Tana zargin jami’an Sibil Difens da kashe danta
Wata mace mai suna Binta Abdullahi ta zargi jami’an tsaro na Sibil Difens da sanadiyyar rasuwar danta mai suna Jamilu Abdullahi da jami’an hukumar suka tsare kafin garzayawa da shi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usman dan Fodiyo inda ya rasu a ranar Juma’ar da ta gabata. Malama Binta ta ce, danta shi ne ginshikin gidansu […]
Wata mace mai suna Binta Abdullahi ta zargi jami’an tsaro na Sibil Difens da sanadiyyar rasuwar danta mai suna Jamilu Abdullahi da jami’an hukumar suka tsare kafin garzayawa da shi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usman dan Fodiyo inda ya rasu a ranar Juma’ar da ta gabata.
Malama Binta ta ce, danta shi ne ginshikin gidansu da ke kokari kula da su bayan rasuwar mahaifinsa wanda ma’aikaci ne a karamar Hukumar Tureta, “Ina zarginsu da kashe min dana don haka ya sa muka ki karbar gawarsa a lokacin da suka kawo mana ita bayan ya rasu a asibiti,” inji ta.
Ta kara da cewa za su nemi hakkinmu a wurin shari’a, inda ta ce yanzu suna jiran samun takardar bayani kan dalilin mutuwar yaron ne sa’annan su karbe shi don yi masa sutura kamar yadda shari’a ta tanada.
Hukumar Tsaro ta Sibil Difens da ke Sakkwato ta kafa kwamitin mutum 10 don binciko musabbabin mutuwar Jamilu Abdullahi mai shekara 38 wanda aka tsare a hukumar, kuma ta tabbatar da mutuwar matashin a hannunta tare da bayyana cewa gawarsa tana dakin ajiye gawawarkin na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usman dan Fodiyo, kamar yadda Kwamadan Hukumar Malam Bello Musa ya tabbatar wa manema labarai.
Ya ce “Jami’anmu ne suka kama marigayin kan kararsa da makwabciyarsa Amina Muhammad ta kai kansa, inda ana cikin binciken da ake yi masa ne ya rasu. “Ba gaskiya ba ne yadda wasu ke fadi a gari cewa jami’anmu ne suka kashe margayin kuma yanzu ana bincike duk wanda aka samu da laifi shari’a za ta hau kansa don za a yi masa hukuncin da ya dace da shi.”