Tambayoyin Duniyar Ma’aurata 9

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaba da bayani a kan amsoshin tambayoyin da masu karatu suka aiko, da fatan Allah ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa […]

Tambayoyin Duniyar Ma’aurata 9
Tambayoyin Duniyar Ma’aurata 9

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaba da bayani a kan amsoshin tambayoyin da masu karatu suka aiko, da fatan Allah ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa musamman wadanda suka aiko da tambayoyin, amin.

Tambaya Ta 22: Anti Nabila na kasance mai zinar hannu kafin aure, yanzu ga shi na yi aure kimanin shekara biyu ke nan matata bata sami juna biyu ba; shin hakan yana da nasaba da abin da na aikata kafin in yi aure?

F.A.Y Yakasai.
Amsa: Ko kadan wannan ba shi da nasaba da wancan abu da ka aikata kafin aure, matukar kuna gabatar da ibadar aurenku ba tare da wata matsala ba, wancan abu da ka aikata ba ya hana daukar ciki, sai dai in Allah bai kawo lokacin ba ko kuma akwai wata matsala daban.
Tambaya Ta 23: Ko ya halatta maigida ya tsotsi wajen shayarwar matarsa idan tana goyo, kuma yin hakan ba zai haifar masa da wani abu ba?
Maryam Katsina.
Amsa: Shan ruwan nonon uwargida ga maigida makaruhi ne, amma in ya sha din to hakan ba zai haifar masa da komai ba.
Tamabaya Ta 24: Na karanta bayanin da kuka yi a kan hakkin maye, tambayata ita ce ya hallata ka rubuta wata sura ta alkur’ani kamar a ce ka rubuta Suratul Yusuf, duk karshen aya a rubuta sunan miji a wanke da ruwan kankana a sha? Shin har su tukudi da kayan marmari ma bai halatta mu ci ba don karin ni’ima?
Amsa: Duk wani abinci da kayan marmari ya halatta a sha ko a ci matukar ba za su haifar da wata barazana ga lafiya ba. Amma sanya sunan miji cikin rubutu ya so ya yi yanayi da tsibbu kuma ya fita daga koyarwar addinin Islama , Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam bai koyar da wani abu makamancin wannan ba ,haka kuma Sahabbansa masu daraja; hanya daya ta more zakin addini da dacewa ranar gobe kiyama ita ce hanyar yin addini kamar yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya koyar da shi. Amma ana iya karanta ita Suratul Yusuf din, ko wani bangare daga cikin Al-kurani mai girma cikin natsuwa da mai da hankali gaba daya wajen karatun da sauraren sakonnin da ke cikin ayoyin; ta yadda mutum zai ji dadi da gardin karatun na ratsa jikinsa; bayan an kammala sai a roki Allah dukkan bukatun ko gyaran da ake so game da miji ta hanyar yin tawassuli da wannan karatu da aka yi; in sha Allah za a samu biyan bukata, domin shi al-kur’ani waraka ce da kuma rahama ga dukkan musulmai.
Tambaya ta 25: Na karanta makalarki mai taken “Raba daidan lokaci.” Don Allah ina matsayin mazajen da ke tafiya da daya ko biyu daga cikin matansu su zauna da su a birni, alhali sun bar dayar ko sauran a kauye ba tare da neman yardarsu ba?
Amsa: Matsayin irin wadannan mazaje shi ne su ba adalan maza ba ne, domin ba su zartar da adalci a tsakanin matansu ba kamar yadda Allah Madaukakin Sarki Ya umarce su da yi. Kamar yadda bayani ya gabata a wannan fili cewa koyarwar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam a yayin da irin haka ta kama maigidan da yake da mata sama da daya shi ne yin kuri’a, duk wadda ta canki dai-dai to da ita za a yi wannan tafiyar. Don haka wannan ba zabin maigida ba ne, zabin Allah ne ta hanyar yin kuri’a. Sai dai in maigida ya nemi izinin sauran mata suka amince masa da ya zabi wadda zai tafi da ita, ko su da kansu suka ce mun amince ka tafi da wance. Ko su matan da kansu suka zabi su zauna a kauyen saboda wani dalili nasu. Saboda haka, maza masu aikata irin wannan rashin adalci su ji tsoron Allah Subhanahu Wata’ala su tuba su bari, su nasihantar da kansu da hadisin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam wanda ya bayyana cewa mazan da ba su zartar da adalci a tsakanin matansu ba, to ranar kiyama za a tashe su da barin jikinsu a shanye. Da fatan Allah Ya ganar da mu kura-kurenmu kuma ya ba mu ikon gyarasu, amin.
Tambaya ta 26: Neman shawara da taimako: Ni mijina yana kuka da ni a kan in yana tare da ni ba na taya shi da komai wajen ibadar aure, wannan yana kawo mana yawan sabani; a taimaka min da shawara, na gode.
Amsa: Tun da har kin san matsalar da ke kawo maku sabani, kuma abin yana damunki, to ai sai ki dage ki yi maganin matsalar ta hanyar yin irin abubuwan da kika lura yana son ki yi masa in kuna tare. In kuma akwai wani abu da yake hana ki taimaka masa din, kamar tsananin kunya, sai ki yi kokarin kawar da ita. Ki fara kokarin taimaka masa din da kadan-kadan, da haka har ki saba, yin hakan ya zame maki jiki. Da fatan Allah Ya yaye wa dukkan ma’aurata matsalolin auratayyarsu , amin.
Sai mako na gaba in sha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance a cikin kulawarsa ko da yaushe, amin.