Tambuwal ya kalubalanci Musulmi kan hadin kai

Shugaban Majalisar Wakilai ta Tarayya Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya bukaci al’ummar Musulmin Najeriya da na duniya su hada kai don tunkarar kalubalen da addinin Musulunci yake fuskanta  a  duniya. Alhaji Aminu Tambuwal ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wurin kaddamar da gidauniyar raya ilimi ta Naira biliyan 2.3 da kungiyar […]

Tambuwal ya kalubalanci Musulmi kan hadin kai

Shugaban Majalisar Wakilai ta Tarayya Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya bukaci al’ummar Musulmin Najeriya da na duniya su hada kai don tunkarar kalubalen da addinin Musulunci yake fuskanta  a  duniya.
Alhaji Aminu Tambuwal ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wurin kaddamar da gidauniyar raya ilimi ta Naira biliyan 2.3 da kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa ta gudanar a Dandalin Eagle Skuare, da ke Abuja a ranar Lahadin da ta gabata.
Ya ce “ya  kamata mu fahimmci wannan al’amari, mu takaita abubuwan da suke kawo mana sabani a tsakaninmu, don mu tabbatar da mun kafa jagoranci na kwarai a tsakaninmu mu samu ci gabanmu da na addininmu.
Ya ce sabanin da ke faruwa a tsakanin majalisarsu da bangaren zartarwa ba sabani ne na son zuciya ba. “Mu ’yan Majalisar Tarayya an zabe mu ne a matsayin wakilan jama’a domin mu zo mu tabbatar da cewa bangaren zartarwa na gudanar da abubuwan da suke da amfani ga al’ummar Najeriya,” inji shi. Ya ce duk abubuwan da suke yi a majalisar suna yin su ne domin a samu zaman lafiya da ci gaba a Najeriya.
Sai ya yaba wa kungiyar kan ayyukan da ta sanya a gaba tun daga kafa ta musamman kokarin jawo hankalin al’umma kan rungumar ayyukan alheri.
A jawabin Gwamnan Jihar Neja kuma Shugaban Majalisar Gwamnonin Jihohin Arewa, Alhaji Mu’azu Babangida Aliyu ya ce duk wani Musulmi ya san ilimi shi ne kan gaba da komai. Ya ce “Idan ba mu rumgumi harkokin ilimi ba, za a ci gaba da barinmu a baya a kasar nan. Amma idan muka rungumi ilimi za mu samu ci gaba a duk harkokinmu na rayuwa,” inji shi.
Tun farko a jawabin Shugaban Majalisar Malamai na kungiyar Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya ce sun shirya tarone kaddamar da gidauniyar raya ilImi ta bana ne domin neman gudunmawar Naira biliyan 2 da miliyan 300 saboda su giggina makarantu da sayen
motocin aiki a nan Najeriya da kasashen makwabta.
Ya ce kungiyar tana samun nasara a bangaren raya ilimi, inda a yanzu tanke da makarantu 5,754
da dalibai miliyan 5 da dubu 588 da 960.
Ya nuna damuwa kan tabarbarewar tsaro a kasar nan, inda ya dora alhakin haka a kan laifin shugabanni, “Domin babu yadda za a yi a ce babu laifin Shugaban kasa da gwamnoni da ’yan Majalisar Dattawa da Wakilai kan tabarbarewa tsaro a Najeriya, saboda su ne aka dora wa shugabancin kasar nan,” inji shi.
Ya yi kira ga Shugaban kasa da gwamnoni musamman na Arewa da ’yan Majalisar Tarayya su tashi tsaye wajen ganin an kawo karshen zubar da jinin al’umma da ake yi a yankin.
A samu gudunmawar miliyoyin Naira inda Babban Mai kaddamarwa kuma tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ba da Naira miliyan 25, yayin da Jihar Sakkwato ta ba da Naira miliyan 20 sai Kebbi Naira miliyan 10, sai Gwamnan Jihar Neja ya yi alkawarin ba da fili mai fadin eka 150 da motoci 5 da Naira miliyan 5. Jihohin Katsina da Yobe da Gombe da Taraba Naira Naira miliyan 5 kowaccensu. Mai alfarmar Sarkin Musulmi Naira miliyan 1, sai ‘yan majalisarsa Naira miliyan 1, sai Sanata Babayo Gamawa Naira miliyan 2, Sanata Ahmed Makarfi Naira miliyan daya.