Tana neman diyyar Naira miliya 40 daga mijinta kan sanya mata cutar kanjamau

Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kasuwar Kurmi ta fara sauraren karar da wata mata ta kai tsohon mijinta tana neman ya biya ta diyyar Naira miliyan 40 bisa zarginsa da harbarta da cutar kanjamau. Matar mai suna A’isha Mansur ta shaida wa kotun cewa mijinta ya sa harbe ta da cutar kanjamau daga bisani […]

Tana neman diyyar Naira miliya 40 daga mijinta kan sanya mata cutar kanjamau
Tana neman diyyar Naira miliya 40 daga mijinta kan sanya mata cutar kanjamau

Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kasuwar Kurmi ta fara sauraren karar da wata mata ta kai tsohon mijinta tana neman ya biya ta diyyar Naira miliyan 40 bisa zarginsa da harbarta da cutar kanjamau.

Matar mai suna A’isha Mansur ta shaida wa kotun cewa mijinta ya sa harbe ta da cutar kanjamau daga bisani ya sake ta, don haka take neman kotu da ta karba mata diyyar Naira miliyan 40 daga hannunsa a matsayin kudin da za ta rika neman magani.
Bayan sauraren bukatar matar, alkalin kotun Mai shari’a Muhamamd Rab’iu Dausayi ya shawarci ma’auratan su yi zaman sulhu a tsakaninsu da lauyoyinsu sannan ya dage zaman shari’ar zuwa ranar 14 ga Nuwamban da muke ciki.
Aminiya ta gano cewa an dauki tsawon makonni ana tirka-tirka kan shari’ar wadda aka fara saurarenta a Babbar Kotun Shari’a da ke Nomanslan a karkashin Mai shari’a Faruk Ahmed amma ba a cimma matsaya ba, a karshe alkalin kotun ya mayar da shari’ar
zuwa Babbar Kotun Shari’a da ke Kasuwar Kurmi.
A hirar da Aminiya ta yi da A’isha Mansur ta ce kafin yin aure da tsohon mijinta lafiyarta lau, sai bayan an ta haihu da shi ne ta san cewa ta kamu da cutar kanjamau. “Kasancewar ya san yana da wannan cuta bayan mun yi aure na samu ciki da na nemi na rika zuwa awon ciki sai ya nuna shi a gidansa ba a zuwa asibiti. Sai daga baya likitoci suka tabbatar min ina da cutar suka kuma nemi na kai mijina. Da muka je ne sai suka ce ai shi ya fi shekara goma yana karbar magani a wurinsu. Daga nan na komo gidanmu a Kano na haihu daga baya aka mayar da ni can Abuja gidansa ganin cewa na riga na kamu da cutar babu wani abu da za a iya yi a kai. A haka muka zauna da shi yau fari, gobe tsumma har zuwa ranar da muka yi rigima inda ya yi min duka tare da yanyanka ni a jikina,” inji ta.
A’isha Mansur ta ce rigimarsu da mijinta ta samo asali ne a ranar da ya yi amarya inda ta bayyana wa amaryar halin da mijinsu yake ciki game da lafiyarsa. “Bayan amaryarsa mai suna A’isha Katsina ta tare a gidanmun na Malumfashi sai na shiga dakinta na gaya mata halin da mijinta yake ciki. Na ce kada ta soma yarda ya kusance ta. Da farko ba ta gaskata ni ba domin a tunaninta kissa nake yi mata don kada ta zauna a gidan, har tana cewa wai me ya sa ni nake zaune a gidan. A nan ne na shaida mata cewa ni ma don na riga na kamu da cutar ne, amma da a ce uwargidansa ta sanar da ni, to babu abin da zai sa na zauna a gidan.”
A’isha ta ci gaba da cewa “To bayan ango ya shiga dakin amarya sai ta ga ilahirin jikinsa a rame, ba yadda ta saba ganinsa a lokacin da yake zuwa zance gidansu ba, ashe sutura yake cikawa a jikinsa inda yake zama mai kiba. A nan take amarya ta yi tsalle gefe ta gaya masa cewa ba za ta zauna a gidan ba har sai sun je an yi musu gwajin cutar
kanjamau. Nan take ya ce ya san babu wanda zai gaya wa amryarsa wannan magana sai ni, don haka ya taho dakina cikin sauri. Sai jin saukar duka na yi a kaina, ya yi min dukan kawo wuka har da dauko wuka ya yanyanke ni a fuskata da kirjina da hannuwana, kuma ya sake ni.”
A cewar A’isha bayan ta koma gidansu ne iyayenta da hadin gwiwar kungiyar Zawarawa da Marayu ta kasa suka shigar da kara gaban kotu don bi mata hakkinta a wajen tsohon mijin nata.
Rahotanni sun ce ita ma A’isha amarya ta shigar da karar mijinta Mansur Musa a gaban Babbar Kotun Musulunci ta Jihar Kano da ke Nomanslan don neman ya sake ta.
A lokacin sauraren wannan shari’a ne, alkalin kotun Mai shari’a Faruk Ahmed ya raba aure tsakanin wanda ake kara da amaryarsa ba tare da ta biya shi ko kwabo da sunan kudin aurensa ba.
Mansur Musa ya sake shigar da sabuwar kara gaban kotun Kotun Lardi da ke Garu a Abuja yana neman iyayen amaryarsa su biya shi kudin da ya kashe a lokacin aurenta, ita kuma amaryar za ta ba shi wata kwamfutarsa da ke hannunta. A can Abujan ma alkalin Kotun ya sanya ranar 20 ga watan Nuwamban da muke ciki don sauraren shari’ar.
Lauyan da ke kare matan biyu, wato uwargida A’isha da amarya A’isha, Barista
dalhatu Shehu ya ce suna neman kotu ta tilasta wa tsohon mijin matar ya biya ta wannan kudi domin ta samu kudin da za ta rika neman magani da kuma kula da kanta, ganin yadda ya aure ta daga hannun iyayenta cikin koshin lafiya. “Mun gano cewa wannan mutum so yake yi ya rika yada wannan cuta tsakanin al’umma domin a halin da ake ciki ya auri mata biyar ya kuma sake su. Muna neman ya biya wannan mata da ya sa wa cutar Naira miliyan 40. Ita kuma amarya ba za ta biya duk abin da yake nema ba.
Shugabar kungiyar Zawarawa da Marayu ta kasa, Hajiya Atine Abdullahi ta ce kungiyarsu za ta bibiyi wannan shari’a har sai hakansu ta cimma ruwa, domin a cewarta hakan zai sa maza masu irin wanan hali su rika taka-tsantsan wajen sakin matansu, musamman ma idan suka sanya musu wasu cututtuka.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi