Tambayoyin Duniyar Ma’aurata (6)

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa a cikin wannan fili da fatan Allah Ya amfanar da mu dukan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban amsoshin tambayoyinku da fatan Allah Ya isar da wannan bayani ga duk masu bukatarsa, amin. Ina son a yi mini bayani a kan illar kodin a kan […]

Tambayoyin Duniyar Ma’aurata (6)
Tambayoyin Duniyar Ma’aurata (6)

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa a cikin wannan fili da fatan Allah Ya amfanar da mu dukan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban amsoshin tambayoyinku da fatan Allah Ya isar da wannan bayani ga duk masu bukatarsa, amin.

Ina son a yi mini bayani a kan illar kodin a kan karfin mazakuta, saboda na ji an ce yana kashe gaban maza, musamman mu matasa da ba mu yi aure ba. Da yawanmu mun kasance muna shan kodin wato totalin, don Allah a wayar mana da kai.

-Daga Shamsu Gusau.

 

Amsa:

Kodin (Codeine) na daya daga cikin sinadaran da ake kira da opiates, tasirinsu ga jikin dan Adam shi ne kashe radadi da saukar da laulayin jiki irin na barci. In kuma aka sha fiye da ka’ida yakan sanya jin dadin rai da natsuwa da kwanciyar zuciya irin na maye. Yawan shan wannan magani a matsayin kwaya na lahani ga manyan gabobin jiki musamman hanta da koda da madaciya (pancreas) da kuma zuciya. Haka yana taba ma’aikatar hankali ta hanyar haifar da cututtukan halayya musamman tsananin huzni da sauran cututtuka da ke tattare da shi. Haka kuma yana bugarwa sosai da sa dogon suma da fisge-fisge. Kuma yana sa raunin jijiyoyin jiki da kuma tauyewar jijiyoyin. Kuma tabbas yana haifar da sanyin gaba mai wuyar warkarwa domin tasirin ya samo asali ne daga gaba daya. Illar da yawan shan ya haifar ga ilahirin jikin dan Adam haka kuma yana kashe ma’aikatar sha’awa gaba daya ta daina motsawa. Kuma yana lalata dangantakar mai shanta a matsayin kwaya da makusantansa. Wannan kadan ne daga cikin illar da wannan kwaya take yi ga jikin dan Adam da kuma zamantakewarsa a cikin al’umma. Wannan bayani kadai ya isa ya sa matasa su yi nazari su karfafa niyya su guji wannan kwaya tun kafin ta hallaka musu rayuwarsu ta duniya baki daya; koda yake wannan mai sauki ne in aka kwatanta da sakamakon da mutum zai tarar Ranar Alkiyama, domin ku sani ya ku matasa da sauran masu fama da irin wannan lalura! Kasancewar kodin magani ne ba shi ke sa ya zamana mayar da shi kwaya na halal ba, ku sani shan kodin ba bisa ka’ida ba zunubinsa daidai yake da shan giya. Dukansu kayan maye ne kuma dukansu mayen suke sawa, dukansu alfasha ne kuma ayyukan fasikanci, kuma tabbas in mutum ya mutu a haka ba tare da ya yi kyakykyawar tuba ba, to sakamakonsa daidai ne da wanda ya mutu a cikin mayen giya ba tare da ya tuba ba. Don haka Malam Shamsu kai da sauran matasa, damuwarku ta tafi a kan kuna fama da lalurar aikata sabon Allah, ku zama masu yawan tuba da neman taimakon Allah Ya raba ku da wannan fitina, domin illarta ba ga jikinku kadai ba ne, ba ga duniyarku kadai ba ne, illarta sai na iya hana muku kyakykyawan rabon gobe Kiyama. Da fatan Allah Ya warkar da dukan masu fama da wannan lalura kuma Allah Ya yaye dukan damuwa daga zukatan bayinSa, amin.

Don Allah Malama ki yi jan hankali da nasiha ga mata, domin akwai wata dabi’a da suke yayi yanzu na idan sun hau A Daidata Sahu sai su yaye mayafansu daga kirjinsu kuma na lura har matan aure suna yin haka, sannan ga mata masu leke su ma abin dada ta’azzara yake, muna rokon Allah Ya sa mu gyara halayenmu gaba daya, amin.

-Daga Sunusu Sani Dala.

Amsa:

Nasihar duniyar ma’aurata ga ’yan uwa mata da suke fama da wannan rauni shi ne, ku tuna cewa Allah Mai girman Jalala da karamci Shi ne Ya umarce ku ku rufe dukan jikinku daga ganin duk wani namiji da ba muharraminku ba. Ku tuna cewa keken A Daidaita Sahu a titi yake, kowa zai iya ganin gabobin jikinku, wani in ya gani ma ya ji dadi ya yi sha’awa, in mai mugun ido ne ma kallonsa ya haifar muku da mummunan tasiri. Sannan ku sani ba mu kadai ke rayuwa a wannan duniya ba, akwai aljannu cikinmu kewaye da mu zagaye da mu, rufe jikinku gaba daya shi ne babban kariyarku daga idanuwan wadanda ba ku ganinsu amma su suna ganinku. Kasancewa cikin keken A Daidaita Sahu ba kamar  kasancewa a cikin gida ba ne, don haka ku tuna tsoron da kuke yi wa Allah Madaukakin Sarki, ku tuna  girmanSa da kuke gani ku tuna girman azabarSa da radadinta, ku tuna hucin Jahannama da hadamarta, ku sabunta imaninku.Ku tuba ku daina ku yake shi ku tsare mutuncinku ta hanyar sanya isasshiya kuma cikakkiyar sutura. Nana Fadima ’Yar Manzon Allah (SAW) Radiyallahu Anha, tana cewa mafiya daraja daga cikin mata su ne wadanda ba su ganin maza kuma maza ba su ganinsu. Sannan Allah Ya yi kira ga dukan matan Musulmi su tabbata a cikin gidajensu su daina yawan fita irin ta gaye-gaye, fitar Jahiliyya. Da fatan Allah Ya ba mu ikon yin aiki da umarninSa da kiyayewa ga haninSa, Amin.

Sai mako na gaba insha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.