Tambayoyin Duniyar Ma’aurata

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga amsoshin wadansu daga cikin tambayoyin da masu karatu suka aiko. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga masu bukatarsa musamman wadanda suka aiko da wadannan tambayoyi, amin.Tambaya ta 1: Don Allah ko amfani da magungunan mata (hakkin maye) […]

Tambayoyin Duniyar Ma’aurata
Tambayoyin Duniyar Ma’aurata

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga amsoshin wadansu daga cikin tambayoyin da masu karatu suka aiko. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga masu bukatarsa musamman wadanda suka aiko da wadannan tambayoyi, amin.
Tambaya ta 1: Don Allah ko amfani da magungunan mata (hakkin maye) na iya kawo matsala ga zamantakewar auratayya? Ko suna da illoli ga ma’aurata?
Amsa: kwarai kuwa, hakkin maye na haifar da matsaloli sosai ga zamantakewar ma’aurata: akwai labarai daban-daban da mukan ji na irin yadda hakkin maye ke gurbata zamantakewar ma’aurata wata sa’in har yakan yi sanadiyyar mutuwar aure.
Illolin Hakkin Maye Ga Zamantakewa Ma’aurata:
Hakkin maye kan zama sanadin rashin yin adalci ga namijin da ke da mata sama da daya, sai ya kasance maigida ya like wa mai amfani da wadannan kayan mata ya ki kula sauran.
Wata sa’in mace za ta sha wadannan kayan cikin tsammanin kasantuwar ibadar aure a wannan rana ko lokacin da ta sha su, idan aka samu akasi kuma sai sai hakkin mayen da ta sha ya zame mata matsala, wadansu har ’yar karamar hauka yakan haifar musu.
Takan faru kuma wata sa’in maigida ya ji canji a dandanon ibadar aure saboda Uwargida bata samu ta sha hakkin mayen, wannan sai ya haifar da jin haushinta kuma kimarta da darajarta sai su ragu wajen Maigida.
Sannan yana sa mata cikin talauci saboda duk kudin da suka samu, wajen hakkin maye yake karewa kuma kodayaushe suna fargaban yadda za su yi su samu kudin sayen wani, wannan ke sa wasu yawan cin bashi, kullum ana kan yi musu aiken biyan bashi, wata sa’in ma a gaban mazan nasu. Wasu kuma hakan ke kai su ga ha’intar mijinsu ta kudin cefane, ko wani abun, duk dai don su samu su samu kudin sayen hakkin maye.
Illolin Hakkin Maye Ga Lafiyar Ma’aurata:
Da farko dai ba kwakwaran binciken kimiyya da ya tabbatar da inganci ko rashin hadarin hakkin maye ga lafiyar jikin dan Adam, ana dai shan su ne haka kawai.
Sannan yawan shan magunguna barkatai, na tsawon lokaci babban hadari ne ga lafiyar jiki, domin sinadaran da ke cikin magungunan hakkin maye na iya taruwa cikin hanta ko koda, kuma hakan na iya rage musu karfin aiki ko ma ya lahanta su gaba daya.
Sannan idan kwayoyin sinadarai daban-daban suka hadu cikin jini suna iya yin barna maimakon gyaran da ake so su yi: wani na iya inganta aikin wani; wani ya dakile aikin wani sinadarin, wanda aikinsa mai muhimmanci ne ga jiki, wani kuma na iya shiga cikin wani su rikida su haifar da wani sinadarin daban, wanda ka iya zama illa ga daukacin lafiyar jiki.
Sannan akwai wadanda yawan shan su na haifar da ballewar jini a ‘yanmatancin mace; haka kuma akwai masu sa kuraje ko maruru su bayyana a gaban mace; akwai masu sa kaikayin gaban mace da sauransu.
Akwai hakkin maye mai bugar da mata idan sun sha shi, ta yadda ko sallah ba su iya yi sai ya sake su, irin wannan, tabbas shan sa haramun ne.
Sannan yawan shan hakkin maye na sa yawaitar sinadarin ‘nitrate’ cikin jini wanda ke haifar da  kumburin jiki.
Da yawa ana alakanta yawan cututtukan kaba da cutar daji ta mahaifa da sauran tsire-tsire na kwayoyin cuta ga yawan amfani da hakkin maye da ya zama ruwan dare ga matan wannan zamanin.
Tambaya Ta 2: Ina da mata daya, gashi kuma ni mai yawan bukata ne, ita kuma maidakina ba ta da yawan bukata, duk lokacin da na yi mata maganar zan kara aure sai ta hada rai saboda kishi. Ga shi ni kuma ina gudun fada wa hanyar shaidan; mene ne abin yi?
—Babangida U. Kano.
Amsa: Ai ba wani abin yi da ya wuce kawai ka cije ka je ka kara aurenka, in ka biye ta kishin matarka ba za ka taba kara aure ba. Kuma tun farko ma ka yi kuskure da kake mata maganar karin aure, abin da ya fi dacewa shi ne, ka je ka nema, in an dace magana ta daidaita, sannan ka sanar da ita wannan shi ne mafi alfanu. Da fatan Allah Ya tsare ka tare da dukkan Musulmi daga fada wa cikin hanyar shaidan, amin.
Sai sati na gaba sauran amsoshin tambayoyinku na zuwa in sha Allahu. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.