Tambayyoyi daban-daban

Ni idan ina wanka na kankare fatata sai in rika ganin wani abu. Ko wannan matsala ce? Daga Khadija Randawa Amsa: E, zai iya zama matsala kwarai da gaske duk da cewa baki fadi abinda ki ke gani idan ki ka kankari fatar ba. Yawanci a karkashin fata akwai wani mayani fari da mukan kira […]

Tambayyoyi daban-daban
Tambayyoyi daban-daban

Ni idan ina wanka na kankare fatata sai in rika ganin wani abu. Ko wannan matsala ce?

Daga Khadija Randawa

Amsa: E, zai iya zama matsala kwarai da gaske duk da cewa baki fadi abinda ki ke gani idan ki ka kankari fatar ba. Yawanci a karkashin fata akwai wani mayani fari da mukan kira fascia wanda ya ke tsakanin fata da tsoka,sai an kai ga ganin shi kafin a kai ga ganin tsoka da jini, watakila shi ki ka kankaro. Ki dai yi a hankali. Mun san mata akwai su da son ado da shanawa amma a tashin farko ba mace ce ita kadai za ta zauna a gida tana kankarar fatarta domin ta yi kyau ba. Kamata ya yi alal akalla ta fara zuwa wurin kwararriyar mai gyaran jiki ta yi mata aikin gyaran jiki gaba daya, ta kuma nuna mata yadda ake yi.Wannan shi ya fi inganta. Domin su masu gyaran jikin suna da kayan aiki na musamman kamar sabulai da mayuka irin wadanda ke iya fitar da fata,wato watakila ma ba su da soson dirje fata balle a karce ta. Sana’a ce da ta samo asali a kasashen Arewacin Afirka irinsu Masar da Maroko.

A likitance ma mu muna ganin cewa ita fata da kanta take gyara kanta,domin duk bayan ‘yan satuttuka (sati uku zuwa hudu) sai fatar jiki ta sabe wata sabuwa ta fito, wankan da muke da ruwa da sabulu da soso kawai wanke abin da ya sabe a ke. Shi ya sa a wasu lokuta ko da ba a amfani da kayan shafe-shafe za a ga fata yau ta yi duhu-duhu bayan kwanaki ta dan yi haske idan sabuwa ta tofo.

To idan mace na yin wannan gyaran (wanda kusan ake yi wata-wata) za a ga an tsallake lokutan da fatar za ta yi duhu saboda gyaran ya wanke sabar, ba da kanta ta sabe ba.Ai irin wannan shi ne kan sa a ga mutum idan ya samu canjin rayuwa misali daga wahala zuwa dadi ba wani gidan gyaran jiki zai je a yi masa gyaran fata ba, amma kawai za a ga fatarsa na canzawa daga mai duhu zuwa mai sheki, saboda kawai canjin abinci da abin sha da sabulu da man shafawa da rashin shiga rana. Daga ranar da canjin rayuwar ya kare idan aka dawo shiga rana da raguwar cimaka mai karko za a ga ta sake canzawa.

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna