…Tankar mai ta jawo konewar motoci 10 a Kano

Wata tankar dakon man fetur ta yi sanadiyyar konewar akalla motoci 10 bayan da ta kama da wuta a garin Dakatsalle da ke kan babbar hanyar Kano zuwa Kaduna a karamar Hukumar Bebeji a Jihar Kano a ranar Lahadi da magariba.Wani ganau da ya yi wa wakilinmu karin bayani a kan lamarin, Malam Musa Dakatsalle […]

…Tankar mai ta jawo konewar motoci 10 a Kano
…Tankar mai ta jawo konewar motoci 10 a Kano

Wata tankar dakon man fetur ta yi sanadiyyar konewar akalla motoci 10 bayan da ta kama da wuta a garin Dakatsalle da ke kan babbar hanyar Kano zuwa Kaduna a karamar Hukumar Bebeji a Jihar Kano a ranar Lahadi da magariba.
Wani ganau da ya yi wa wakilinmu karin bayani a kan lamarin, Malam Musa Dakatsalle ya ce bayan direban tankar ya tsaya zai yi buda-baki, sai kawai aka ga ta kama da wuta inda nan da nan abin ya rincabe har motoci 10 suka ci wuta ciki har da wasu tankokin dakon biyu makare da litar mai dubu talatin da uku kowaccensu.
Haka kuma wutar ta ci shaguna masu yawa da ke kusa da inda abin ya faru, sai dai ba a samu rahoton mutuwar mutane ba, amma an yi asarar dukiya mai yawa.
Mutanen garin da masu wucewa ne suka yi ta kokari wajen ganin wutar ba ta ci gaba da yaduwa zuwa sauran wurare ba.

Zazzaɓin Lassa ya kashe mutum 214 a Najeriya — NCDC

An kama masu garkuwa da mutane a Borno 

Rikicin ya kunno kai a Hukumar Alhazan Jihar Delta

Sojoji sun ceto mutane 5 da ISWAP ta sace a Harin Ngoshe