Tambuwal ya ba iyalan sojan da ya mutu a kullen COVID-19 tallafin N1m

Birgediya Gara ya ba wa iyalan mamacin tabbaci a kan biyansu hakkokin sojan da ya riga mu gidan gaskiya.

Tambuwal ya ba iyalan sojan da ya mutu a kullen COVID-19 tallafin N1m

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Aminu Tambuwal tare da Babban Hafsan Sojojin sama, Sadique Abubakar

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sakkwato, ya ba da gudunmuwar Naira miliyan daya ga iyalan sojan da ya rasa rayuwarsa yayin tabbatar da an kiyaye dokar kullen coronavirus a watannin baya.

Kofur Isma’ila Ishiaku, na Bataliya ta 26 ta Rundunar Sojin Kasa ya rasu ne a wani hatsarin mota da ya auku ranar 18 ga watan Afrilun 2020 a kan titin Bodinga zuwa Tambuwal.

Yayin gabatar da kudin ga matar marigayin, Kwamandan Rundunar Soji ta 8, Birgediya Moses Gara, ya bayyana mamacin a matsayin soja mai kwazo da jajircewa a kan aiki.

A cewarsa, ba a taba samun marigayin sojan ba da wani laifi yayin sauke nauyin da ya rataya a wuyansa.

Ya nemi iyalan mamacin su dau dangana tare da fadakar da su a kan neman aminci da sauki a wurin Mai Duka.

Birgediya Gara ya ba wa iyalan mamacin tabbacin biyan su hakkokin sojan da ya riga mu gidan gaskiya.

Uwargidan mamacin, Patient Ishiaku, ta yi godiya ga Gwamna Tambuwal a kan togamashi da kyakkyawan karamci da ya yi musu.

Mahaifinmu ba shi da ciwon suga – Ɗan Janar Rabe

Sojoji sun daƙile harin Boko Haram, sun ceto mutum 9 a Borno

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo