Tambayoyi da tsokacin masu karatu ta imel (III)

Salaamun alaikum, barka ka dai.  Ganin cewa shafin sada zumunta na Facebook ya kayyade yawan abokan hulda guda 5000, shin ko akwai wata hanyar kara wasu yawan abokai kuwa? Daga Mainasara Nasarawa Funtua.08034208356- [email protected] alaikumus salam Malam Mainasara.  Kafin wannan tambaya taka, da yawa cikin mutane sun sha aiko tambaya makamancinyarta ko a rubuce ko […]

Tambayoyi da tsokacin masu karatu ta imel (III)

Salaamun alaikum, barka ka dai.  Ganin cewa shafin sada zumunta na Facebook ya kayyade yawan abokan hulda guda 5000, shin ko akwai wata hanyar kara wasu yawan abokai kuwa? Daga Mainasara Nasarawa Funtua.08034208356- [email protected]
Wa alaikumus salam Malam Mainasara.  Kafin wannan tambaya taka, da yawa cikin mutane sun sha aiko tambaya makamancinyarta ko a rubuce ko ta hanyar kira.  A gaskiya babu wata hanya a dai yanzu.  Hukumar Facebook sun kayyade kowane mai shafi ya mallaki abokai 5,000 ne kadai.  Zai iya yiwuwa nan gaba su kara, ko kuma ma su rage, ko kuma su barshi yadda yake yanzu.  Komai na iya faruwa.  Bayan haka, watakila idan ka bincika cikin Intanet za ka yi ta ganin ana tallata wasu manhajoji na sayarwa masu taimaka wa mutane kara yawan abokansu a Facebook.  In har ka ci karo da su, kada ka saurare su, domin shafukan bogi ne.  ‘Yan damfara ne suka mallake su, kuma idan ka bi tasu, komai na iya faruwa.
Mu sani, hukumar Facebook sun tanadi manyan kwamfutoci ne da ke taskance dukkan bayanan da muke musayarsu a shafukanmu; rubutattun sakonni, da hotuna, da kuma bidiyo.  Sannan kar mu mance, akwai tallace-tallace da ake ba su, wadanda suke gicciye su a gefen shafukanmu ta bangaren dama ko hagu ko tsakiya. Dukkan wadannan bayanai suna makare ne a kwamfutocinsu. A ka’idar sadarwa, idan bayanai suka yawaita a cikin mizanin kwamfuta, kuma ya zama a kowace dakika sai an bukace su ta hanyar Intanet daga wurare daban-daban, ta amfani da manhajoji daban-daban, da na’urori daban-daban, dole masu shafin su rika taka-tsantsan wajen kokarin fadada manhajar ko shafin.  Idan ba haka ba, za a iya wayar gari ma mutane su nemi shafukansu su kasa shiga, saboda kwamfutar ta kwanta da dama.
Don haka, abin da hukumar Facebook ke yi shi ne, suna lura da yawan jama’ar da ke dauke kan rumbun bayanansu ne, da mizanin ma’adanar kwamfutocinsu, da kuma yadda za su iya saukake hanyar isa ga bayanai ba tare da tsaiko ba.  Na yi cikakken bayani cikin kasida mai taken: “Yadda Dandalin Facebook Ke Gudanuwa.” Idan muka dubi yadda suke canza tsare-tsaren da ke zaurukan Facebook (Facebook Groups) za mu fahimci hakan cikin sauki.  Don haka, zai iya yiwuwa nan gaba su kara yawan abokai – ko dai ga kowa da kowa  ko kuma ga masu bude sabon shafi – ko kuma su ma rage yawan abokai – ko dai ga kowa da kowa ko kuma ga masu bude sabon shafi – ko kuma, a karon karshe, su barshi yadda yake.  Komai na iya faruwa.  Da fatan ka gamsu.
Assalamu alaikum Baban Sadik da fatan kana lafiya.  Don Allah ina son ayi mini bayani a kan wadannan kalmomi: 1) Energy2) Matter 3) Electronic debice 4) Emission theory. Daga dalibinka Hassan Muhammad Maiduguri Borno State: 08037327741 – [email protected]
Wa alaikumus salam, barka dai Malam Hassan.  Kalmar “Energy” dai a fannin kimiyya tana da ma’anoni daban-daban; ya danganci bangaren da ake magana a kai.  Amma a takaice dai, kalmar na nufin “Makamashi” ne, wanda ke taimakawa wajen aiwatar da aiki.  Kafar samar da makamashi a wannan duniya tamu dai gaba daya ita ce rana.  Akwai makamashin rana, wato “Solar Energy”, akwai makamashin Nukiliya, wato “Nuclear Energy”, akwai makamashin aikin karfi irin na jiki ko na’urorin aiwatar da ayyuka da karfin cin tuwo, wato “Mechanical Energy, sannan akwai makamashi a bangaren sinadaran da ke shawagi a wannan duniya tamu, wato “Chemical Energy.”  
Kalmar “Matter” kuma na ishara ne ga duk wani sinadari da ke dauke a mahalli kuma yana da kima wajen nauyi.  A Hausance Marigayi Malam Hambali Junju ya fassara wannan kalma da cewa ita ce: “Madda.”  Kamar kalmar da ta gabaceta, ita ma tana da fuskoki daban-daban.  Ya danganci bangaren da ake magana a kai.  Hakan ne zai tabbatar da irin ma’anar da ta cancanci a bata.
Kalmar “Electronic Debice” kuma na nufin na’urar lantarki ne.  Wato duk wata na’ura da za a iya jona mata makamashin lantarki kafin tayi aiki, ita ake kira da wannan suna.  Wannan kuwa ya hada da kwamfuta, da wayar salula, da injin wanke tufafi, da na’urar lissafi, da rediyo mai amfani da wutar lantarki kai tsaye, da dai sauransu.
Kalmar “Emission Theory” kuma ka’ida ce ta kimiyya da ke binciken alakar da ke tsakanin gudun haske da kuma karfin gudun asalin hasken. Ana danganta wannan ka’idar kimiyya ce ga mashahurin malamin kimiyyar nan wato Isaac Newton.  Wannan ka’ida tana dauke ne da fannoni biyu na kimiyya.  Fannin farko shi ne fannin binciken alakokin da ke tsakanin sinadarai.  Wannan yana dunkule cikin ka’idar da ake kira: “Relatibity Theory.”  Daga nan fannin kuma shi ne bangaren lantarki ko haske da tsarin sauyawarsa a yayin tafiya.  Wannan shi ne ke dunkule cikin ka’idar “Electrodynamics Theory.”  Bayan samar da wannan ka’ida dai, da dama cikin masana binciken kimiyyar haske da lantarki da alakokin da ke tsakaninsu wajen tafiya ko gudu, sun gano kura-kurai cikinta, wannan ya sa a baya masana irin su: Albert Einstein suka yi mata gyaran fuska.  Da fatan ka gamsu.
Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya.  Tambayata ita ce: na bude shafin Facebook da wannan lambar: 07016004360, sun kuma turo mini berification code komaidai ya yi, har na yi abokai da yawa, to amma daga baya sai na mance “Password” din.  Da na bukaci in canza “Password” din sai a ce mini an turo“Code,” amma shiru.  To sai daga baya na kara duba lambar da na yi rajista da ita, sai na ga ta koma: 09021973335.   Don Allah a taimaka mini da yadda zan yi in gyara wannan matsalar.  – [email protected]
Wa alaikumus salam, barka dai.  Na duba wannan matsala kuma na yi ta kiran layin wayarka da ka bayar,  amma wayar a kashe.  Abin da nike iya fahimta shi ne, akwai wanda ya san “Password” dinka; ko dai ka taba ba shi ko ya sani ta hanyar kirdado.  Wannan ta sa ya canza “Password” din naka zuwa abin da yake so; ya mallake shafin ke nan.   Shi ya sa idan ka yi kokarin hawa ka ga, bayan lambarka, ga wata lamba kuma daban.  Shi ne ya sanya lambar.  Don haka na so mu yi magana da kai.  Za a iya maido shafin kuma a goge lambar wayarsa da ya sa.  Bai kamata in yi wannan batu a shafin jarida ba.  Idan ka samu karanta wannan bayani, sai ka kira ni.  Amma fa ka tabbata har yanzu kana amfani da lambar wayar da ka bude shafin da ita.  In kuwa ba haka ba, to, ya ci bulus ke nan.  Allah ya kare nagari daga mugu, amin.
Assalamu alaikum Baban Sadik. Da fatan kana lafiya.  Muna godiya da jinjina da fatan Allah ya kara basira. Baban Sadik ina meman shawararka.  Na kasance ina sha’awar sarrafa kwamfuta.  A halin yanzu ina kokarin tafiya makaranta don cimma wannan buri.  Ina neman shawara gareka a kan wane bangare ne ya fi muhimmanci in kutsa masa a fannin?  Nagode.  Isa Abdullahi Kumo.  [email protected]
Wa alaikumus salam, barka dai.  A gaskiya akwai fannoni da dama a wannan bangare.  Ban kuma san mece ce kwarewarka ba.  Ba zan iya cewa ga fannin da shi ne ya fi dacewa da kai ba.  Da a ce ka rubuto mini bangaren da ka fi shahara ne a kai, nan ne zan iya bayar da shawara.  Sai dai in shawarceka da ka nemi shawara wajen daya daga cikin malaman da ke karantar da ku, domin shi yake tare da ku kuma ya san kwarewar kowannenku.  Don haka, zai iya ba ka shawara.  Idan kuma ka fi samun natsuwa da tawa shawarar, kana iya aiko mini da cikakken bayani kan tsarin karatun, da kwarewarka a kowane fanni.  Ina yi maka fatan alheri a kodayaushe.
Salam Baban Sadik, nadade ina bibiyar wannan ilimin da Allah ya hore maka kuma kake amfanar jama’armu da shi. Don girman Allah ka taimaka min da kasidarka mai albarka mai taken:Tsibirin Bamuda da kuma ta bincike a kan Internet. Allah Ya kara basira, Amin Summa Amin. Daga, Yau Nuhu Tumfafi, Kasuwar Dawanau, Kano.  Y. N. Tumfafi – [email protected]
Wa alaikumus salam, barka dai.  Ina godiya da addu’ar da ka mini.  Ka duba akwatin Imel dinka na aika maka kasidun da ka bukata.  Allah kara basira ya kuma sa a dace, amin.
Assalamualaikum Baban Sadik. Da fatan ana lafiya da kai da masoya gaba daya Amin. Tambaya nike da ita: ni da abokina muka dan yi wata ‘yar takaddama; ya ce wai akwai wani gini a wata kasa, saboda tsawonsa mutanen dake karkashinsa idan ana ruwan sama ba su sani.  Kuma wai ginin ya haura gajimare.   Shin, haka ne? Tambaya ta biyu, ni dalibine a fannin ilimin kwamfuta, ta yaya zan sanya wa “Folder” Password? Ka huta lafiya.  Daga Aminu Salisu.  – [email protected]
Wa alaikumus salam, barka da warhaka.  Dangane da tambayarka ta farko, a gaskiya ban taba sanin wani gini a duniya makamancin haka ba.  Da a ce ya ambaci sunan ginin da gari ko kasar da ginin yake, hakan zai fi bayar da damar gudanar da bincike don gano hakikanin gaskiyar lamarin.  Amma a haka ba zan iya cewa komai ba.  Tambayarka ta biyu kuma na bukatar zuba wasu bayanan gina manhajar kwamfuta (Source Code) masu tsawo, don kwatanta maka yadda ake sanya wa “Folder”.  Don haka, ka duba akwatin Imel dinka na aika maka wadannan bayanai da hanyar da za ka bi wajen zartar da su.  Allah ya sa a dace, amin.
Malam Baban Sadik, Allah ya kara basira. Da fatan kana cikin koshin lafiya tare da amincin Allah a tattare da kai.  –  [email protected]
Alhamdulillah, ina godiya matuka da addu’arka.  Allah ya saka da alheri, ya kuma bar zumunci.  Na gode!  Na gode!!  Na gode!!