Tambayyoyi daban-daban

Me yake kawowa a haifi wasu jarirai da wani ciwo a baya kamar doro? Daga Garba Adamu, Azare Amsa: Tangardar halittar jaririn ake samu a ciki. Mafi yawan lokuta akan samu dalilan tangardar ce daga iyaye. Walau shi kwayoyin halittun mahaifin suna da rauni ko kuma ita uwar nata kwayoyin kwayayen suna da matsala. Wasu […]

Tambayyoyi daban-daban
Tambayyoyi daban-daban

Me yake kawowa a haifi wasu jarirai da wani ciwo a baya kamar doro?

Daga Garba Adamu, Azare

Amsa: Tangardar halittar jaririn ake samu a ciki. Mafi yawan lokuta akan samu dalilan tangardar ce daga iyaye. Walau shi kwayoyin halittun mahaifin suna da rauni ko kuma ita uwar nata kwayoyin kwayayen suna da matsala. Wasu lokuta kuma dukkansu biyu lafiyayyu ne, kawai sai a samu matar ta sha wasu magunguna da za su jirkita halittar jaririn, kamar wasu magungunan asibiti ko na gargajiya. A cikin magungunan asibiti wadanda aka san suna iya sa irin wadannan jirkita halittun jariri akwai magungunan farfadiya.

Haka a daya hannun kuma rashin shan wasu magunguna ga mai juna biyu, irin su bitamin din folic acid da ake bayarwa wurin awo, shi ma na iya sa wa jariri tangarda ya samar da irin wannan ciwo mai kamar doro. Sai dai a lokuta da dama ana iya tiyata a gyara matsalar in dai ba ta shafi lakar gadon baya ba.

 

Me ya sa wadansu yara sukan yi bakon-dauro duk da cewa an yi musu allurar riga-kafin ciwon?

Daga Shehu M.K

Amsa: Zai iya zama dalilin bambancin karfin garkuwar jiki ne. Wadansu yaran da an musu wannan allurar shi ke nan har abada jikinsu ya samu tsaro, wadansu kuma sai an maimaita (shi ya sa ma kake ganin a mafi yawan lokuta a yanzu sabon tsarin shi ne sai an maimaitata a shekara daya da rabi bayan an yi a wata na tara)

Duk da haka dai in dai aka yi wa yaro allurar, ko ya zo daga baya ya samu ciwon ba zai yi zafin ko karfi kamar a wanda ba a yi masa ba.

Wani lokaci kuma ba ma bakon-dauron ba ne. Wadansu yara na yin ciwon farankama mai kama da bakon-dauro, sai a dauka bakon-dauro ne.

 

Ni ce ina da juna biyu sai na je asibiti aka ba ni magani wanda idan na sha sai in rika tsuma ina zufa numfashina na sama-sama.

Daga Mai neman shawara

Amsa: To shawara a nan ita ce ki tsayar da maganin kada ki kara shan sa, ki koma da shi asibitin a canJa miki wani a madadinsa. Watakila maganin bai karbe ki ba ne, abin da muke kira side-effect. Irin wannan matsala ba sai da juna biyu wasu magunguna suke jawo haka ba, ko da juna biyu, ko babu, idan magani bai karbi mutum ba da ya sha zai fara jin wasu sababbin alamu na wata irin rashin lafiya ta daban, kamar irin yadda kika ji, amma da an daina amfani da maganin yawanci alamomin ke tafiya.

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna