Tambuwal ya nada dan PDP a matsayin mai ba shi shawara
Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya nada dan jam’iyar adawa ta PDP da wasu mutum hudu a matsayin masu ba shi shawara a bangarori daban-daban na tafiyar da gwamnati. Kamar yadda sanarwar da kakakin gwamnan, Malam Imam Imam ya rabawa manema labarai ya ce, Alhaji Akibu Dalhatu bayan an ratsar da shi zai […]

Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya nada dan jam’iyar adawa ta PDP da wasu mutum hudu a matsayin masu ba shi shawara a bangarori daban-daban na tafiyar da gwamnati.
Kamar yadda sanarwar da kakakin gwamnan, Malam Imam Imam ya rabawa manema labarai ya ce, Alhaji Akibu Dalhatu bayan an ratsar da shi zai kula da hada kan jama’a da wayar da kansu, sai Alhaji Umar Bature taimakon jama’a da ganin sun shiga shirye-shiryen gwamnati, Akitek Ibrahim Al-mustapha kula da taswirar jiha, Aminu Hassan Shagari zai kula da lamarin da suka shafi mutane masu lalura ta nakasa da kuma Dakta Rabi’u Alkali kula da cigaban kiyon kajin gona.
Gwamnan a wurin rantsar da su, ya nemi wadanda aka nadan da su dage wajen ayyukan mutane. “Dukkan ku ‘yan siyasa ne dake cikin ganiyarsu dake tare da talakawa, kan haka muke son ku ba da ta ku gudunmuwa da za ta taimaki mutanen Sakkwato, a kodayaushe abin da yake zo min a rai mukaman nan da muke rike da su an ba mu su ne saboda an yarda da mu don haka ku kara tashi tsaye ku yi aiki tukuru da zai taimaki al’ummar Sakkwato.
Da Aminiya ta tuntubi Alhaji Akibu Dalhatu kan ko ya bar PDP ne ya samu wannan mukami na mai baiwa gwamna shawara, sai ya ce shi mai girma gwamna bai ba shi mukami don yana PDP ba, kuma da zaran an baka mukami a gwamnati ya kamata a yi tsammanin kana tafiya da gwamnati ne, don haka yin wata jam’iya daban da gwamnati bai ta so ba.
Wakilinmu ya kira sakataren jam’iyar PDP na jihar Sakkwato, Alhaji Kabiru Aliyu don samun karin bayani ko wata hadaka ce aka shirya, ya ce ‘Alhhaji Akibu Dalhatu bai ba da takardar barin jam’iyar PDP ba har yanzu dan jam’iyarmu ne bai fita ba, sai dai ba matsayin PDP ne ya sanya aka ba shi mukamin ba, kusacinsa da gwamna ne ya sanya ya ba shi mukamin, har yanzu hakkinsa na dan PDP yana nan a wurinmu, kafin mu ga abin da zai yi a mukamin da aka ba shi, in ya sabawa PDP ne zamu dauki mataki, amma a yanzu ba wani rashin jituwa tsakaninmu da shi, muna yi masa fatan alheri matukar ba a yi amfani da shi ba wajen cin zarafin PDP, ba ruwanmu da shi’ a cewar sakataren Jam’iyyar PDP na Sakkwato.