Tambayoyin Duniyar Ma’aurata (4)

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban amsoshin tambayoyinku. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga masu bukatarsa musamman wadanda suka aiko da wadannan tambayoyi, amin.Tambaya ta 7: Don Allah wane abu ne namiji ya fi so matarsa ta yi masa wanda za […]

Tambayoyin Duniyar Ma’aurata (4)
Tambayoyin Duniyar Ma’aurata (4)

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban amsoshin tambayoyinku. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga masu bukatarsa musamman wadanda suka aiko da wadannan tambayoyi, amin.
Tambaya ta 7: Don Allah wane abu ne namiji ya fi so matarsa ta yi masa wanda za ta nuna masa kauna?
— Maman Abdul.
Amsa: Wannan ya bambanta daga wani mijin zuwa wani: Kowane mutum akwai abin da yake so, wanda ke dadada masa rai daban da na dan uwansa, kamar yadda Hausawa kan ce: abincin wani gubar wani. Don haka mijinki shi ne mafi dacewa da ya sanar da ke abin da ya fi so a yi masa wajen nuna so da kauna. Sai ki tambaye shi ta hanya mafi dacewa; kuma kina iya zama ki yi kyakkyawan nazari game da mijin naki, ki tuna, a tsawon lokacin da kuke tare, wadanne abubuwa ne ya fi so; wadanne ne ba ya so?
Wadanne lokuta ne ya fi kasancewa cikin tsananin farin ciki da jin dadi? Idan kika tuno lokutan da abin da ya sa farin cikin a wannan lokacin, to ta haka ne za ki iya gano abubuwan da ya fi son a yi masa na nuna so da kauna. Da fatan Allah Ya kara so da kauna da amincin juna a cikin rayuwar aurenku da ta sauran dukkan ma’aurata Musulmi, amin.

Tambaya ta 8: Don Allah Anti Nabila ina so ki ba ni addu‘ar neman miji? Na gode kwarai.
— Mai Son Yin Aure.
Amsa: Abin da za ki yi don samun mijin aure shi ne, ki jajirce kuma kodayaushe ki nace da yawan addu’a ba dare ba rana; ki rika kai kukanki ga Allah madaukakin Sarki, ki rika tawassali da sunayenSa Kyawawa, ko da yawan yin Salati Ga Manzon Allah SAW, ko kuma da kyawawan ayyukanki wadanda kika san kin yi dari bisa dari tsakaninki da Allah.
Haka ma yawan yin Sallolin tsayuwar dare, yawan yin azumin nafila, yawan yin kyawawan ayyuka kamar su kyautata wa makwabta, sada zumunci, ziyarar marasa lafiya, duk kyawawan ayyukan da za su kara miki kusanci ga Ubangijinki. Idan kika dage, kika cije, da sannu Allah Zai biya miki bukatunki, domin Yana jin ki, yana kuma sauraren ki, kuma Zai amsa miki addu’arki. Sannan ki kara hadawa da yawan yin wannan addu’ar kodayaushe:
Rabbana, Hablana, min azwajina, wa zurriyatina, kurrata a’ayuni waj’alna lil Muttakina imama.
Da fatan Allah Madaukakin Sarki Ya baki mafi alheri da mafi daukakar abokin zama, tare da sauran dukkanin Musulmi masu irin wannan bukata, amin.

Tamabaya ta 9: Ina da tambaya da neman shawara: A halin yanzu matata daya kuma mun samu shekara 30 da ’ya’ya 10 da jika 1. Kwanan nan zan auro ta biyu da ta 3, shin zan iya sa ranar tarewa ta zamo rana daya; kuma yaya za a yi rabon kwana? Da fatan an fahimce ni kuma za a ba ni shawara, na gode.
— Isa Muhd.
Amsa: Babu laifi idan aka sa ranar tarewar ta zamo rana daya, idan har an yi haka din, to wajen rabon kwana sai a yi kuri’a wacce ta canki daidai ita za a fara ba kwanakin amarci, kwana uku idan zawara ce, bakwai idan budurwa ce. Idan an gama mata sai a ba dayar amaryar kwanakinta. Sannan daga nan a ci gaba da rabon kwana har da uwargida.
Yana da kyau ka yi shawara da duka matan naka ka ji ra’ayinsu kafin daukar wani mataki, domin ya kasance kowaccensu ta yi na’am da shi. Kuma a yi taka tsan-tsan ganin cewa ba a shiga hakkin uwargida ba saboda zakwadin amarci, domin idan matan naka biyu dukkansu ‘yan mata ne, ka ga uwargida za ta yi sati biyu ba ta yi amsar kwana ba ke nan!
To yin haka kuwa akwai shiga hakki a ciki. Don haka Duniyar Ma’aurata na ba ka shawara da ka dan sanya tazara ko da ta sati biyu tsakanin tarewar sabbin amaren naka don kada ka shiga hakkin uwargida da yawa. Da fatan Allah Ya ba ku zaman lafiya da kwanciyar hankali, amin.
Zan dakata a nan, sai sati na gaba in sha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.