Tambayoyin Duniyar Ma’aurata (10)

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa a  wannan fili, da fatar Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban amsoshin tambayoyin da masu karatu suka aiko. Tambaya: Malama Nabila don Allah ki isar da sakona zuwa ga ’yan uwa mata wadanda Allah Ya kaddara da shiga gidan […]

Tambayoyin Duniyar Ma’aurata (10)

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa a  wannan fili, da fatar Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban amsoshin tambayoyin da masu karatu suka aiko.

Tambaya:

Malama Nabila don Allah ki isar da sakona zuwa ga ’yan uwa mata wadanda Allah Ya kaddara da shiga gidan aure a matsayin na biyu ko na uku ko na hudu a gidan mazansu cewa su ji tsoron su rika shiga da zuciya daya, su daina shiga da niyyar rusa gidan da suka iske wata matar ta sha wahala ta gina. Su daina shiga da niyyar raba mata da mijinta da raba uba da ’ya’yansa. Sannan maza su rika yin hangen nesa lokacin karin aure, su yi karin aure lokacin matarsu ta fari tana da dan sauran kwarinta, ba sai ta tsufa ta gama haihuwa ba sannan su auro mata ’yar cikinta. Wannan cin fuska ne da cutarwa ga macen da ta sadaukar da karfinta da yarintarta ga mijinta sai daga baya ya butulce mata ya nuna ba a yi da ita. Wannan al’amari ya faru gare ni har yanzu ina cikin tsananin alhinin abin. Mahaifiyarmu ta yi iyakar wahala da mahaifinmu lokacin bai da shi, sai yanzu bayan ta tsufa har ta aurar da ’yar autarta sannan ne Allah Ya yi masa budin arziki sakayyar da ya yi wa mahaifiyarmu ke nan na auren yarinya ’yar cikinsa sannan marar mutunci, ta sa ya rabu da mahaifiyarmu, sannan ’ya’yansa kowanne sai da ta hada su fada wadansu ma har da tsinuwa saboda ita. ’Yan uwansa duk ta hada su fada. Wata rana na je gidan gaida mahaifiyata, amaryar Baba ta yi wa mahaifiyarmu rashin kunya har da zagi da dunguri, ni kuwa na kasa daurewa na yi mata dukan tsiya, a dalilin haka har yanzu mahaifinmu fushi yake yi da ni. Na ba shi hakuri na yi tuba ba adadi amma ya ki hakura, naji an ce wai ita ta ce in dai ya yafe min to za ta bar gidan.

Kafin karin auren ni ce ’yar lelensa duk da kuwa ni ce ta fari amma yana matukar ji da ni, duk shawarwarinsa da ni yake yi, in ya samu kudi ni ke aje masa. In ya shiga damuwa gidan aurena zai same ni ya gaya min ga abin da ke damunsa, in kwantar masa da hankali, ya yi ta sa min albarka wata sa’ar har da kuka. Amma a dalilin karin aure yanzu in na je gida Babana kora ta yake yi ko son ganina bai yi. To mene ne amfanin wannan karin da zai raba mutum da dukkan dangantakarsa ta alheri?

Ina son a yi min bayani kan irin wannan karin auren da wadansu mazan suke yi bayan matarsu ta fari ta manyanta ta gama haihuwa, sannan su auro mata ’yar cikinta kuma sannan su juya mata baya su nuna mata ita an gama yayinta saboda ta tsufa.

Amsa: To irin wannan aure dai ya halatta, matarka ta farko komai yawan shekarunta ya halatta ka hada da wadda ko sa’ar jikarta  ce ba ma ’yyar cikinta ba. Sai dai wajibi ne a cika sharuddan karin aure da ma wasu ka’idojin shari’a na zamantakewa. Daga cikin sharuddan karin aure shi ne adalci, duk wanda ya san ba zai iya adalci ba karin aure bai halatta gare shi, kuma duk wanda ya yi karin aure yake aikata abubuwan rashin adalci, to yana cikin aikin zunubi kuma in ya mutu a wannan hali zai tashi da rabin jikinsa a mace ranar gobe Kiyama.

Sannan yana daga cikin sharuddan karin aure da ma kowane irin aure mutum ya auro ’yar mutunci mai tarbiyya, ’yar kirki kuma musamman mai rikon addini. Haram ne auren mace mai akasin wadannan halaye komai kyau ko irin son da ake yi mata. Sannan tozarta Musulmi wanda ba wata sanayya ko zumuncin da ya gabata, da ci masa mutunci da nuna shi ba a bakin komai yake ba babban kaba’ira ne, ina kuma yin haka ga matar mutum da ya dade tare da ita aka yi ta fadi-tashin rufa wa juna asiri? Haka kuma yana daga cikin hukuncin shari’a saka wa kyautatawa da kyautatawa wacce ta fi ta ko kwatankwacinta, wanda ya aikata akasin haka ya saba wa abin da Allah ke so. Matarka da ta rufa maka asiri lokacin da ba ka da shi yanzu da ka samu ita ya kamata ka fara sakawa, in kuma har ba ka saka mata ba kuwa bai kamata a ce ka kuntata mata ba. Wannan al’amari wata annoba ce ta wannan zamanin, maza kadan ne ke rikon amanar matan da suka yi gwagwarmaya da su. Da fatar Allah Ya shiryar, Ya ganar kuma Ya ba mu ikon aikata ayyuka nagari a koyaushe, amin.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos