Tambuwal ya ba manoma tabbacin tsaro
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sokoto ya bukaci manoma a yankunan da hare-haren ‘yan bindiga suka addaba da su koma gona, tare da ba su tabbacin tsaro. Tambuwal ya kirayi mazauna yankunan da su yi hakuri da ayyukan sojin da ke gudana a yankunan, yana mai cewa Gwamnatinsa da ta Tarayya na yin dukkan […]
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sokoto ya bukaci manoma a yankunan da hare-haren ‘yan bindiga suka addaba da su koma gona, tare da ba su tabbacin tsaro.
Tambuwal ya kirayi mazauna yankunan da su yi hakuri da ayyukan sojin da ke gudana a yankunan, yana mai cewa Gwamnatinsa da ta Tarayya na yin dukkan mai yiwuwa domin samar da tsaro a jihar.
“Akwai takura amma ina tabbatar muku cewa karuwarmu ce gaba daya.
“Ba za mu yi sake a hana manomanmu noma ba, daga baya mu zo muna fama da karancin abinci”, inji gwamnan.
Ya ce gwamnatin jihar ta samar wa manoma takin zamani da sauran kayan noma domin samun amfani a daminar bana.
A sakonsa na Babbar Sallah, gwamnan ya hori Musulman jihar da su kiyaye matakan kariyar cutar coronavirus a koyaushe, sannnan su yi addu’ar samun sauki ga wadanda suka kamu.
Ya yaba wa jami’an lafiya da kwamitin yaki da cutar a jihar bisa sadaukar da kansu wajen wayar da jama’a da kuma kula da masu cutar.
“Wajibi ne mu ci gaba da wayar da kai a game da wannan cutar, domin har yanzu tana nan kuma sai mun yi hattara”, inji shi.
Ya roki Allah Ya amsa ibada, Ya yafe kurakuran bayinSa, Ya shiryar da su ga hanya madaidaiciya.