Tambayoyin Duniyar Ma’aurata (5)

Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa a cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Don Allah me mutum zai yi idan ba ya iya gamsar da matarsa saboda yawan shekaru? Fahimtar matsala rabi ne na maganin da zai warkar da ita. Don haka kai […]

Tambayoyin Duniyar Ma’aurata (5)
Tambayoyin Duniyar Ma’aurata (5)

Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa a cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukan bayanan da za su zo cikinsa, amin.

Don Allah me mutum zai yi idan ba ya iya gamsar da matarsa saboda yawan shekaru?

Fahimtar matsala rabi ne na maganin da zai warkar da ita. Don haka kai da uwargida ku fahimci cewa kamar yadda yawan shekaru ke canja yanayin jiki, hatta tafiya da sautin amon murya sukan canja saboda yawan shekaru, to haka ma yawan shekaru ke canja bangaren sha’awa da ibadar aure. Yawan shekaru na haifar da sanyin sha’awar ita kanta da sanyin gaba da saurin inzali da kuma sanyin gamsuwar ibadar aure, abin da a lokacin samartaka ake jin su wuta-wuta sai su koma garwashi ko ma toka-toka saboda gabatowar shekaru. In ya kasance ita uwargida da sauran yarinta a tare da ita shi ya sa ake samun wannan matsala, sai ta fahimci cewa haka yanayin yawan shekaru ya zo ga maigidanta, don haka ta sa hakuri da dangana a zuciya, don yawan damuwa da bayyana damuwar ba zai haifar da komai ba sai dai ya kara dagula matsalar. Musamman in ta tuna cewa akwai da yawa matan da suke auren matasa kuma suna fama da matsalar rashin samun gamsuwar.

Duk da cewa yanayin dan Adam ne raguwar karfin sha’awa lokacin tsufa, akwai wasu abubuwa da suke kara assasa tasirin haka:

Yawancin abin da ke haifar da matsalolin sha’awa ga dattijai shi ne raunin jijiyoyin jiki  musamman jijiyoyin al’aura. Don haka sai a dage da yawa wajen motsa jiki a kai-a kai. Hanya mai sauki ita ce a yi tafiya a kasa ta tsawon minti 30 kullum, sannan a rika yin samfurin motsa jijiyoyin al’aura wato kegel. Lallai wannan yana tasiri sosai wajen kara karfin sha’awa da rage aukuwar sanyin gaba ga dattijai.

Gabatowar shekaru na iya haifar da karancin sinadaran sha’awa cikin jini, binciken likita zai bayyanar da haka, in har hakan ta tabbata akwai kwayoyi da likita zai rubuta don samun karuwar sinadaran sha’awar.

Akwai wasu cututtuka da yawan shekaru ke assasa motsuwarsu kuma sukan yi tasiri kwarai ga ma’aikatar sha’awa, musamman ciwon suga na shafar jijiyoyin al’aura. Sannan magungunan wasu cututtuka musamman hawan jini da ciwon suga suna haifar da sanyin gaba, a irin wannan sai  a yi aiki da umarnin likita.

 

Ina fama da karancin maniyyi da rashin karfin gaba, da fatan za a ba ni shawara.

Abin da ka iya haifar da raunin gaba da karancin maniyyi ya hada da:

Gabatowar shekaru na daga cikin abubuwan da ke haifar da rashin karfin gaba da rashin ruwan maniyya. Don haka in har an fara tara shekaru haka ya faru, to wannan haka tsarin al’adar jikin dan Adam yake. Amma in babu yawan shekaru, to abubuwa daban-daban ne ke haifar da haka da suka hada da:

Karancin sinadaran sha’awa cikin jini, musamman in haka na faruwa hade da wasu cututtuka kamar yawan gajiya, sanyin sha’awa da tsotsewar gaba da maraina. Sannan ciwon suga na haifar da raunin jijiyoyin jiki duka kuma yana iya sa hanyar fitar maniyyi ta toshe, maniyyin ya koma cikin mafitsara maimakon ya fito waje.

  • Cutar gwaiwa ma na iya haifar da karancin maniyyi da raunin gaba musamman wacce aka yi wa fida ko sakiya
  • Haka nan shan magungunan hawan jini na iya haifar da wannan matsala don haka shawara ita ce a daure a yi wa likita bayani domin wannan matsala ce da take da sabubba daban-daban a likitance, binciken likita ne kadai zai bayyanar da musabbabinta da samar da maganin da ya dace.
  • Yawan cin kayan marmari, magungunan Musulunci, yawan cin kwadon ganyayyaki da kuma yawan cin farfesun kaza, farfesun naman shanu ko na rago da kuma romon auren ’yan shila na iya farfado ko kara karfin sha’awar da yawan shekaru ya sa ta lafa.

 

Duk in lokacin sanyi ya zo gabana sai ya rika tsatstsagewa kamar kauje a kafa da sanyi ya wuce sai ciwon ya mutu, to ko wane irin ciwo ne wannan, sannan mene ne maganinsa?

In dai lokacin sanyi kadai hakan ke faruwa, to wannan na nuna cewa akwai matsalar rashin isasshiyar lema a jiki, yanayin hunturu kuma na tsotse dukan lemar da cikin sarari da kuma lemar fatar jikin dan Adam. Abubuwan da za su taimaka don samun saukin wannan matsala sun hada da:

  • A riki kula da fata a koyaushe ta hanyar tsabta da shafe dukan jiki da mai ba sai lokacin hunturu kadai ba.
  • A rika sa gyauto na maza (wato pant ko dan duros na maza a ciki kafin a sa wando wannan zai ba da karin kariya daga busarwar da hunturu ke kawowa.
  • Yawan shan ruwa na kara yawan lema a jiki, yawan shayi ko naskafe kuma na rage lemar jiki don haka sai a kiyaye.
  • Haka nan yawan cin kayan zaki na rage lafiyar fatar jiki wanda hakan zai yi tasiri ga karancin man da fata ke sarrafawa don hana bushewa.
  • A guji yin wanka da ruwan sanyi domin hakan na busar da jiki, in ya zama dole a rika kashe zafi kadai.
  • Man kade na maganin bushewa da kaujen fata musamman in aka riki al’adar shafa shi sau biyu kullum, safe da yamma.

Sai mako na gaba insha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos