da babbar manhajar “Android” misali.  Idan kaje bangaren “Network Connections,”daga gefe za ka ga wasu layuka kamar guda uku a tsaye daga sama, sai ka latsa, jerin bayanai za su budo; ka gangara na karshe ko kusa da karshe, ka latsa “Wi-Fi Direct.”  Wannan manhaja na aiki ko da babu katin SIM a waya.  Ba abin da ya hada ta yanayin sadarwar waya (Network Connection).  Amma a lura, ba a amfani da ita wajen shiga Intanet; ba kamar “Wi-Fi” bace.Da fatan ka gamsu.
Assalamu alaikum, barka da warhaka, da fatan kana cikin koshin lafiya. Na dade ina bibiyar wannan shafi na Aminiya kuma ina ilmantuwa da abubuwa masu yawan gaske a wannan shafin kimiyya da fasaha, kuma ina fatan Allah ya kara maka basira da karfin gwiwa. Sannan kuma ina so don Allah ka turo ko aiko mini kasidar Bamuda (Bermuda Triangle) ta akwatin e-mail dina:[email protected].  Kuma idan akwai wani dandali na shafin Whatsapp ina so a saka ni don in cigaba da ilmantuwa.  Nagode.  Daga Junaidu Maje Suleja.  07050819993
Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Junaidu.  Dangane da kasidar Tsibirin Bamuda, na aika maka kai tsaye.  Sai ka duba akwatin Imel dinka.  Abin da ya shafi wani zaure na musamman a Whatsapp kuma, sai ince babu.  Domin ba ni da cikakken lokacin da zan iya karbar sakonni da tambayoyi da bukatun jama’a kai tsaye.  Bude zaure a Facebook ko a Whatsapp yana bukatar kulawa a kodayaushe.  Ni kuma yanayin aikina ba zai barni ba.  Watakila dai zuwa wasu lokuta nan gaba idan na samu saukin yanayi da hali.  Na gode da addu’o’inku, Allah ya saka da alheri, amin.
Allah Ya saka da alhairi.  Ka taimake ni da rubutun da kayi kan manhajar Whatsapp da Facebook da Imo da Too da 2go da Tweeter da sauransu. Wannan shi ne maudu’in bincike da nake yi don samun kammala digirin digirgiri da dingirewa, wato: PhD ke nan.  Taken binciken shi ne: “Adaption of Smartphone on Students’ Academic Performance.”  Bincike na musamman don gano tasirin amfani da wayar salula ta zamani (Smartphone) ga dalibai kan kokarin karatunsu.  A halin yanzu ina makaranta a daya daga cikin kasashen gabashin Afirka. Don Allah, duk wani rubutu da kayi kan wayar salula ta zamani (Smartphone) ina matukar bukatarsa, bayan na wadancan hanyoyin sadarwa ke nan.Allah Ya saka maka da alheri ya kuma kyautata maka kamar yadda kake kyautata mana.  [email protected]
Wa alaikumus salam, barka da warhaka.  Ina godiya da addu’a (Dr.) Haruna Shika.  Allah Ya saka da alheri.  A mini afuwa saboda rashin samun damar aika sakonnin sa’adda aka bukace su.  Na dauka kana Zariya ne, ashe kana can.  Allah Ya  tabbatar da alheri, ya baka nasara kan abin da kake yi, Ya kuma sanya Ya zama haske da dalilin gyara ga al’ummarmu musamman, amin.  Na aika maka kasidun da nake da su.  Alal hakika ban yi rubutu daya-bayan-daya kan kowanne daga cikin wadannan nau’ukan hanyoyin sadarwa ba.  Wadanda na killace da bincike dai su ne: Facebook da Whatsapp, sai kuma bangaren hakikanin tsarin gudanuwar wadannan madaukai.  Wannan, a tunanina, shi ne abin da ya fi fa’ida.  Domin idan ka fahimci yadda hanyoyin sadarwar ko wadannan dandalin abota ke gudanar da shafukan da yadda ake mu’amala da su ta bayan fage, fahimtar duk wata matsala da ka iya tasowa ba zai zama da wahala ba.  A takaice dai, na aika maka kasidu iya gwargwadon yadda zan iya fahimtar maudu’in bincikenka.  Sai ka duba, idan akwai wani bangare da babu, ka sanar da ni, in akwai zan turo maka.  Idan babu zan iya kalato maka su ta amfani da kwarewar da Allah ya hore mini, a shafukan Intanet.
Allah Ya agaza maka, ya yalwata maka fahimta da basira, ya kuma sa a dace baki daya, amin.
Assalaamu alaikum Baban Sadik.  Bayan gaisuwa mai dimbin yawa. Da kuma fatan iyalinka lafiya. Allah Ya sa haka amin. Don Allah ka taimaka ka kara turo mini kasidar tsibirin BermudaTriangle, wadda ka turo mini a baya ta goge. Ban san yadda aka yi ta gogeba. Na gode. dalibinka, kuma mai karuwa da kai a kullum, Ahmad Aliyu Alkashnawiy.
Wa alaikumus salam Malam Ahmad.  Barka da warhaka.  Ina kyautata zaton ko dai ka goge kasidar ne cikin kuskure.  In kuma ba haka ba, to, watakila ta fada cikin jakar  “Sakonnin Bogi” (Spam Mails).  Duk da haka dai, na sake tunkudo maka kasidar kamar yadda ka bukata.  Allah Ya sa a dace, ya kuma kara mana basira, amin.
Salamun alaikum Baban Sadik. Muna jin dadin rubuce-rubucen da kake yi a kan abin da ya shafi kimiyya.   Allah ya kara basira. Don Allah Baban Sadiki ina so ka turo mini da wasu daga cikin rubuce-rubucenka da za su amfanar da ni ssosai, musamman ‘Tsibirin Bamuda’ da ‘Hanyoyin Mu’amala da Password’ da ma wasunsu ta wannan email din. Na gode sai na gasakon. – [email protected]
Wa alaikumus salam, barka dai.  Ina godiya da addu’o’inku matuka.  Allah Ya saka da alheri, amin.  Ka duba akwatin Imel dinka, na tunkudo maka kasidun.  Allah Ya kara basira, ya kuma sa mu dace baki daya, amin.