Tankar mai ta yi bindiga a garin Tafa

Mutum uku sun mutu sannan kimanin mutum 15 sun samu munanan raunuka yayin da tankar man fetur ta kwacewa direbanta a daidai garin Tafa da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna ta fadi. Garin Tafa wanda ya kai kimanin tafiyar minti 40 daga tsakiyar garin Abuja, yana cikin karamar hukumar Kagarko da ke jihar Kaduna. […]

Tankar mai ta yi bindiga a garin Tafa

Mutum uku sun mutu sannan kimanin mutum 15 sun samu munanan raunuka yayin da tankar man fetur ta kwacewa direbanta a daidai garin Tafa da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna ta fadi.
Garin Tafa wanda ya kai kimanin tafiyar minti 40 daga tsakiyar garin Abuja, yana cikin karamar hukumar Kagarko da ke jihar Kaduna.
Aminiya ta gano cewa kimanin gidaje 17 da tankokin mai da aka ajiye a kan babbar hanyar da ta ratsa garin Tafan duk sun kone.
Wani ganau ya ce tankar man mai dauke da tambarin kamfanin mai na Shema ta na kan hanyarta ta zuwa Abuja daga Kaduna inda direban ya yi kokarin kaucewa yin taho-mu-gama da wata mota da ke tahowa amma kuma ta kwace masa ta fadi.