Tambayoyin Duniyar Ma’aurata 12

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaba a kan amsoshin tambayoyin da masu karatu suka aiko, da fatan Allah ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa musamman wadanda […]

Tambayoyin Duniyar Ma’aurata 12
Tambayoyin Duniyar Ma’aurata 12

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaba a kan amsoshin tambayoyin da masu karatu suka aiko, da fatan Allah ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa musamman wadanda suka aiko da tambayoyin, amin.

Tambaya ta 28: Yanzu watana biyu da aure Allah ya albarkace ni da samun juna biyu, don Allah ko akwai wasu abubuwa da ya kamata in rika yi ko in kiyaye da za su taimaka min samun da na gari mai albarka,
-Khadija M, Kaduna
Amsa: Ga bayani kan kyawawan abubuwan da ya kamata ko wacce musulma mai dauke da juna biya ta rika aikata wa har zuwa ranar da Allah ya ba ta iko ta sauka lafiya:
-Yabo da godiya ga Allah: Da zarar mace musulma ta fahimci cewa tana dauke da juna biyu, mafi muhimmancin abin da za ta fara yi sh ine yin kyakkyawar godiya ga Ubangijin da ya ba ta wannan kyauta mai matukar girma da daraja. Ta gode masa da kyawawan kalmomi kuma ta kyautata yabo da jinjina gare shi. Ki tuna cewa akwai mata da maza da yawa da suke fama da kuncin rashin haihuwa amma Allah Ya kange ki daga wannan kuncin, don haka lallai ya zama dole yawan nanata godiya ga Allah Subhanahu Wa Ta’ala. Ki rika yawan maimata wadannan addu’o’in na godiya ga Allah Madaukakin Sarki.
Alhamdu lillahil laziy bi ni’imatihi tatimmus salihin
Allahummâ Lakal Hamdû Wa Lakash-Shukru; da sauran kyawawan addu’o’i na nuna godiya da girmama yabo ga Allah madaukakin Sarki.
-Yawan Addu’a: Don samun da nagari mai jinkan iyaye da taimakon addini Islam, sai ki dage da yawan yin addu’oin neman albarka da na tsari daga shaidan ga abin da kike dauke da shi. Ki rika yawaita karatun wadannan addu’o’i:
Rabbi habliy milladunka zurriyatan dayyibatan innaka sami’ud du’a.
Rabbana, hablana min azwajina wa zurriyatina, kurrata a’ayuni waj’alna lil muttakina imama.
Rabbij’alni mukimassalati wa min zurriyatiy, rabbana wa takabbal du’a.
Sannan ki hada da rokon Allah wasu bukatunki game da dan da za ki haifa; kamar ki roki Allah Ya ba ki da hafizin ku’ran, mai jin magana, mai amsar tarbiyya, mai kyawun hali da kyawun halitta, da makamatan haka. Kar ki gajiya da yawan yin addu’o’i, domin kuwa babu arzikin da ya kai na samun yaro na gari wanda zai jikan iyayensa yayin da rauni ya zo masu kuma ya taimaki addinin Allah Mahaliccinsa.
-Kyautata Ibada:Ki dulmiyar da kanki cikin yawan ibada ga Allah Madaukakin Sarki, ki daure komin tsananin yanayin da kike ciki ki rika yin sallolin farilla a farkon lokacinsu kuma ki lazimci yin sallolin nafila ko da raka’a biyu ne kadai a ko wanne dare. Duk cikin sujjadar sallolinki da bayan karatun tahiya a zaman karshe sai ki rika yawan ambaton addu’o’in sauka lafiya da neman albarka ga dan da kike dauke da shi.
Tuba daga aikata miyagun aiyuka: Wannan wani lokaci ne mai matukar muhimmanci a gare ki da ya kamata ki mai da hankalinki gaba daya zuwa ga mahaliccinki Allah Subhanahu Wa Ta’ala. In kuwa har kina ci gaba da aikata aiyukan sabon Allah, to zuciyar ba za ta iya koma wa ga Ubangijinta irin yadda ya kamata ba. Don haka ki daure ki rabu da dukkan aiyukan sabon kamar su gulma, almubazzaranci da kayan masarufi, yawan yawace -yawace, kullatar mutane da rashin yi masu uziri, saurin fushi, jinkirta sallolin farillah, da makamantan haka. Haka kuma ki yi kokarin raba kanki da aiyuka wadadda ba za su haifar da wani alfanu ba a rayuwa, kamar su yawan kallon fina- fina, yawan barci, yawan fita unguwa da sauransu.
Ki sani, kamar yadda danki yake zaune cikin jikinki, yana ci daga abincin da kika ci, in wani ciwo ya shafi jikinki zai shafe shi, to kamar haka ne ruhinki da nasa suke hade a wannan lokacin, duk wani dattin sabon Allah da kika sake ya lullube ruhinki, to wannan dattin zai shafi wannan ruhin yaron da kike dauke da shi a wannan lokacin.
-Yawan Neman Gafara: Ko wanne dan’adam ajizi ne, don samu karin haske da aminci gare ki da abin da kike dauke da shi, sai ki koma ki marairaice ga Ubangijinki, ki nemi gafarar zunubanki, ki yi nadamar munanan aiyukanki kuma ki bar aikata su kuma ki bari ma gaba daya. Kuma ki yawaita yin haka ko da yaushe ba dare ba rana.
-Kula da jikinki: Domin samun ckakkiyar lafiya gare ki da abin da kike dauke da shi, sai ki dage wajen kula da jikinki ta hankayar cin abinci mai kyau da kiyaye tsabtar jiki. Ki guji abinci masu sa kwarnafi irin su yaji da abinci mai tsami ko mai yawan mai sosai a cikinsa. Ki rika yawan cin ganyayyaki da ‘ya’yan itace. Haka kuma ki rika yawan shan madara, nono da ‘yoghurt’ don suna dauke da sinadaran karin lafiya da kuzari gare ki da danki. In kina fama da laulayin yawan amai sai ki rika tafasa danyar citta ki sha kofi daya tun da safe; haka kuma ki rika cin abinci da kadan kadan kar ki ci shi gaba daya ki cika cikin, sai dai ki raba shi kamar kashi biyar, sai wanda kika ci ya zauna sannan ki kara cin wani, domin cika ciki dama na tsokano amai a wannan yanayin kuma sai kin jigata sosai a kan in abincin dan kadan ne kika ci. Haka ma ki rika shan kwayar maganin folic acid da iron duk don karin.lafiya da kariya daga cutuka ga abin da kike dauke da shi. Sannan ki rika cin abinci masu albarka irin su man zaitun da zummuwa.
kulla zumunta da danki: Daga lokacin da ciki ya cika wata uku cif ya shiga na hudu, to a wannan lokacin yaron zai fara jin maganar mutane musamman maganar mai dauke da shi. Don haka a wannan lokaci sai ki fara yin magana ga danki; duk lokacin da kika ji ya yi motsi sai ki ce da shi Allah Ya yi maka albarka, Allah Ya sa ka zama salihin bawa, Allah Ya sa ka zama mai taimakon addinin Allah, da sauran makamantansu. Kuma ki rika yawan karatun ayoyin ku’rani gare shi, ko ki rika kunnawa ko da a waya ne ki kanga ga wajen cikin akai-akai. Sannan ki rika yawan karanta masa aya ta 35 cikin Suratul Ali-Imrana, inda mahaifiyar Nana Maryam (AS) ta sadaukar da abin da ke cikinta don bautar Allah kadai. Ke ma ki yi haka da nufin Allah Ya albarkaci yaronki ya sa ya zama salihin bawa: Rabbi inniy nazartu laka ma fi badani muharraran fatakabbal minniy, innaka antas sami’ul alim.
-Hakuri da Kyautata Halayya: daukar juna biyu babban al’amari mai cike da wahalhalu daban-daban, ban da yanayin canzawar jiki har zuciya da shu’ukanta sukan canza su yamutse ga mafi yawan mata. Don haka sai kin yi hakuri da juriya a ko da yaushe, domin rashin hakurinki zai haifar da wasu matsalolin ne kadai. Sannan ki kasance mai kyautata halayya wajen zamantakewa da mutane, mai saurin yafiya, mai hakuri mai danne fushi. Kar ki yarda ki rika zagi ko fadar miyagun kalamai, domin in kika yi kamar kin sadar da su ne ga danki tun yana ciki kafin ya zo duniya.
Da fatan Allah Ya sa ki sauka lafiya tare da sauran mata musulmi masu dauke da juna biyu.
Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarsa a ko da yaushe, amin.