Tana kashe wa tantabaru 2 Naira miliyan 2 kan kayan kwalliya duk wata
Meggy tana kashe musu Fam 400 (kimanin Naira 226 da 294) a duk wata.
Kowa da kiwon da karbe shi, inji masu iya magana.
Wata budurwa mai suna Meggy Johnson ta ba duniya mamaki bayan da aka gano tana kashe wa wasu tantabarunta biyu kudin da ya kai Fam 4,000, (kimanin Naira miliyan biyu da dubu 273 da 118) wajen kula da su da kuma dandasa musu kwalliya ta kece-raini.
- Matsalar tsaro na dab da zama tarihi a Najeriya – Buhari
- Ana zargin mahaifi da kashe dansa da tabarya a Kano
Budurwar ta tsinci tantabarun ne a wani waje da aka yar da su cikin wahala tun suna kanana, inda ta kai su gida ta rika kula da su na tsawon mako shida.
Lokacin ne ta saba da su ta kaunace su, suka shiga ranta matuka, hakan ya sa ta rada musu suna Sky da Moose.
Meggy Johnson mai shekara 23 da take zaune a birnin Louth, a Lardin Lincolnshire a kasar Birtaniya, ta ce, ta kebe musu dakinsu na musamman, ta dinka musu kaya iri-iri, sannan takan je kanti don yi musu sayayya, kuma kowaccensu tana da kayan da yawansu bai gaza iri 17 ba, akalla tare da yi musu ma’ajiyar kaya ta jikin bango, kuma ta saya masu keken da take dora su a kai su fita ganin gari.
Bayan daukar tantabarun, Meggy ta kai su wajen likitan dabbobi don duba lafiyarsu, sannan takan shayar da su da hannunta ta hanyar amfani da bututu a kowane lokaci har na tsawon mako shida har suka samu lafiya irin ta sauran tsuntsaye.
Ana shirya musu kayataccen bikin murnar ranar haihuwarsu har ma a yanka musu kek. A lokacin bikin an ba su kyautar abubuwan wasanni irin na yara.
Duk da yawan martanin jama’a game da yadda Meggy take kula da tantabarun, tana ba su amsar cewa wadannan tantabarun suna bukatar kulawa kamar kowace dabba.
Meggy tana kashe musu Fam 400 (kimanin Naira 226 da 294) a duk wata.
Meggy ta ce, “Wadannan tantabarun an mallaka musu dakin barci da wajen hutarwarsu da kayan wasansu da ma’ajiyar tufafinsu suna yin rayuwa mai dadi.”
“Tantabarun sun kasance masu son ado suna da wajen ajiyar tufafinsu inda suke da launukan tufafi kimanin 17 kowace tufa ta kai Fam 25 zuwa Fam 30, (kimanin Naira dubu 14 da 143, zuwa dubu 16 da 972,” inji ta/
Idan aka sanya masu tufafi suna natsuwa kuma sukan mai da muhallin cikin tsabta.
Meggy tana daukar tantabarun a kafadarta ta kai su lambu kuma suna jin dadin hakan don shan iska, kuma ba su taba yunkurin tserewa ba. Idan kuma akwai zafin rana tana daukarsu a keken da ta saya musu ta yi yawo da su don ganin gari.
“A lokacin da na binciki asusun bankina sai na fahimci cewa, ina kashe wa tantabarun sama da Naira dubu 200 a duk wata ko fiye da haka, sai na razana.
“Ina taya su murnar zagayowar ranar haihuwarsu tare da sauran ’yan uwana tare da kuma gabatar masu da kyaututtuka masu yawa,” inji ta.
Meggy ta fara sha’awar tsuntsaye ne a shekara 2016 bayan mutuwar karenta mai suna Pippa, lokacin tana tare da wasu tantabaru biyu, daya ta mutu dayan kuma tana da rai sai ta fara rainon dayar a gida.
Tun bayan tuntubar cibiyar adana dabbobi, daga nan ta fara tausayin tsuntsaye da ba a kula da su. Yanzu dai shekara biyu ke nan tana rainon wadannan tantabaru bayan mai kiwonsu ya yi watsi da su tun suna kanana, a watan Satumban shekarar 2019.