Tana barci akalla sau 40 a kullum
Lucy Tonge, wata budurwa ce wadda take fatan shiga jami’a don ci gaba da karatunta, amma hakan ya faskara saboda wata lalura da take fama da ita ta ciwon barci, inda a kullum take runtsawa akalla sau 40, kamar yadda jaridar Birtaniya ta Daily Mail ta ruwaito. Yariyar ’yar kimanin shekara 18 da haihuwa, wadda […]
Lucy Tonge, wata budurwa ce wadda take fatan shiga jami’a don ci gaba da karatunta, amma hakan ya faskara saboda wata lalura da take fama da ita ta ciwon barci, inda a kullum take runtsawa akalla sau 40, kamar yadda jaridar Birtaniya ta Daily Mail ta ruwaito.
Yariyar ’yar kimanin shekara 18 da haihuwa, wadda take zaune a birnin Bedford na kasar Ingila, tana fama da wani ciwo ne mai suna, “Narcolepsy”. Barci dai yana dibarta a kusan kowane lokaci. Wannan ya sa ba ta iya magana mai tsawo, ba ta iya karance-karance littattafai da kuma tukin mota, kamar yadda ta bayyana.
Kodayake, ta bayyana cewa wannan lalurar ta fara ne kimanin shekara shida da suka wuce bayan ta yi fama da ciwon masassara. Amma gwamnatin kasar ta ce lalurar ta samo asali ne daga wata allurar rigakafi da Lucy ta amfani da ita a baya, mai suna, Pandemrid. Sai dai duk da haka, mahukuntan sun ki biyanta diyyar da take bukata.
Likitoci dai sun bayyana cewa lalurar ba ta da magani, sai dai sun ce akwai hanyoyin shawo kanta. Hanyoyin da suka hada da yin barci a kai-kai da cin abinci mai kyau da kuma yin wasannin motsa jiki.