Tanade-tanade 4 da Gwamnatin Kano ta yi wa ’yan TikTok — Hisbah

Mu dama Hisbah aikinmu shi ne umarni da aikin alheri da kuma hani da mummuna.

Tanade-tanade 4 da Gwamnatin Kano ta yi wa ’yan TikTok — Hisbah

Sheikh Daurawa yayin ganawa da ‘yan TikTok da suka amsa goron gayyatar hukumar

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta bayyana cewa za ta hada kai da ’yan TikTok domin tsaftace abubuwan da suke yadawa a shafukansu wajen gyara tarbiyyar al’umma.

Kwamanda Janar na Hukumar Hisbah Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne ya bayyana haka a lokacin da Hukumar ta gana ’yan TikTok a hedikwatarta.

Sheikh Daurawa ya ce sun kira taron ne don a tsaftace harkar TikTok a tsakanin matasan jiha a wani mataki na Operation kawar da badala.

“Mu dama Hisbah aikinmu shi ne umarni da aikin alheri da kuma hani da mummuna.

“Idan an duba kwanan nan mun himmatu wajen kawar da badala a wannan jihar.

“Hakan ya sa muka ga dacewar zama da ’yan TikTok don mu ga sun tsaftace ayyukan da suke yi a maimakon yada abubuwan badala da suke su koma su rika yin amfani da shafukansu wajen yada ayyukan alheri.”

Hukumar ta kara da cewa Gwamnatin Jihar Kano ta tanadi tagomashi ga matasan don ganin sun amfana

“Mai girma Gwamna ya tanadi abubuwa hudu ga ’yan TikTok din ciki har da aurar da masu son aure a cikinsu sannan masu son sana’a za a ba su jari.

Wasu daga cikin ‘yan TikTok da suka halarci taro a Hedikwatar Hisbah

“Haka su ma masu son karatu za a dauki nauyin karatunsu daga nan har zuwa Landan. Su ma wadanda ke da matsaloli na damuwa ko rashin lafiya za a sama musu magani tare da ba su shawarwarin da za su canza tunaninsu.”

Sheikh Daurawa ya bayyana cewa daga yanzu Hukumar Hisbah za ta bude shafi na musamman tare da ’yan TikTok din don tattaunawa tare da bibiyar abubuwan da suke yi a shafukansu don sanin ko sun canza halayyarsu ko kuma akasin haka.

Wasu daga cikin ’yan TikTok din da suka tattauna da Aminiya sun nuna jin dadinsu game da taron da suka yi tsakaninsu da Hukumar, inda suka yi alkawarin canza akalar abubuwan da suke yi wanda suka saba shari’a.

Khadija mai bakin kitse ta bayyana cewa ta amfana da zaman da ta yi da Hukumar Hisbah, inda ta ce daga yanzu ta daina sanya raye-rayen banza a shafukanta.

“Gaskiya na ji dadin wannan zama da muka yi kuma insha Allah daga yanzu na daina sanya rawa a shafina.

“Zan canza zuwa abubuwa na alheri. Ina kiran sauran ’yan uwana ’yan TikTok da suka tsorata suka ki zuwa da su yi kokari su halarci zama na gaba.”

Shi ma wani mai suna Al-amin da aka fi sani da Na Annabi, ya ce a yanzu ya shirya tsaf wajen ganin ya yi watsi da abubuwan da yake yi domin ci gaba da karatunsu.

Fiye da ’yan TikTok 200 ne suka halarci taron wanda kuma Hukumar Hisbah ta bai wa kowannensu da Naira dubu biyu a matsayin kudin mota.

A ƙofar banɗakin Gidan Yarin Kuje nake kwana — Ɗan zanga-zanga

An ceto jaririyar da ’yar aikin gida ta sace a Edo

An ceto mutum 58 da aka sace a Kaduna

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7