Tambayoyin Duniyar Ma’aurata 8
Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo a cikinsa, amin. Ga ci gaba da amsoshin tambayoyin da ma su karatu suka aiko, da fatan Allah ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa musamman […]
Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo a cikinsa, amin. Ga ci gaba da amsoshin tambayoyin da ma su karatu suka aiko, da fatan Allah ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa musamman wadanda suka aiko da tambayoyin, amin.
Tamabaya ta 20: Ina neman shawara ne game da zaman auren da nake yi da mijina. Shi ya kasance yana matukar so na, kuma ni ba na son shi, na yi hakurin aurensa ne kawai don yin biyayya ga iyayena da kuma zaton kila in muka yi aure in ji ina son shi, amma har yanzu na ka sa son shi. Yanzu abin da yake damu na shi ne ina da wanda nake so kafin in aure shi kuma yanzu har waya yake mini; ina cikin wani hali na rasa yadda zan yi don ba damar in gaya wa iyayena ba na son shi, don ba na son in bata masu rai. Shi kuma mijina ba na son in gaya masa mu rabu don yana ba ni tausayi kuma ba na son shi.
Amsa: Ga shawarwarin duniyar ma’aurata gare ki game da wannan matsala:
Amsa:
1. Shawara ta farko ita ce: Ki ci gaba da yin biyayya ga iyayenki kamar yadda kika faro, ki daure, komai tsanani kar ki gaza domin biyayya ga iyaye babbar ibada ce wacce a dalilinta kadai sai Allah Ya jikanki ya fitar da ke daga cikin mawuyacin halin da kike ciki.
2. Shawara ta biyu ita ce: Ki ci gaba da zama da maigidanki da kyautatawa da kuma tausaya masa saboda Allah, domin duk wanda ya sadaukar da farin cikinsa don faranta wa wani ko ya tausaya wa wani shi ma ana sa ran Allah zai faranta masa kuma Ya tausaya masa. Ki sani cewa, tausayi daya ne daga cikin sinadaran jin dadin zamantakewar aure, tun da kuwa har kina jin tausayinsa, a hankali wataran za ki wayi gari soyayyarsa ta cika zuciyarki cikin yardar Allah.
3. Shi kuma tsohon masoyinki, ki yanke dukkan wata hulda tsakaninki da shi, ki sani ci gaba da amsa wayarsa da kike yi sabon Allah ne; don haka ki tuna girman hakkin Allah a kanki, ki tuba ki bari gaba daya. Shi kuma tsohon masoyinki in har musulmin kirki ne shi, to shi ma ya kamata ya tuba daga wannan aikin sabon na kiran matar wani yana hira da ita, domin duk musulmin kirki ba ya shiga gonar da ba tasa ba, kuma duk musulmin kirki yana kiyaye hakkin dan’uwansa musulmi; kamar yadda ya san ba zai so wani mutum ya rika buga wa matarsa waya ba da sunan yana son ta, haka nan shi ma bai kamata ya rika buga wa matar wani ba ko domin ya gaishe ta ne. In shi masoyin hakika ne to ba irin alherin da zai maki da ya wuce ya kyaleki ki yi ibadar aurenki cikin kwanciyar hankali da natsuwa; hakan kuwa bai samuwa in yana yawan buga maki waya yana tuno maki abin da ya kamata ace kin manta da shi kin ba shi baya.
4. Shawara ta hudu ita ce: Ki sani wannan wata jarrabawa ce daga Allah Ubangijin halittu zuwa gare ki. Allah yana jarraba bayinsa ta hanyoyi daban-daban, domin auna nauyin imaninsu da karfin rikon biyayyarsu ga Allah, wanda ya yi hakuri shi zai dace da dadi kala uku, ladan hakuri, ladan cin jarrabawa da alhairan da za su biyo bayan cin jarrabawa, watau shi ne sauki biyun da ke tattare da duk wani tsanani daya kamar yadda ya zo a ayoyin Suratul Sharh. Don haka ki yi hakuri mai kyau, har zuwa lokacin da Allah zai yaye maki wannan matsala.
5. Bayan kyakykyawan hakuri sai kuma ki nace da yawan addu’a tare da sakankancewa a ranki lallai Allah zai amsa maki addu’arki; ki yawaita yin Sallar neman zabin Allah da Sallolin tsayuwar dare, da nufin Allah Ya kawo maki mafitar wannan mawuyacin halin da kike ciki. Kyakkyawan hakuri da nacin addu’a su ne manyan maganin ko wacce irin matsala ta rayuwa.
Tambaya Ta 24: Don Allah shawara nake nema, ina karatu a Kwalejin Ilmi amma mijina ya ki bari na in ci gaba da karatun, na yanke shawarar kawai mu rabu in ci gaba da karatuna. Don Allah ku ba ni shawara.
Daga Aisha.
Amsa:
1. Babban kuskure ne za ki tabka a rayuwarki in kika ce za ki kashe aurenki a dalilin karatun boko kadai, in dama ace karatun ilmin yadda za ki bauta wa Ubangijinki ne maigidanki ya hana ki, to a nan kina da hujja na ki rabu da shi don ki nemi ilmi. Ki sani, aure babbar ibada ce mai tsananin muhimmanci a rayuwar musulmi, ya wuce a kashe shi kawai don neman ilmin boko, wanda amfaninsa kadai shi ne ki sami aikin da za a rika biyanki albashi a dalilinsa. In kika yi hakuri sai ki ga Allah Ya musanya wannan hakurin da wani alherin da ya fi ilmin boko nesa ba kusa ba. Don haka ki yi hakuri, ki yi ladabi da biyayya ga maigidanki, ki zauna a gidansa ki ci gaba da bautar aure, domin mafi alherin wurin zama ga ’ya mace shi ne gidan mijinta, kuma mafi kololuwar matsayi a gare ta shi ne ta zamo salihar uwa ga ’ya’yanta kuma salihar mata ga mijinta.
2. Ki nace da yin Sallar neman zabin Allah da nufin Allah Ya zaba maki abin da ya fi alheri gare ki duniya da lahira, ki kuma nace da yin addu’a in da alheri a cikin karatunki, to Allah ya tausasa zuciyar mijinki ya bar ki ki ci gaba da karatunki.
3. In har wannan hani da maigidanki ya yi maki ya bata maki rai har ya sa kina jin haushinsa, to ki tausashi zuciyarki, ki yafe masa kuma kar ki rika nuna masa kina jin haushinsa saboda abin da ya yi maki. Ki ci gaba da kyautata masa da kula da shi, kila hakan da za ki yi ya karkato da zuciyarsa zuwa ga bukatarki.
4. Sannan kina iya sanar da magabatanki ki ji irin shawarar da za su ba ki.
Sai sati na gaba in sha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarsa a ko da yaushe, amin.