Tambayoyin Duniyar Ma’aurata (10)
Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaba a kan amsoshin tambayoyin da masu karatu suka aiko, da fatan Allah ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa musamman wadanda […]
Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaba a kan amsoshin tambayoyin da masu karatu suka aiko, da fatan Allah ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa musamman wadanda suka aiko da tambayoyin, amin.
Tambaya Ta 27: Mutum ne yake son karin aure, sai ya je wajen boka don neman sa’a, sai bokan ya zaba masa irin matar da zai aura, wai idan ya aure ta zai sami budi ya yi arziki. An nasihantar da shi cewa irin wannan auren haramun ne babu kyau, sai ya ce ko wanne aure mai kyau ne ba wani aure maras kyau. Shin abin da ya fada gaskiya ne? Kuma in ya kasance ya sami arziki bayan auren kamar yadda bokan ya fada za a iya zama a ci a matsayin halal?
Amsa: Abin nan da ya fada, cewa ko wanne aure mai kyau ne, ba gaskiya ba ne, domin kyakkyawar niyya ita ce take sa aiki ya kyautata; don haka komai kyawun aiki, idan niyya ba ta kyautata ba to aikin ma ya baci kuma babu lada ko albarka a cikinsa. Ana yin aure ne da kyakkyawar niyya domin Allah da raya Sunnar Manzonsa Sallallahu Alaihi Wasallam da tsare farji daga aikata alfasha. Auren mace don neman sa’ar zama mai arziki ba ya cikin halartacciyar niyyar yin aure. Haka nan zuwa wajen boka kadai, ko da mutum bai yarda da zancen da bokan ya sanar da shi ba haramun ne,kuma Sallar mutum ta kwana arba’in ya yi asarar ta, ba a karbarta. Sannan zuwa wajen boka da malaman tsibbu, da yarda da maganganunsu da aiki da umarninsu shirka ce mai girma wadda idan mai yin haka ya mutu ba tare da ya tuba ba Allah Madaukakin Sarki ba zai taba gafarta masa ba. Don haka haramun ne bayar da aure ga mutum mai irin wannan shirka mai girma.
Sannan in har bayan ya yi wannan auren ya kasance ya samu arzikin, to in dai ta hanyar halal ya samu arzikin, kamar ta hanyar yin kasuwanci cikin halartacciyar hanya; ba ta mummunar hanya ba, to ya halatta a zauna a ci wannan arzikin tare da shi. Domin Allah Yana iya jarrabarsa da budewar arziki bayan auren, wanda hakan zai sa ya kara yarda da zancen bokan nan, hakan kuma zai kara dulmiyar da shi cikin halaka.
Amma idan an tabbatar ta mummunar hanya ya sami arzikin, kamar satar kudin gwamnati, cin hanci da rashawa, kudin riba ko kudin caca, to bai halarta a zauna a ci kudin nan da shi ba ko da kuwa bai hada da aikata shirka ba. Domin Allah ba ya karbar aiki sai mai tsarki, komai kyawun aiki in an hada shi da haramun ya zama gurbatacce, kuma duk gangar jikin da ake gina ta da haramun, imanin cikin zuciyar mai jikin nan ba zai taba habaka ba sai dai ya yi ta ci baya. Haka nan cin haramun shi ke sa zuriyar da aka ciyar da irin wannan dukiya su zama masu bijirewa, marasa albarka. Da fatan Allah Ya ganar da mu ya dora mu a hanya madaidaiciya ko da yaushe.
Tambaya ta 28: Mijina mai yawan karanta jaridunku ne, don haka nake so ku yi rubutu a kan larurata. Muna da yara hudu, amma ba ni da natsuwa ,don haushina maigidana yake ji saboda nonona ya zube. Shi kuma abin da yake tayar masa da sha’awa ke nan a jikin ’ya mace. Don ko bakuwa na yi, ko muna tare a hanya in ya ga mace sai ya kalli kirjinta. Ku ba mu shawara tare da shi don Allah.
Amsa: Ke ai ba ki da wani laifi a cikin wannan ’yar’uwa, me ne ne laifin macen da ta shayar da rai har hudu a dalilin haka har wajen shayarwarta suka nuna alama? Ai kowa ya san cewa sakamakon shayar da yara ga wajen shayarwar mace shi ne zubewarsu. Mata ’yan kalilan ne wadanda suke shayarwa ba tare da wajen shayarwarsu ya canza ba. Don haka sai dai a yi wa maigidanki da duk wani magidanci mai hali irin nasa nasiha:
Ya kai wannan bawan Allah! Mai ya sa kake jin haushin matarka a kan abin da ba ta da laifi a ciki? Ka sani wannan cin fuska ne da wulakanci ga matarka kuma uwar ‘ya’yanka. Kuma babban zalunci ne ka rika nuna mata cewar iyakar darajarta a wajenka shi ne tsayuwar wajen shayarwarta, in haka ne, to da sai ka gindaya sharadi tun wajen daurin aure cewa kai tsayuwar wajen shayarwarta kawai kake son aure ban da ita!
Ka nasihantar da kanka da wannan aya ta cikin Suratul Nisa’i, inda Allah Madaukakin Sarki Ya umarci mazaje da su kyautata zamantakewa da matansu:
“Sa’annan ku yi zamantakewa da su da alheri, idan kun ki su to akwai tsammanin ku ki wani abu alhali Allah ya sa alheri mai yawa a cikinsa”.-S4:A19
Sannan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya yi umarni kada mu’umini namiji ya yi kiyayya ga mu’umina mace; domin in ya tsani wani abu daga gareta dole ya so wani abun.
Wannan dabi’ar da ka dauka tana munana zamantakewarka da iyalinka, don haka ka ji tsoron Allah ka tuba ka bari. Lallai sha’awar wannan halitta ba laifi ba ne kuma ba abin zargi ba ne, amma tuhumarta da hukunta ta a kan laifin da ba ta yi ba shi ne laifi. In ka yi tunani, da ba ka kusance ta ka tsirar da ciki a jikinta ba,da har yanzu tana nan yadda take lokacin da ka dauko ta daga gaban iyayenta. Don haka kai ne babban mai laifi ga zubewar wajen shayarwata ba ita ba!
Sannan kallon kirjin duk macen da ta gifta gabanka babban alkaba’iri ne, kuma ketare iyakokin Allah ne domin ya yi umarni da runtse idanu daga kallon matan da ba muharramai ba. Don haka ka yi kokari ka yaki zuciyarka kuma ka yaki shaidan don ka raba kanka da wannan mummunar dabi’a.
Sai sati na gaba in sha Allah, da fatan Allah Subhanahu Wata’ala Ta’ala Ya sa mu kasance cikin kulawarsa a ko da yaushe, amin.