Tambuwal ya zama sabon shugaban Gwamnonin PDP

An zabi Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal, a matsayin sabon hugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP. Sabon shugabana ya  ce kungiyar zata yi aiki tare da kwamitin gudanarwar jam’iyyar PDP wajen inganta jam’iyyar tare da karfafa dimokuradiyya a Najeriya. Gwamna Tambuwal wanda zai gaji takwaransa na jihar Bayelsa Seriake Dickson wanda wa’adinsa ke karewa nan […]

Tambuwal ya zama sabon shugaban Gwamnonin PDP

Tambuwal

An zabi Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal, a matsayin sabon hugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP.

Sabon shugabana ya  ce kungiyar zata yi aiki tare da kwamitin gudanarwar jam’iyyar PDP wajen inganta jam’iyyar tare da karfafa dimokuradiyya a Najeriya.

Gwamna Tambuwal wanda zai gaji takwaransa na jihar Bayelsa Seriake Dickson wanda wa’adinsa ke karewa nan da mako biyu masu zuwa.

 

Tambuwal ya bayyana haka ne a lokacin bude taron kwamitin zartaswar jam’iyyar karo na 88 a yau Litinin a Abuja.