Tambayoyin Duniyar Ma’aurata (2)
Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaba a kan amsoshin tambayoyin da masu karatu suka aiko. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga masu bukatarsa musamman wadanda suka aiko da tambayoyin, amin.Tamabaya Ta 3: Shekarata hamsin, ina kasa biya wa kaina da matata […]
Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaba a kan amsoshin tambayoyin da masu karatu suka aiko. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga masu bukatarsa musamman wadanda suka aiko da tambayoyin, amin.
Tamabaya Ta 3: Shekarata hamsin, ina kasa biya wa kaina da matata bukata lokacin ibadar aure, sai dai idan na sha maganin kara karfi. Wasu sun ce maganin abin shi ne in kara aure, kun taba fadin cewa mutum ya daina fargaba, to ni na kasa, duk lokacin yin ibadar aure sai in rika jin fargaba; ku taimake ni!
—A.U Pantami.
Amsa: Gaskiya karin aure ba shi ne maganin fargaba ba, sai dai idan ya kasance fargabar da ke damun ka tana daga uwargidan taka ce, misali, a dalilin yanayinta, ko wani abu da take yi ko take fada da suke haifar maka fargaba. Amma idan wani abu ne da ya danganci kai kadai, wanda ba shi da alaka da matar da kake aure, to karin aure ba zai tafiyar da wannan matsalar ba.
Kana iya yin amfani da wadannan dabarun don tafiyar da fargaba lokacin ibadar aure:
• Gab da gabatowar lokacin ibadar auren, sai ka yi alwala, ka yi sallar nafila ra’aka biyu, a cikin sujadarka da wajen zaman tahiya sai ka roki Allah da Ya tafiyar maka da wannan matsala. Sannan bayan ka yi sallama sai ka yi karatun Al’kur’ani maigirma ko da shafi daya ne, amma da sharadin ka karanta shi a hankali, kana mai tauna haruffan da hararo ma’anar kalmomin da kake karantawa. Wannan zai saukar maka da natsuwa cikin zuciyarka, natsuwar da in sha Allah za ta kori fargabar da ke damunka.
• Jan dogon numfashi da ajiye shi kadan-kadan na tafiyar da fargaba da duk wani jin dar-dar da mutum ke ji a lokacin gabatarwar ibadar aure. Don haka sai ka mayar da yin hakan ya zama al’adarka ko da ba lokacin gabatarwar ibadar auren ba ne.
• Idan fargabarka na da alaka da uwargidanka a kan wani abu da take fada ko take yi, to sai ka zauna da ita zama na gaskiya, ka bayyana mata da cewa kazan nan da take yi ko da take fada ga tasirin da yake yi a gare ka, don haka ta ji tsoron Allah ta daina domin karuwar inganci a zamantakewarku.
• Yana da kyau ka je asibiti a yi maka gwaji na musamman ko akwai wata cuta da ke zama sanadin wannan fargaba, domin wasu cutukan, irin su ciwon zuciya da hawan jini, da ciwon suga suna haifar da irin wannan fargaba. Da fatan Allah Ya yaye maka wannan matsala tare da sauran dukkan ‘yan uwa Musulmi masu fama da wata matsala, amin.
Tambaya Ta 4: Ina tambaya ne game da amfani da baki a al’aura: Kun ce wadansu malamai sun ce ba haramun ba ne, sai dai idan maniyyi ko maziyyi ya shiga baki shi ne haram. Shin sai an hadiye ne ko kuma a baki kawai? Domin wadansu sun ce sai an hadiye ne zai zama haram. Don Allah ina son karin bayani.
• —Dahiru Umaru.
• Amsa: Kamar yadda bayani ya gabata cewa wani bangaren na malamai na daukar maniyyi da dangoginsa a matsayin kazanta kawai (watau khaba’ith). Shigar maniyyi da dangoginsa cikin baki haramun ne, domin su din abubuwan kazanta ne, bakin dan Adam kuwa ba wurin sanya abubuwan kazanta ba ne, don haka ba inda shari’a ta amince da shigar abin kazanta cikin baki. Allah SWT Ya haramta mana ci ko shan abubuwan kazanta a cikin Al’kur’ani Mai girma; misali, a cikin Aya ta 157 cikin Suratul A’araf:
• “Kuma Shi (Allah Madaukaki) Ya haramta musu abubuwan kazanta…”
Don haka dole ma’aurata su kiyaye kada wadannan abubuwan kazantar su rika shiga cikin bakinsu har idan ya zamar masu dole sai sun yi haka din. Da fatan Allah Ya ba da ikon kiyayewa, amin.
Zan dakata a nan, sai sati na gaba in sha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koda yaushe, amin.