Tankar mai ta kone gidaje 11 a garin Dabai

Wata tankar dakon man fetur ta kone gidaje 11 ta kuma kashe mutum biyar tare da jikkata wasu mutum shida. Hadarin ya faru ne a lokacin da tankar ta fadi a gangaren shiga cikin garin Dabai a karamar Hukumar Zuru da ke Jihar Kebbi.Gobarar tankar ta kuma yi sanadiyyar konewar motoci 11 wadanda suke ajiye […]

Tankar mai ta kone gidaje 11 a garin Dabai
Tankar mai ta kone gidaje 11 a garin Dabai

Wata tankar dakon man fetur ta kone gidaje 11 ta kuma kashe mutum biyar tare da jikkata wasu mutum shida.

Hadarin ya faru ne a lokacin da tankar ta fadi a gangaren shiga cikin garin Dabai a karamar Hukumar Zuru da ke Jihar Kebbi.
Gobarar tankar ta kuma yi sanadiyyar konewar motoci 11 wadanda suke ajiye a kofar gidan Shugaban karamar Hukumar Zuru.
Wasu wadanda abin ya faru a gabansu, sun shaida wa wakilinmu cewa tankar man ta dawo baya ne a lokacin da take kokarin haye hawan Dabai domin kai man fetur wani gidan mai da ke garin na Dabai.
Wata budurwa mai suna Rashida da abin ya faru a gabanta ta shaida wa wakilinmu cewa lokacin da tankar ta fadi mutane sun yi ca domin su debi man da ke zuba a kasa, sai kwatsam gobara ta tashi, inda aka samu wadannan asarar rayuka da dukiyoyi.
Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi Sama’ila Yombe Dabai ya ziyarci wurin da abin ya faru domin gane wa idonsa irin asarar da aka yi tare da ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasu da kuma jajanta wa wadanda suka yi asarar dukiya ko suka jikkata.
Mataimakin Gwamnan ya roki Allah Ya jikan wadanda suka rasu, inda ya ce wannan wata kaddara ce da Allah Ya kawo, kuma ya ce gwamnatin jihar a karkashin jagorancin Sanata Abubakar Atiku Bagudu za ta yi taimaka i