Tankar mai ta sake yin bindiga a Jigawa
A baya irin wannan ta faru, inda wata tankar mai ta yi bindiga tare da hallaka sama da mutum 170.
Wata tanka ɗauke da mai ta sake kamawa da wuta a Jihar Jigawa.
Gobarar, ta faru ne kusa da iyakar Jigawa da Kano, wanda lamarin ya tsoratar da mutanen da ke kusa da inda tankar ta yi bindiga.
Mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya a Jihar Jigawa, Aliyu M. A, ya tabbatar wa manema faruwar lamarin a ranar Laraba.
Aliyu, ya bayyana cewa, “A ranar 12 ga watan Nuwamba, 2024, da misalin ƙarfe 10:43 na safe, Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya ta samu kiran gaggawa daga Dagacin Ƙauyen Kuho, Zubairu Ahmad, game da hatsarin tanka a Kwanar Kalle, kusa da ƙauyen Gamoji a kan hanyar Maiduguri.”
Ya ƙara da cewa tawagar jami’an hukumar, sun isa wajen da misalin ƙarfe 10:50 na safe kuma sun yi nasarar kashe gobarar.
Lamarin ya faru ne wata guda bayan wata irin gobara makamanciyar irin wannan ta auku, wadda ta yi sanadin mutuwar sama da mutum 170 a watan Oktoba.
Hatsarin na baya ya rutsa da wata mota wadda ta yi dakon fetur daga Kano zuwa Nguru a Jihar Yobe, ta yi bindiga a garin Majia.
Hatsarin ya sanya ruɗani da firgici a tsakanin mazauna yankin, waɗanda suka rasa mutanensu da dama.